Babi na Daya

1K 41 3
                                    

             RAYUWAR MACE
                           1
                         Na
              Shatou Muh'd
     

   "Safeena!" Nadia ta kira ta a karo na goma hade da dan dukanta a gadon bayanta. Firgigi Safeena ta yi kamar wacce aka tsikara bata shirya ba "iye na'am" Safeena ta fadi a tsorace. A hasale Nadia ta fara magana "wai meye haka ne Feena kinzo kin zauna tun dazu ina maki lissafin kudin da za'a kashe a bikin nan amma da kyar ma in kinji rabin abinda nake fada, tunanin me kike yi ne ko har kin fara tunanin auren ne?" Nadia ta k'arasa maganar da salo irin na zolaya. Murmushi wanda da gani be kai zuciya ba Feena tayi sannan ta ce "Nads kenan bazaki gane ba wallahi, sorry cigaba ina sauraren ki". Nads ta cigaba da lissafa mata events da kuma kudaden da za'a kashe a bikin wanda ya rage wata daya kacal. Jinta kawae Feena keyi amma bawai tana fahimtar abinda kawarta take cewa ba har daga karshe suka kare suka nufi hanyar fita daga makarantar ta su wacce da ganinta kasan Jami'a ce. Kowacce ta hau motar da zata kai ta gidansu bayan sunyi sallama.
     A sanyaye tayi sallama cikin gidan nasu, Ya Ummi ce ta amsa mata da " wa'alaikumussalam, ha'a 'yan makaranta har an dawo? Aiko dazunnan Zainab ta kira wayarta nake cemata baki nan ta kira nan da Awa biyu ashe ma kina kan hanya." Ya Ummi ta fada tana cigaba da tsintar wake a bakin famfo. Basar da zancen Feena tayi ta k'arasa inda mahaifiyar ta take aiki tareda sa hannu cikin waken da nufin taya ta tareda cewa "Ya Ummi ina wuni?" Ya Ummi ta amsa mata cike da fara'a da kuma yabawa da natsuwar 'yar ta "Lafiya lau Safeena daga dawowa ko ajiye jaka ba'ayi ba sai a fara aiki,  a'a jeki daki ki huta ga abincinki can a kula kinji 'yar albarka" Wani irin daci ne ya ziyarci zuciyarta tareda wata kwalla dake shirin fitowa daga idanunta "na cuci iyayena" shine abinda kawai ta iya fadi a zuciyarta ta tashi ta shige dakinta. Rage kayan jikinta tayi ta kwanta dai dai akan gado tana hawaye wanda bansan dalilin su ba. Abincin da Feena bataci ba kenan bacci yayi awon gaba da ita.
     Ba ita ta farka ba sai kusan la'asar. Tsakar gida ta fito taga har Ummi ta gama gyara waken. Alwala tayi ta shiga daki ta zauna kan sallaya ba tareda yin sallar ba. Motsi da taji ne kamar za'a shigo dakin yasa tayi saurin yin sujjada kamar gaske dama sallar takeyi. Bayan mintuna ta sallame ta tashi ta nufi dakin Ummi. (Halin Safeena kenan na rashim son yin sallah, yanda takeyi kenan idan tayi alwala ta shige daki ta zauna a kan sallaya in taji motsi ta hau sujjada ko ta hau tahiyya).
    "Umma kawo nikan waken in kai maki" Feena tace ma Ummi wacce take linke sallayan da ta idar da sallah. Murmushi Ummi tayi sannan ta ce "Safeena kenan, ya kamata ace kin saba da halin babanku zuwa yanzu.  Sanin kanki ne Babanku baya son ana aiken ki a matsayin ki na mace, daidai da makota bai yarda kije ba daga makaranta sai makaranta ballanta na wani aike. Ki bari kawai in su Hayatu suka dawo sa kaimin markaden". Tashi Feena tayi ta shige dakin ta rai a bace. Wannan na daga cikin halayen mahaifinta data fi tsana. Dogon tsaki taja tareda fadin "aikin gama ai ya riga ya gama" ta rufo kofar dakinta sannan dauko wayarta a cikin akwati chan kasa ta kunna ta fara chatting.
     Sallamar su kannenta ne yasa tay maza maza ta tura wayar a karkashin katifa don tasan yanzu zasu nemi shigowa dakin nata don gaisheta. Hakan kuwa ya faru don seda suka shigo su uku suka gaisheta cikeda girmamawa.
  

Ramin K'aryaWhere stories live. Discover now