Babi na Sha Biyar

205 23 6
                                    

  Cigaban labari

  Goge hawayen dake gangaro mata akan fuskarta tayi ta kakkab'e jikinta dukda bakomi a jiki, ta tashi ta shiga bandaki don yin wanka. Bata cika mintuna goma ba ta fito, ganin kiran da Naufal yayi mata ne yasa ta karisa inda wayarta take, danna lambar shi tayi taji bizi, alamar yana waya, sauri sauri tayi ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa wacce akayi dinki mara hayaniya sosai. Tayi kyau kwarai tabarakallah. Gyalen kayan ta dauka ta yafa a kanta wanda ya k'ara fitowa da kyan atamfar. Karar shigowar kira a wayarta ne yasa ta dauke dubanta ga madubi Don ganin mai kiranta. Naufal, ta fad'a a fili kafin ta danna amsawa. "Basma ganinan a harabar gidanku" ya fad'a a yayinda ita kuma ta daga labulen taga domin gani. Motarshi da hango tana shigowa Don samun wurin parking. Bugawar zuciyarta ne ya tsananta saboda tunanin son maso wani da takeyi, gani take kamar tanacin amanar Naufal ne. Kauda tunanin tayi sannan ta feshe jikinta da turare mai kamshi a nufi hanyar kofa.
" Mum gashi nan yana iso fa"

"Kaikaikai tabarakallah Masha'Allah, wannan irin kyau haka Basma, da kinsan yadda atamfa ke maki kyau da kindena sa kananan kaya. "
Turo baki tayi kafin nan ta bayyana mum amsa da "kedai Kawai kinaso indena sa wa. Amma ninan har na fara zufa."

Dariya sukayi sannan basma tayi gaba Don bud'e kofar d'akin baki dake waje. Tunda na bud'e kofar takejin kamshin turarensa alamar yana iso kenan. Fitowa tayi don tarbarsa da karfin hali kana ta daura wani yalwataccen murmushi a saman fuskarta wanda yai sakamakon lotsawar gefen kumatunta. Yayi kyau kwarai cikin shaddarshi Kalar sararin samaniya, ya daura hularshi mai Rodin sararin samaniya da blue, fuskar shi tana dauke da wani mayetaccen murmushi maisa natsuwar zuciya, kyakyyawa ne ajin karshe sannan fari neh fuskarshi na dauke da saje lufluf. Iskar da ya hura mata a idonta ne ya razanar da ita, kunya ce ta kamata Don batasan lokacin daya k'ariso inda takeba. Lallai zuciyarta ce ta yaudareta, ba ya Suraaj dinta bane yazo, wannan Naufal neh. "Baby yada kallo? Karki damu nan da kankanin lokaci fuskarnan da jikin dake manne da ita zai zama mallakinki" ya k'arisa yana kanne mata ido. Basar da zancen tayi don har GA Allah abinda yace ya bata kunya, amma ya ta ita? Tun ba yanzu ba tasan halin Naufal da irin wannan sakin layin nasa. "Sannu da zuwa, bismillah" ta fad'a tana mai nuni da kofa.
Shiga yayi tareda zama kan d'aya d'aga cikin kujerun dake falon.
"Ina wuni, ya hanya, ya kuma kasan baro mutan gidan?"
"Wanne zan fara amsa maki ne, but kowa Lpy kalau, hanya Kuma Alhamdulillah". Bayan sunyi gaisuwa da yar hira ne ta tashi Don kawo mai abinci, inda a sannan mum ta shigo suka gaisa da Naufal cikin girmamawa.  Tunani ta tsaya a kitchen yanayi gaskiya ba laifi Naufal shima namiji ne don ba abinda ya Suraaj zai nuna mashi wai natsuwa, amma banda wannan Naufal yayi. Zata dena bin shiritar zuciyarta ne na ganin Suraaj zai dawo gareta ta rungume kaddara kawai, baccin so ay Naufal ba abin yaddawa bane.
Tray din abubuwan ci da sha ta dakko inda da shigowarta taji mum na maganar sa Rana, inda Naufal kecewa shi inda son samu shi ko sati daya ne ya yarda Don ana ta matsa mashi a gida. Murmushi mum tamai tareda cemai zatayi magana dashi wakilan Basma. Sannan ta  tashi ta fita har suka hadu da Basma a hanya wacce idonta yayinda cicciko da kwalla. Sati daya fa? Gaskiya yayi tsawo ta fad'i a ranta sannan ta k'arasa falon tasamu Naufal Yanata murmushi tamkar wanda akaima bushara da aljanna. "Amaryata kindade,harna fara tunanin biyoki kitchen din" Murmushi tayi wanda bai kai zuciya ba wanda Sanadiyyar hakan hawayen data makale Ya tona asirinta Ta hanyar kwaranyowa kan kuncin ta. 

Hankalin Naufal yayi matukar tashi don tashi yayi daga inda yake zaune ya matso gareta. "Subhanallah, baby maiya sameki?" ya tambayeta muryarsa na nuna tashin hankali k'arara.
Wayencewa tayi ta hanyar kama karamin  danyatsan ta tana hurawa "Danaje kitchen ne natab'a tukunya shine na k'one".

"Eyyah, sannu kinji, ko muje asibiti ne? Is it still paining?" ya tambaya a tare.  Hakan da yayi ba karamin tab'a zuciyarta yayi ba, Lallai Naufal yana sonta nan da nan taji zuciyarta tana nema mai gurbi. "Aa ya dena zafin MA dear"

Dear? Ya maimaita a ranshi , yanzu kam ya tabbatar Ya samu karbuwa a wajenta.
  Haka sukaci abinci suna hira don Basma ba karamin sakin jiki da shi tayi ba, Naufal ba baya ba wurin barkwanci da sa mutum dariya. Da zaitafi ne ya dauko tsarabar da yayi mata. Kayane sosai na sawa dana kwadayi. Godiya tayi mashi sannan yaja motarshi ya tafi yabarta da kewarsa.

****

"A Gaskiya Naufal yaron kirki ne Alhaji shys nake ganin ko za'a yi bikin gabaki d'aya ne dana surajo? " Fadar Hajiya Ladidi.

Yayan nata ne ya amsa da Toh amma da an bari yarinyar ta Dan saba dashi tukunna suma su shirya don shirya biki a sati daya ba karamin abu bane.

"Ay na riga na shirya don yanzu haka kayan kitchen ne kawai banyi odar su ba, nidai yaya kawai abinda nakeso shine kaje a sanarda yan uwan babanta."

"Toh shikenan Allah ya shige mana gaba, kice MA yaron Ya turo manyansa suzo ayi magana gobe ko jibi." Murna fal ta cika Haj Ladidi don dama so take ta nuna ma Suraaj da mahaifiyarshi cewa yarta ba Kwantai tayi ba.

Tun a mota ta kira Naufal Ta fada mashi cewa ya turo. Murna wajenshi yama kasa boyewa Ya dinga zuba mata godiya tareda adduo'i, hakan dayayi kuwa ba karamin kara mata karfin gwiwa yayi ba don take  kira kawarta da ke Dubai wacce ta kusan dawowa Ta bada sak'on kayyayakin kitchen tundaga electronics har kayan sawa gabadaya.

Basma na kwance Naufal ya kirata Ya guntsa mata labarin, itama tayi murna kwarai Don tuni ta yakice tunanin auren Yaa Suraj inda tayi adduar Allah ya kara saka mata son Naufal a zuciyarta.

*****
Waleema
  Ayau Jumma'a jama'a da dama suka shaida Walimar Bikin Safeena da Suraaj, amarya ta cake cikin wata doguwar riga wacce ya Abee ya kawo mata inji Suraaj, a cewarshi. Tayi mamakin yadda akayi Ya samu kudin wannan riga, b'ata tsinke da lamarin ba saida sukaje wurin waleemar ta rude da ganin deco din wurin da Kuma abincin dataga anata yawo dashi lafiyayye.  Kodai Ya Abee dama ya shirya ma wannan bikin ne haka?  Shiru tayi da bakinta ta zuba ma sarautan Allah  ido. Malama Khadeeja ita ce ta sa jikin mutane yayi sanyi da nasihohin da tayi akan amanar aure. Kwarai waazin Ya ratsa zukatan jama'a amma banda Feena. Kosawa tayi a tashi don ganitake kamar da ita ake waazin, kamar malamar tasan abinda take shirin aikatawa. Bayan anyi rufe taro da addu'a wanda hakan baisa karamin dadi yai MA amarya ba sai danjin Ango suka fara zuwa ganin amarya. Tasha jinin jikinta kwarai ganin irin shigar da kowannensu tayi cikin bakaken abayoyi masu kyau da tsada, ko wacce hannayenta cikeda zobuna da warwaraye na zinare. Daga ita har kawayenta ba wanda ya Iyali cewa komi amma kowa ya zaku ya koma gida don samun ainihin labarin Mijin Safeena.

Amarya basma kuma a d'aya bangaren, tana gida ana gyaran jiki wanda ya Shafi'u dilka da sauransu, basuyi shirin wani event ba kasancewar bikin yazo a kurarren lokaci. Haj Ladidi da kanta take gyara yarta, Don haka bata samu zuwa waleemar ba don itama Tana fama da nata bikin.

  Yan uwa da abokan arzik'i da sukaje waleemar haka suka koma gida Suna santin kyan amarya da kuma jinjina ma Suraaj ganin yayi dacen mata. Mami kam farinciki ne ya lullube ranta don taji dadin shaidar da akayi ma amaryar.

A yau Asabar wacce tayi daidai da ranar daurin auren Basma da Naufal, dakuma daurin auren Suraaj da Safeena. Farin ciki wurin Suraaj Yaki misaltuwa Don sai sharri abokanshi suke mashi wai yana dokin aure, share su yayi da farko amma da yaji abin yayi yawa sai ya basu amsa da "Bazaku gane irin luck din da Allah yabani bane na farko yadan bani arzik'in dukiya, ya bani ilimi, yanzu kuma ya bani Almar'atus Saliha, Kunga kam I am the luckiest person on earth" dariya sukayi kowa yana fadin albarkacin bakinshi. Karfe goma daidai aka daura auren Naufal da Basma a babban masallacin Jumma'a dake unguwar akan Saraki dubu arba'in kacal. Daganan aka k'ara dunguma unguwar su Feena aka daura na Safeena da Suraaj akan Saraki dubu ashirin.



Assalamu alaikum!  Ya kuke? Ya family? Karatu nd komi da komi. Inaso inyi amfani da wannan damar wajen ba mabiya littafina hqr Don Shiru da sukaji ni na lokaci mai tsawo... Ina mai baku hqry akan hakan. Kun yafe min?  *puppy eyes* ... 
 
Anyways an daura auren.. The long awaited moment.. Hehehehe*Chipmunk voice*. This story is just beginning....

Don't forget to press that cute little 🌟  below..




Ramin K'aryaWhere stories live. Discover now