40

1.4K 81 15
                                    

RAYUWA DA GIƁI 40
ƘARSHE




Batul Mamman💖



Allahumma Balighna Ramadan...AMEEN




A can hotel Mubina ba ƙaramar takura ta shiga ba. Aure dai an ɗaura amma kamar yadda ta ce babu kowa nata sai dangin miji. Duk sai ta koma abar tausayi. Yaya Kubra ta lura da haka sai su ka yi magana da Yaya Hajiyayye, aka kama mata ɗaki daban domin kwana biyun da su ka yi ɗakunan da su ka kama na group ne masu gado hurhuɗu.

"Hamdiyya ki koma wajenta ki tayata zama. Idan kuna buƙatar wani abu ki mana magana. Na san ba za ta sake da mu ba yanzu kuma sai a hankali."

Hamdi tayi murmushi harda rufe fuska da tafukan hannu "nima dama kunyar taku nake ji har yanzu."

Yaya Kubra ta harareta da wasa
"Ehhh lallai, wallahi ki ka sake cewa kina jin kunyarmu sai na yi mi ki handsfree a gaban Alhaji."

"Tsegumta min mana likita. Me ki ka gani? Tajo ya yi ajiya ko? Oh ni uwar babana. Aure ko wata biyu ba a yi ba. Dama na san za a rina. Taj ko kaɗan bai yi kama da salihai ba.

Hararar da take yiwa Hamdi komawa tayi kan Yaya Hajiyayye.
"Ke fa daɗina da ke sakin zance wallahi. Don Allah kina yi kina tauna magana kafin ki furzar. Me ya kawo batun salihanci tsakanin mata da miji banda abin ki?"

"Raini ya jima da shiga tsakaninmu dama Kubra. Gara ki kwaye min baya a gaban...." ta waiga babu Hamdi babu dalilinta. Can ta hangota ta kusa ƙure korido tana ta zuba sauri kamar ta kifa. Ita da Kubra su ka haɗa ido su ka kwashe da dariya. Faɗan da ba su ƙarasa ba kenan.

*

Ƙarfe tara da rabi Umma ta shiga ɗakin su Mubina. Hamdi kaɗai ta samu ta kashingiɗe akan abin sallah. Umman na shiga ta tashi zaune.

Umma tayi murmushi "ƙanwar Ango ina amaryar yayanki?"

"Tana banɗaki" ta amsa mata ita ma tana murmushin.

"Ai gara tayi wank..."

Caraf Mubina ta katse Umma daga cikin toilet ɗin da rawar murya. Tsoro muraran ya bayyana a tare da ita.

"Ba wanka nake yi ba. Alwala zan yi na fito."

"Ai ba laifi ki ka yi ba Mubina. Ki yi wankan ki shirya a nutse Alhaji ya ce ni da Hajiyayye mu raka ki asibitin."

"Na'am? Asibiti kuma" Ta buɗe ƙofar ta fito a firgice. Idanunta zuru-zuru sai ɓare-ɓare take yi. Mubina akwai ruɗewa  sai a lokacin hakan ya bayyana.

Hamdi ta kalli Mubina sai taji wani tausayinta ya tsirga mata. Shi fa aure kwarjini gare shi na daban. Gashi dai da ƙafarta ta taho ƙasar amma yau ɗaya duk ta sauya saboda alhini.

Umma zama tayi akan gado ta yafito Mubina da hannu.
"Mene ne amfanin aure idan mace bata kasance tare da mijinta ba Mubina? Asibitin da kansu su ka ce sun yarje miki zama tare da shi tunda ke likita ce sannan sabon aure."

"Umma ni dai don Allah" sai kawai ta fashe da kuka.

Umma ta tashi tsam ta rungume ta.

"Kamal ɗin ne ba kya so?"

Mubina ta girgiza kai.

"Aure a irin wannan yanayin ko? Ba haka aka saba ba na sani, amma faruwarsa a hakan ya sa naku ya zama special."

Ba kunya Mubina ta ɓare baki "ni dai Mamana, Umma don Allah wajen Mamana zan tafi."

Ɗago kanta Umma tayi ta ce "Tamɓali! Mubina? Shekararki nawa ne?"

Mubina ta sanya hannu ta rufe fuskarta tana kuka tana murmushi lokaci guda.

"Na fahimce ki" Umma ta sake yin murmushi "ƙarasa abin da ki ke yi ki kwanta"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 28 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RAYUWA DA GIƁIWhere stories live. Discover now