14

907 73 1
                                    

1️⃣4️⃣Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta

               Na

Benaxir Omar

         *NWA



Www.benaxiromar.com

       Kafin yace wani abu ta nufi kansu, kan Amrah ta nufa ta fara duka kaman Allah ne ya aiko ta, Amrah kuwa tana kokarin kare kanta, Jamal kuwa ya rasa ya zaiyi don haka kawai ya dago Amina
"meye haka meyasa baki da hakuri ne?"
ko kula shi ba tayi ba sai da ta tabbata ta riko Amrah da karfi ya riko hannunta ya wurgata bayansa yace " muje waje in miki bayani" kaman ta nutsu haka tabi shi suna fita ta juyo dasauri ta shiga dakin ta rufe kofan  daga ita sai Amrah, wayan cable ta ja ta balla ta hau kan Amrah dashi dama gashi tafi Amrah auki, inda take shiga ba tanan take fita ba,Amrah tayi kuka sosai jikinta ya faffashe ganin igiyan cable din ya tsinke ga kuma Jamal sai buga kofa yakeyi kaman zai balla da karfi ta riko Amrah ta hada ta da bango, yadda bangon yayi kara hatta Jamal dake waje sai da yaji kafansa yasa da karfi yana buga kofan amma shiru, kofan yaki buduwa alokacin Amina ta gama komi sannan tace
" meya hada ki da mijina"
Amrah bata cikin hayyacinta don a sume take ganin haka yasa   ta bude kofan da sauri ya nufi kanta  yana jijigata jikinta duk ya dau zafi, cak ya dauketa ya nufi mota da ita, Amina ta riko shi tace "wallahi baka isa ba, karuwan zaka kai asibiti kabarni ni matar sunnah?"
"ba abunda kike tunani bane don Allah ki bari in kaita zan miki bayani daga baya".

    Amina kin sakeshi tayi ga karfi kaman doki haka ya rasa ya zaiyi da ita ga Amrah rai a hannun Allah don jini ne yake fita a kanta,
Fahad ne ya shigo  da motansa mai gadi ya bude kofa kenan ya hangosu a tsaye, da sauri ya bude motansa ya fito ko kasheta baiyi ba, Karban Amrah yayi  da sauri yasa a motansa sai asibiti ido Amina ta rufe tace ba inda Jamal zaije hasali ma kuka ta fara yi abunda ya kara gigita shi duk da ba son Amrah yake ba amma yadda yakeji game da  abunda ya faru yasan akwai rashin hankali,   kafin yace me ta mike ta dauko akwatinta
"ina zakije?"
"gidanmu, garinmu"
"don girman Allah kiyi hakuri, wallahi tallahi ba abunda kike tunani bane"
tana matsowa gefe hannunta daya da akwati yayinda dayan hannun kuma ta boye a bayanta,
"yimin bayani zangane" tana fada tana matsowa gefenshi har ya gyra tsayuwa yana tunanin karyan da zai hada mata kawai yaji abu a  cikinsa, da karfinta tasa mishi wukan da ta riko a boye
" wallahi gwara ka mutu akan kowacce mace ta dandana dadin jikinka, gwara na kasheka mu huta, wallahi baka isa ka yaudareni ba, baka isa kaci amanata ba Jamal, akan gadonmu na sunnah ka dauko karuwa!"
yadda ta caka masa haka taja akwatinta zata gudu sai kuma yadda taga yana kokarin mutuwa ta gigice idonta ya ciko da hawaye, maigadi ta kira sannan ya tayata sashi a mota dasauri ta tuka motan sai asibiti jikinta na bari, Standard hospital suka nufa   da sauri aka mika sa,    tana kuka tayiwa likitan bayanin abunda ya sameshi duk da bata ce ita ta saka mishi wukan ba, dasauri suka shiga dashi ita kuma tana tsaye  hankalinta duk ya tashi,  taga Fahad a tsaye agefe da wani babban mutum ga wata dattijuwa agefensa alamun suma suna jira ne,
'daga gani wannan karuwan suke jira anan lallema Fahad' abunda take fadi aranta kenan yayinda ta nufi kansu da karfi
" Fahad baka da amana, ina ce kana gani cewa yayanka ya dauko karuwa ya kawo min cikin gida shine harda kawo ta asibiti da hadin bakinsa ko? meyasa baka da kishi ne?" tana fada tana rike da colar rigansa, Fahad kuwa idonsa kyam kyam yana kallonta domin bai gane ina ta shiga ba balle ta fita ba, a saninsa Jamal yace secretarynsa ce don haka meye nata na cewa Amrah karuwa
" toh ai kece karuwa in ba haka ba meye ruwanki da hidimarsa da gidansa?"
" ni ce karuwa ? ina matsayin matarsa ta sunnah? "
Tttasss taji wayan dake hannun Hajiya ya fadi kasa a firgice ta karaso kanta
"kece matarsa? ta ina? innalilahi wai na ilaihi rajiun".

Abinda Aka Gasa Shi yaga WutaWhere stories live. Discover now