BABI NA UKKU

8.3K 820 67
                                    

Karfe sha d'aya da yan mintina na dare ta ji kokarin bude kofarsa, da alama ruwan da ake tsugawa ne ya sanya shi shigowa da wuri.
Sai da ya rage kayan jikinsa, ya watsa ruwa, kafin ya doshi dakin da ke kallonnasa.

Kwance take, idanunta a lullube ta zurfafa a kogin tunanin da ya hane ta jin sautin takunshi, Rukayya na kwance saman ruwan cikinta, a haka ya daga labulen da ya suturta dakin, yana mai tura kanshi ciki.

Sai da ya k'are musu kallo, kafin ya ja siririn tsaki. A duniya idan akwai abinda ya tsana baya da mahaifinshi, to ba zai taba wuce wadannan halittun guda biyu da suke ikirarin zama a karkashin ikonsa ba.
Hannu yasa ya taba ta a hankali, hakan ya haifar da firgici a kasan zuciyarta, ta dago a tsanake ta na mai sauke idanunta a kanshi.

"Ki same ni dakina"
Furucin da yayi kenan, ya juya da zumar barin dakin, sai dai ganin bata da niyyar motsawa yya sanya shi dakatawa, ya juyo a masifance yana mai kare mata kallo.

Mikewa tayi bayan ta gyara ma Rukayya kwanciya, tana mai kauda kanta a dubansa, ta kuma san sarai manufar maganar tashi, sai dai alkawari ta dauka na lokaci yayi da ya kamata ace ya san muhimmancinta.

Ganin bata da niyyar ansa shi ya sanya shi dukawa a gabanta,

"Kinsan abinda nike bukata Jameela. Ki sassauta ma kanki kiyi abinda na umarce ki, otherwise, zan iya kwata ta karfi matsawar bukatata zata biya. Ki tadda ni dakina."

Kululun bakin cikin da ya tokare makoshinta ne ya hana ta furta ko da kalma daya, shin yaushe Sadam zai sauko daka dokin nak'in da ya hau? Yaushe rayuwarsu zata ci gaba kamar yadda suka fara shimfida ta? Tabbas bata tunanin irin wannan ranar mai zuwa ce, idan tayi duba da irin cin kashin da ya kan sauke kanta a safiyar ko wacce rana.
Tunaninta ya katse lokacin da taji hannunta cikin nashi, da iya karfinsa na da namiji yake janta, bai dakata ba sai da ya tabbatar da ya shigo tsakiyar dakinsa.

Idanunta ta kankame, haka zalika kafafunta a hade wuri guda, hawayen dake makale a kwarmin idonta suka gangaro cikin firgici take magana

"Dan Allah kayi hakuri, wallahi ban karasa warkewa daga raunin da kai mun wancen karon ba. Ka yi hakuri dan Allah."

A yadda yake jin kanshi a halin yanzu, babu wani hakurin da zai iya yi, asali ma, kalmominta harde masa suke, ya kan ji tamkar muryarta na amsa kuwwa ne a cikin dodon kunnensa, da wannan bai saurara mata ba, kamar yadda itama bata daina yakin kwatar kanta ba.

Tun bayan da ta haifi Rukayya, Sadam bai taba zo mata ba, irin zuwan da addinin musulunci ya tanadarwa ma'aurata, ya kan yi mata son ranshi ne ba kuma tare da damuwar abinda hakan zai haifar gareta ba.
Tun shudewar shekarar farko ta aurensu, baza ta iya kayyade adadin fyaden da mijinnata yayi mata ba, sai dai duk da haka, bata daina zargin kanta ba, domin kuwa itace silar komai.

Tana ji tana gani ya gama bidirinsa, ya kuma tsallake ta ya shige bandaki abinsa.

'Wannan wace irin kiyayya ce? Wace irin rayuwa ta shigo da kanta?'

****

Kukan da take a yanzu, ba za ta taba dangantashi da afkuwar abinda ya faru ba, domin ta dad'e da sabawa da kalar azabobi irin na mutumen da tayi gangancin d'aukakawa fiye da iyayen da suka kawo ta duniya!
Kukan da take na bak'in cikin yadda rayuwa ta juya mata baya ne cikin dan karamin lokaci, ta mayar da ita marar gata, wacce bata da iko akan irin duk wata cuzgunawa da Sadam zai mata.

SABON SALON D'A NAMIJIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora