3

309 18 3
                                    

🖊

🎆 *_MU SO JUNANMU..._* 🎆

® *AYSHA A.R MACHIKA*

*_Wattpad~Ayshamachika1984_*


🌈 *Kainuwa Writers Association*✍

   

*SADAUKARWA GA:*

*BATUUL ADAM JATTKO*
*MAIMUNA H ABUBAKAR*
( *UMMU ONTOP*)

*_Bismillahir~rahmanir~rahiim_*


🅿3⃣



Garin yau an tashi da kwalleliyar rana mai zafin gaske.

  Jawaheer dake zaune atsakiyar falon gidansu, tayi rashe-rashe akan ledar dake shinfiɗe aƙasan falon.

  Wata ƴar yaloluwar rigace ta wani pink ɗin material mai taushi, rigar hannun shimi gareta, gaba ki ɗaya ta buga tagumi tana kallon tsakar gidan nasu da rana ta haska tar!.
 
  Inna ta fito daga ɗaki tabi Jawaheer da kallon mamaki, ta kalli agogon dake jikin bango wanda ya nuna ƙarfe goma da minti talatin da bakwai 10:37am na safe sannan tace.
 
Ke kuma lfy yau ba zaki makarantar bane?
 
Jawaheer ta sauke tagumin da ajiyar zuciya tace wallahi Inna zani, amma kinsan bana son rana haɓo nake gashi kuma yau an tashi da ita.
 
Inna ta hau gyaran zaninta tana cewa, haka nan zaki lallaɓa kuwa rana ai sai godiyar Allah kawai amma bazara ai dole ayi rana kam.
 
  Jawaheer bata sake cewa komai ba ta miƙe ta shige uwar ɗaka, can ta fito da shirin wanka tayi waje.

  Mintuna ashirin ta gama shirinta cikin wata doguwar riga ta atamfa mai shuɗin kala da ratsin fari da baƙi, sai farar hijab ɗinta ƙal dan har ɗauƙar ido take saboda haskenta.
 
Ba wata kwalliya tayi ba a fuska dan daga hoda sai man baki domin lips ɗinta jajayene masu zagayen baƙi kamar tayi masu adon jan baki da baƙin gazal, amma ba ƙaramin kyau tayi ba.
 
Jikinta sai tashin ƙamshin turaren Fashion yake.

  Ta kalli Inna tace toni zan wuce Inna kada nayi latti dan sha biyu muke da aji, zan ɗanyi karatu kafin lokaci ya ƙarasa, Inna tayi mata addu'ar samun sa'a da Allah ya tsare sannan Jawaheer ta warware niƙaf dinta ta ɗaura akai.
 

  Haka take indai zata fita wajen unguwarsu toh da niƙaf ɗinta a fuska, ba wai dan kada aga fuskarta take sanyawa ba, a'a rana ce bata son tana dukan mata fuska acewarta wai fuska koɗewa take kayi baƙiƙƙirin.

  Ƙarfe huɗu saura kwata suka gama lectures ɗinsu ta wannan rana.

Dan haka sai da tayi sallar la'asar anan cikin masallacin makarantar sannan ta fito ta tsaida mai keke napep tana gaya mashi kasuwan sabon gari zai kaita.

  Da niyyar yanko yaɗin hijabai taje kasuwar, amma kuma saita fasa ta siyo masu ƙaton risho (Stove) na silver ta juyo zuwa gida zuciyarta fal murna.

  Saboda dama ta daɗe tanada wannan burin.

  Ta gaji da ganin idanuwan Innarta na zubar da hawayen hura wutar icce, daga yau in sha Allahu sun gama girki da icce.

  Akan hanya ta siyanma Babanta lemo da ayaba harda kankana da abarba, dan aɗan kwana biyu bai sha ba, yanzu kam tunda Haj. Aisha Umma ta basu kuɗin da take basu duk ƙarshen wata da kuma sauran kayan amfanin gida jiya da daddare, ai dole su ɗan ji galmi-galmi suma.

  Lokacin data isa gida Inna na zaune atsakar gida da Babansu agefe kwance yana shan iska.

  Ita kuma Innar tana jiran dawowar Ubaid daga islamiyya ya sawo mata iccen girkin dare.

  Jawaheer tayi sallama cikin sanyin nata kai tsaye inda suke ta ƙarasa ta aje ledojin hannunta.
 
  Inna ta bita da kallo tace, ke kuma waɗannan kayan fa?
  Cikin fara'a Jawaheer ta buɗe leɗar risho ta fiddoshi waje tana faɗin, Inna risho na sawo mana domin sauƙaƙa wahalar iccen nan.

  Innar ta harareta, yanzu Jawaheer kuɗin yadin hijaban ne kika kashe?

Aike kika sani kuma, Jawaheer ta kwaɓe fuska tace.
 
  Inna nayi maneji da nawa kafin wani lokacin, amma gaskiya na gaji da walahar da kike ta hura wuta, haka kawai idanuwanki su mutu da wuri.
  Inna tace toh Allah yayi maki albarka.

  Jawaheer ta miƙe taje ta gyaro kayan marmarin nan ta zuba acikin plate bayan ta ɗibar ma Babanta nashi ta miƙa sauran wajen Innar dake kiciniyan sanya lagwanin risho.

  Ita kuma Jawaheer ta matsa inda Babanta yake kwance yana jinsu amma babu halin motsi maganarshi ma ba ko wacce ke fita dai-dai ba.
 
Baba ga kayan marmari bari na baka, ta zauna sannan ta tayar mai da kai ta jingina shi ajikinta, ahankali ta ɓare ayaba tana bashi yana ci sannu-sannu suna fira da Innar har Ubaid ɗin ya shigo aka maidashi siyan kananzil.

            *************

  Rayuwa akwana atashi dai babu wahala, yau Alhamis da la'asar sakaliya Khaleed ya shigo gidan Ummu, lokacin Jawaheer tana kitchen tana ma Umma aikin abinci, kamar ko wane lokaci dai tuwo ne amma na shinkafa da miyar shuwaka, wanda ƙamshin miyar duk ya karaɗe ilahirin gidan.
 
  Khaleed ya buɗe frigde yasha ruwa sannan ya zauna ƙasa kusa da Umman shi dake zaune kan kujera, kamar koda yaushe ya ɗora kanshi kan cinyarta ita kuma tana shafar kanshi.
 
Umma gobe fa ne zan wuce Lagos na gama shirye-shiryen tafiya India da Dubai ɗin.

  Gashi kuma har yanzu ba kiyi mani maganar da kikace ba, ta sauke numfashi ba tare dajin ko ɗar ba tace, gidanka ɗakuna nawa ka sanyama kaya?

  Bai kawo komai aranshi ba yace, ɗakina kawai na sanya sai kuma falo, tace toh kana dawowa asanya ma sauran ɗakunan funitures, kitchen ma ashiryashi da abinda ya dace.
 
Ya ɗago kanshi cikin murmushi yana kallonta yace Umma aure zakiyi mani ne?
  Itama murmushi tayi tace, kwarai kau auta, zamanka haka ya isa, babu abindaka nema ka rasa dan haka na sama maka matar aure sai dai basu dashi dan haka mu zamuyi komai, in kuma kanada wacce kake so toh kayi magana.
 
Ya maida kanshi ƙasa yana faɗin bani da kowa Umma, dama inada niyyar maki wannan maganar asamo mani mace inyi aure.
 
  Umma taji daɗin maganarshi, dan dama bata da fargaba akanshi, taci gaba da magana, toh inka tafi wannan tafiyar ina so ka haɗo lefe daga can, ni kuma nan kafin ka dawo za'a gama magana dan bansan aɗauki lokaci mai tsawo.

Sannan ina gargaɗinka bana son 'yan uwanka mata susan kai kayi mata komai saboda gudun gori wataran, haba Umma ni ina ruwana da irin waɗannan maganganun kuma.
 
  Sukaci gaba da firarsu har aka kira sallar magriba, ya miƙe yana sosa ƙeya Umma bari na dawo sallah naci abinci domin tun ɗazu ƙamshin ya cika mani ciki.

  Harya juya sai kuma ya dawo, Umma wacece matar tawa?

  Ba zaka ganeta ba ɗiyar Mal. Umar ce Jawaheer tanama kitchen ƙamshin abincinta ne kakeji, ya juya yayi hanyar kitchen ɗin tabbas yasan yarinyar tana ƙarama amma yanzu bai santa ba.
  Ɗan leƙawa yayi kitchen ɗin inda ya hango Jawaheer ta juya baya sanye da hijab ɗinta har ƙasa da alamar wanke-wanke take, baiga fuskarta ba ahaka ya haƙura ya bar wajen domin gudun kada jam'i ya wuceshi.

  Ita kuma jikinta ne ya bata ana kallonta, ta juyo amma sai taga wayam sai ƙamshin turarenshi kawai ke tashi awajen, ta ɗanja tsaki halan wannan shagwaɓaɓɓen autan Umma ne, domin ɗazu tazo shigowa falon ta hangoshi kwance kan cinyar Umma.
 
  Bata tsaya ganin fuskarshi ba tayi saurin juyawa ta koma, mafarin maida hijab ɗinta ajiki kuma kenan koda zai shigo akan rashin sani.
 
  Ta riga ta kammala komai dan haka ko sallah bata tsayayi ba tayi ma Umma sallama ta wuce gida.






~MACHIKA~

MU SO JUNANMU...Where stories live. Discover now