BIYAR

500 54 4
                                    

Tun ina da kananan shekaru nake kokarin kwatanta aikin gida musamman girki. Gyaran dakin mama da kewaye kuma wannan tuni na kware akai. Idan mama taje aiki, da taimakon dada sai na hada abincin gida wanda za mu iya ci ni da ita da yara, wani lokaci har daddy. Dan kuskuren da zanyi irin na mai koyon girki, Dada zata gyara min, ko kuma idan daddy yazo ci yace "karima kin yi kokari, amma next time ki rage kaza ko ki kara kaza maimakon kaza." Daddy yasan kan girki, saboda a lokacin farkon zama na dashi da mama kafin zuwan dada, har girki ya keyi idan ya taje makaranta ko bata da lafiya. Wani irin mijine ga mama ni kuma uba a guna na nuna ma sa'a. Mutun ne mai bawa kowa hakkinsa ga saukin kai. Tsaurinsa mafi akasari akan khalid ne, sai dai duk saukin kansa hakan bai hana shi tsawatarwa idan aka kuskure ba koda mama ce, zai tsawatar kuma yayi gyara yadda ya kamata. 

Ban cika hulda da kawaye barkatai ba, duk da haka ina da kawaye da abokan karatu. Daga baya ban san yaya a kayi na kara kebance kaina daga huldayya da 'yanmata irina, haka kawai sai ina ga kamar zasu gane halin da nike ciki game da abubuwan da uncle tasiu ya ke aikatawa dani su dinga fadi ana kira na 'yar iska. Wannan yasa ake gani kamar girman kai ne. Daga hakan sai tsegumi ya fara yaduwa a makaranta ta hanyar wasu yara da suka san cikin unguwarmu aka kirkira zance wai ni 'yar buzaye ce mama ta dauko kafin ta samu haihuwa shi yasa bani kama da ita da 'ya'yanta. Kuma shi yasa ake kirana da karima jafar 'yayanta kuma Ahmad Aminu da hafsat Aminu. Wasu kuma suce wai daga gidan marayu aka daukoni. Akan wannan maganar sai da mama da daddy suka je har makaranta aka tsawata tare da hukunta yaran da suka assasa maganar. 

Ina zangon karshe na aji hudu a sakandire, mama ta kara haihuwar yaronta na uku Muhammad. Tun a lokacin duk da kuruciyata ina da hips da suka sa ko wando (trouser) na saka daga nesa za'a san karamar budurwa ce ni, a wannan lokaci siffofin mata suka fara bayyana a jikina. A lokacin karamar budurwa ce ni, amma shape dina ko a lokacin baya boyuwa. Sai kuma karin an tarbiyyantad dani da saka kananan kaya, irin tarbiyar gidan 'yan boko masu kwatanta dabi'un zallar bokon a yanayin sanya sutura, duk da ko nayi karatun islamiyya. Saboda a idon daddy da mama ni yarinya ce. A wadancan shekarun, ilimin addini a ibadance ina yi an koyar dani, sallah, azumi da tsarki. Karatun Kur'ani da sauran littafai duk babu matsala ana koya min a makaranta da islamiyya, amma a wajen sanya sutura ba wani abu bane in saka wando da karamar riga tare da mayafi karami.  

Ko kuma matsatstsen skirt ko da fita za muyi a cikin baiwar jama'a.

Bayan arba'in din Muhammad ne na fara samun kwanciyar hankali a zahiri. Ina tsakiyar zana jarrabawar shiga aji biyar na sakandire wato SS2, a wannan lokacin ne aka kama uncle tasiu da budurwa mai suna Nasima a dakin maigadi turmi da tabarya. Ance maigadi ne ya tona ma sa asiri saboda ya gaji da halayensa. Ranar weekend ne kowa yana gida. Hankakin Daddy ya tashi kwarai, daga karshe ya koreshi daga gidan. Mama tayi kuka sosai, tayi da na sanin dauko tasiu ya zauna gidanta da sunan taimako da zumunta. Iyayen yarinyar 'yan ghana ne dake zaune anan kano, muna zaune dasu lafiya, amma akan wannan case din suka fara barazana zasu kai kotu wai tasi'u ya bata musu yarinya. Daga baya ne aka samu maganar ta mutu saboda an samu shaidu cewa ba tasiu kadai take kulawa ba. A kayi ta zagin tasiu da yarinyar, a lokacin ji na keyi kamar na fadi abubuwan da tasiu ya dade yana aikatawa a kaina cikin shekaru kusan shida da yayi a gidan. Amma da naji yadda ake la'anta da zagin nasima sai na kama baki na nayi shiru kar a fassara ni a 'yar iska yadda a ke ta zagin Nasima. Amma kullum ina tunanin abin tunani irin na kuruciya da rashin mafita da rashin sanin abin yi. Ga munanan mafarkai da ke damuna a koda yaushe.

Rayuwata taci gaba da tafiya, a zahiri ina nan a yarinya mai cikkakiyar lafiya da hankali, amma nayi bala'in tsanar maza a raina. Dukansu da yanayin tasiu nake kallonsu. Ina kara girma ana kara yaba siffata, kamannina da kwazona. Ni kuma ina kara tsanar ma'amala da maza. Ahmad da su ummi kamar an bani gadin rayuwarsu nike ji. Ba naso a fita dasu. Abinda ke hada ni da khalid kenan. Idan yazo fita dasu zan dinga jaye jayen da zai sa su dade basu fito ba. Hakan ke hassala shi, kuma ga daddy ya sa doka kar ya kara duka na, idan ya hasala sai ya dinga ce min wallahi zai sa a mayar dasu gidan hajiya yaga iyakar son kanne. Har ce min yake "muguwa dangin chinese" ko yace, "Anty Hadiza da ta haifesu bata yi iko dasu ba sai ke kwashe kwashen dangi, sai nayi maganin rashin kunyar ki". 

A irin waannan lokutan mama ce take kashe maganar ta hanyar tsawata min akan kar in kara hana su Ahmad fita da khalid. To su ma yaran haushi na su keji idan na so hana su zuwa wajen khalid.

A makaranta komai da himma da kwazo ni keyi, ni ce a kowanne club, ni ce school queen tun ina jss, Idan za'ayi bako a makarantar mu ko wani taro yanzu za'a nemo ni a shirya ni, in bashi kyauta. Har gwamna da yazo makarantarmu ni aka sa na gabatar mai da kyautar karramawa. Na iya rawa kamar diyar kabilar TV. Nayi ta juya jiki kamar bani da kashi a jikina. Kowa sona ya keyi ina ba mutane sha'awa, amma ni maza ne bani so ko kadan, ko malamai maza bani iya sakewa dasu. A raina ina fassarasu a matsayin mugaye. Idan a kace wata za tayi aure maimakon farin ciki sai na dinga jin haushi da kunci, tun ina JSS da na fara fahimtar lalle ana aikata kwatankwacin abinda uncle tasiu yake aikata min a gidan aure

A bayyane ana kallona 'yar gata mai nasara da sa'ar rayuwa wato "perfect child", amma zuciyata da ruhina suna dauke da wata irin kebantacciyar damuwa mai kama da cutar da ba'a gani. Wani duhu ke zuwa yana mamaye ruhina daga lokaci zuwa lokaci musamman idan na gani ko na ji labarin mu'amalar mace da namiji ta aure ko makamancin haka.Wasu lokutan kuma haka kawai zan dinga jin tsoro da bacin rai babu gaira babu dalili. Daga na fara jin haka sai na samo littafan makaranta nayi ta karatu ko kuma na kirkiro aikin gida. Shi yasa ba a cika gane halin da nike ciki ba. A islamiyya da malam yace Kur'ani yana yaye damuwa, sai na dinga karantawa a gida duk lokacin da na kare sallah. Kuma tabbas ina jin tsoron yana raguwa a duk lokacin dana karanta.

Kusan mu kare sakandire, lokacin na kara girma na kara farinjini da kyau, amma zuciyata har a lokacin tana dauke da wata cuta boyayya da ba'a ganewa sai ni kadai na sani sai Allah da Ya halicceni. Mafarkaina da tunani na basu da kyau, babu nutsuwa cike suke da tashin hankali. Shi yasa nike kokarin boye damuwata na dukufa aikin gida dana makaranta. Da kuma kwalliya da sauran abubuwan da nasan zasu amfaneni. Duk namijin da ya nuna yana sona to ya zama makiyina. Kuma.ba zan kara ganin mutuncinsa ba. Mama da daddy kuma basu yarda namiji ya  takurani da maganar soyayya, saboda a cewarsu yanzu na fara karatu. Don haka tsanar da nayi ma maza tazo daidai da ra'ayin su.

Mahaifina kafin ya rasu yana da wani aboki, amini kuma ubangida, Alhaji zaki sunanshi. Ya rike amana sosai ko bayan rasuwar mahaifana. kayan sallah da kudi duk yana aiko min har hutu mama da daddy suke tura ni a gidansa a garin sokoto, a wata unguwa da ake kira Arkilla. Amma asalin baba zaki daga garinmu yake wato yabo.

Bayan da na fara girma ina zuwa tare da Ummi ko Ahmad sai dai bani dadewa kamar lokacin da nike karama nike zuwa ni kadai. Alhaji zaki yana da babban 'dansa mai suna Auwal, mafiyawa shi yake aikowa da sakona idan zaya zo kano sarin kaya ko wasu harkokin da suka shafi kasuwanci. Auwal ya san gidan daddy sosai har can gidan hajiyar khalid a na'ibawa duk ya sani. Saboda a lokacin da mahaifinsu daddy yana raye, sunyi mutunci da Alhaji zaki sosai a sanadiyyar auren mama, har suka zamo kamar yaro da ubangidansa, da yake sunyi wasu huldar kasuwanci tare musamman shigo da kayan dakuna irin su gado da kujeru. Auwal yayi karatu zuwa matakin karamar diploma a makarantar Umaru Ali Shinkafi dake a garin sokoto. Amma harkar kasuwanci irin na mahaifinsa ya keyi bai samu ya ci gaba da kara karatun boko ba. 

LAIFIWhere stories live. Discover now