SHAFI NA GOMA SHA DAYA

188 24 0
                                    

BAKAR ZUCIYA


TRUE LIFE STORY


NA

Basira Sabo Nadabo


Shafi Na Goma Sha Ɗaya

Ya cigaba da masifa kamar an ɓalle kan panpo ya juya tare da cewa

"Yanzu ni ƴar nan zata tonawa asiri ni take son wulakantawa ko, to wallahi kafin ni na wulakanta saina fara wulakanta rayuwarta ƴar isar yarinya wacce tayo gadon halin uwarta na tsiya toh wallahi dani take zancen zan nuna mata kurenta shegiya matsiyaciyar uwa wacce ta haifomin annoba a gida, ita kuma Amatul'Kareem ɗin zanje har gidan uwar uwar nata naci mata mutunci ƴar da bata gaji arziki ba sai tsiya, zata gane kuren ta dani" ya fita ta nan ya bullo ta nan haka ya dinga matsifa kamar yau ɗinne akace masa ya faɗi zaɓe

Aunty Salima ta sauke gauron numfashi tare da cewa

"Wallahi Allah nasan za'a rina, wai yama za'ayi kacewa Amatul'Kareem taje asibiti a zubar mata da ciki kuma ka dawo ka zauna har kayi tunanin zataje asibitin aiko wannan tsohuwar kakar nata bazata yarda taje ba, kawai ni ina ganin mafita shine ka tashi muje gidan su Ama ɗin koda ƙarfin tsiya ne mu ɗauketa mu kaita asibiti acire cikin nan, donni wallahi Alhaji ban shirya jin mummunar labari akan faɗuwar ka zaɓe ba wannan shine kawai mafita agare mu ehe"

"To toh kuma fa kin kawo shawara donni kaina kullewa yayi bana iya tunanin komai, kai Allah nagode maka daka azurta ni da mace tagari don ko acikin mata ba kasafai ake samun irinki ba zinariyata, barin tashi muje koh Hajiyata" ya faɗa cikin washewar baki kamar gonar auduga ko kuma nace kamar yaune aka faɗa mishi yaci zaɓe


( Dama Alhaji Ali ya za'ayi mutane su samu mata irin naka ai sai dai kai ɗin, don ko acikin mutane kaima samun irinka sai an tona Allah dai ya kyauta Amin, Nakuma cewa Uhmmmm)

Haka suka ɗungumi jiki don zuwa gidan su Amatul'Kareem suna zuwa kofar gidan Oppa ma yana zuwa ko kallon su bayyi ba domin kuwa yasha kanshi ta ɗauki caji, Aunty Salima ce tace

"Alhaji wannan ba Abdul'Kareem bane?"

"Shine mana me kika gani"

"Gani nayi ya wuce ba tare daya kallemu ba balle mu samu arzikin gaisuwa"

"Barni da ɗan abu kazan uwa dani yake zancen zanyi maganin su daga shu har kakar tasu mai ɗaure musu gurin zama"

"Alhaji muje kaga dare nayi Allah dai ya nuna mana cin zaɓen nan wallahi sai nasa an ɓatar dashi a doran kasa shegu masu halin uwar su"

A tare suka shiga cikin palon gidan ko sallama basuyi ba, yayi dai dai da fitowar Amatul'Kareem daga kitchen ɗauke da faranti da kofuna akai, tajin sallamar su tasake farantin kofunan suka tarwatse a kasa, faɗuwar farantin shine ya jawo hankalin su Mama Kaka da Oppa daga hirar da sukeyi, Mama Kaka tayi saurin mikewa saboda tasan za'a rina tunda har Amatul'Kareem taki zuwa asibitin nan, cikin sanyin murya Mama Kaka tace

"Barkan ku da zuwa Alha...."

Bata kaiga karasawa ba Aunty salima ta katse ta da cewa

"Ke tsohuwar duniya ba gaisuwarki mukazo jiba kuma ba dogon sharhi muke bukata ba zuwa mukayi don tafiya da waccen ƴar iskar yarinyar don zuwa cire mata shegen ɗan data ɗauko mana kuma saboda wannan shegen abun mijina yana iya rasa kujerar takarar da yake nema kun gane ai, ke kuma Amatul'Kareem ki shige ki ɗauko mayafinki ki fito mutafi don ba zama mukazoyi ba"

"Aiba saita ɗauko mayafi ba ahakan ma zamu iya zuwa don ni banga abinda zata rufe a jikinta ba tunda harta iya kai kanta gurin namiji to kuma me yayi saura Hajiyata?"

"Babu fa Alhajina, ke shegiy....."

Kafin ta karasa maganar Amatul'Kareem ta ɗauke ta da wani wawan mari tare da cewa

"Kece shegiya amma ni kinga uban daya haifeni a gefenki, kuma da kike cewa muje azubar da abinda ke cikina toh wallahi daga ke har mijinki kunyi kaɗan babu wanda ya isa ya zubar da abinda ke cikina domin ɗan dake cikina da uban shi kamar yadda na kasance ƴa ga sokon mijinki gashi a tsaye, ke Salima idan har baki cire bakinki akaina ba wallahi Allah saina zubar miki da hokora"

"Amatul'Kareem ashe baki da kunya ban sani ba"

"Yanzu aika sani ko, wallahi kaga cikin nan (ta faɗa tare da shafo cikin) babu wanda zai zubar min dashi kuma duniya da yardan Allah sai ya taka shi har yayi tsalle, sannan kace bakaga abinda zan rufe a jikina ba aini klakancina bai kai nan ba domin har gobe inajin kaina yadda bakayi tsammani ba wallahi ALI kayi kaɗan da zaka tako cikin gidan ummata kacimin mutunci, kai daga yau karna kara ganin karen kafarka a cikin gidan nan tare da jakar matar ka Salima kuma duk randa kuka kuskura kuka shigo gidan nan wallahi tallahi sai an fita da gawan ɗaya daga cikin ku, kuma in kuna ganin ƙarya ne gobe kuzo a shirye nake da in kashe koma waye a cikin ku musamman ma ke Salima, kai kuma ALI bazan kashe kaba amma ina addu'ar kafin ka mutu saika girbe abinda ka shuka, da kanka zaka tonawa kanka asirin abinda ka kullawa wanda kake gudun karna kunce, ga hanya nan yanzun nan ku fice mana acikin gida tun kafin nayi ajalinki Salima ku fita nace" ta karashe maganar cikin tsawa har saida ta tallafe cikinta

Da gudu Aunty Salima da Alhaji Ali suka fice daga gidan

Oppa ya taso cikin murmush yace "Kin birge ni kanwata kin amsa ƴancin rayuwarki da hannunki tabbas yau ina cikin farin ciki"

"Yanzu abinda kika yiwa uban daya haifeki yayi dai-dai kenan Ama uba fa uba ne koda kuwa yana yankan naman jikinki ne"

"Ga wani uban kenan Mama Kaka amma wannan uban ya riga da ya kwashe kayanshi a gaban Ma'aiki bashi da sauran kimar dazan kalle shi a matsayin uban daya haifeni sai dai na kirashi da azzalumin uba, munafikin uba" duk cikin kuka take magana

"Rabu da Mama Kaka kanwata kinyi abinda ya dace dake don daman da bakice komai ba wallahi Allah da yau na zane mutan wofin cen amma yau ina alfahari dake kanwata"

GIDAN ALH ALI

Falon yayi tsit sai sautin kukan Aunty Salima yake shi kanshi uban gayyar ya rafka uban tagumi duk abin duniya ya dame shi, ya janye tagumin tare da cewa

"Yanzu Don Allah bazakiyi shuru ba ni kaina wannan kukan naki karamin damuwa yakeyi don Allah Salima kiyi hakuri ni nasan matakin dazan ɗauka"

"Mataki! Mataki fa kace!! Yanzu kai har kana da wani matakin da zaka ɗauka wanda ka kasa ɗaukan shi a lokacin daya dace tunda har ƴar cikin ka zata ɗaga hannu ta bare ni ka kasa ɗaukan mataki sai yanzu zaka cemin zaka ɗauki mataki, toh wallahi Alhaji barina faɗa maka marina bazai tafi abanza ba dole saina rama ko kuma ka biyani taɓa lafiyar jikina da ƴarka tayi" duk cikin kuka take magana

"Eh naji kuma na abince inhar hakan zaisa kiyi shuru dayin wannan kukan don jin kukan nakeyi kamar garwashin wuta acikin zuciyata don Allah kibar kukan nan" ya faɗa cikin rarrashi



Don Allah readers ku faɗa Alh Ali wani irin uba ne donni kaina kullewa yayi hmmmm. Na kuma cewa dai uhmmmmm


Vote!
Vote!!
Vote!!! 🌟

Karamar Su Babban Suce Ni Wato Ƴar Mutan KD Ce

Basira Sabo Nadabo

Follow nd Vote On Watpad @ Basira-Nadabo

BAKAR ZUCIYA Where stories live. Discover now