15

1.1K 91 10
                                    

1️⃣5️⃣Abinda Aka Gasa Shi Yaga Wuta

               Na

Benaxir Omar

         *NWA



Www.benaxiromar.com

       Ta kalli Hajiya sannan ta rike kwankwaso domin kuwa kunya bai isheta ba "kwarai kuwa, shekaranmu bakwai da aure, yara na biyu"
   Hajiya tayi lamo kaman zata fadi a kasa  yayinda Fahad bai san lokacin da ya hau ta  da fada ba
" Ashe baki da hankali ban sani ba? kina matsayin sacatariyarsa har zaki bude baki kice ke matarsa? Hajiya wallahi karya take yi"
  " a'a ba karya nake yi ba, kaima ya boye maka ne,  ina da hujjoji domin kuwa gidan dana sameshi da wannan kwartuwan gidana ne"
"KE! ki shiga hankalinki! kar ki kara ce mata kwartuwa, Jahila"   Fahad ne ya tsayar da ita  don ranshi ya matsananincin baci ji yake kaman ya wanka mata mari, Alhaji  wanda yake gefe tunda suka fara maganan ya mike ya iso kansu sannan yace "koma meye nan asibiti ne ba kuma gurin muhawara bane, ku bari su sami sauki  a san me ake ciki" ita dai Amina har lokacin abun ya dameta, a gayamata dalilin da yasa za'ace ta jira su warke, ita damuwanta mijinta ba wata kwartuwa ba, haka dai tayi shiru don ganin dattakon mutumin.

    Likitan farko da ya fito na dakin da Amrah take ne, anan yake ce musu ciwuka ne da baza'a rasa ba amma ba matsala yayinda dayan na dakin Jamal ya fito, da ya tambayi yanuwanta Amina ce ta amsa don Fahad takaici yasa ya gagara sanin wani matsayi zai ajiye Jamal, itama yace mata wukan bai shiga sosai ba, insha Allahu ba matsala.

  
   Haka suka jira daga baya Alhaji ya nufi gida yayinda Fahad na zaune yana jira yaji tashin Amrah, da zai iya daukan radadin ciwonta ya musanya da Son da yake mata,Hajiya idonta na kanshi ta lura yayi duhu yayi baki don haka tace "Kaci abinci kuwa?"  ya girgiza kai anan ta diba masa ferfesun ganda da aka kawo  ta hada masa tea sannan tace yasha, duka da yaji nauyi amma ya zage yaci, alokacin Amrah ta farfado idonta akanshi tayi murmushi wanda ya daure masa kai,domin rabon da yaga wannan murmushin tun tana asalin Amrahnta

  "Hajiya lafiya kika yi tagumi? nace baya miki kyau kin ki yadda" nan da nan Hajiya ta mike domin tabbas muryan da maganan na asalin Amrahnta ne ba wacce ta sami matsala ba

Abinda Aka Gasa Shi yaga WutaWhere stories live. Discover now