🖊
🎆 *_MU SO JUNANMU..._* 🎆
® *AYSHA A.R MACHIKA*
*_Wattpad~Ayshamachika1984_*
🌈 *Kainuwa Writers Association*✍
*SADAUKARWA GA:*
*BATUUL ADAM JATTKO*
*MAIMUNA H ABUBAKAR*
( *UMMU ONTOP*)*_Bismillahir~rahmanir~rahiim_*
🎆 *Zuwa gareku masu karatu, da fatan za'ayi mani afuwa domin post zai koma sau biyu asati sabosa hidima da tayi mani yawa, ga kuma karatu inayi lokacin da nike samu kaɗanne, ina tare daku da iznin Allah yabawarku shine ƙarfin gwiwwata*🎆
🅿6⃣
Ganin tana tahowa inda yake tsaye ya bashi damar ƙare mata kallo.
Doguwa ce amma ba can ba, tanada hasken fata sai dai ba fara bace irin tas ɗin nan, domin ta fishi hasken fata, siririya ce amma ba irin wadda ke numa rama ba.
Tanada nonuwa tubarakallah da kuma mazauna sai ƙirar tata ta ƙara mata kyau, afuskarta tanada dogon hanci kamar biro da matsakaitan idanu masu hasken gaske, sai baki ƙarami mai ɗan tudun laɓɓa.Data matso inda yake sosai ya lura da gazar-gazar ɗin gashin idanuwanta da kuma na gira wanda suke kwance luf abinsu.
Can cikin shaƙewar murya ya furta tsarki ya tabbata ga mahaliccin wannan halitta, masha Allah.A hankali ta miƙa hannuwanta ta karɓi ledojin hanunshi murya can ciki tace sannu da zuwa.
Ya jita amma bai amsa ba sai bin bayanta da kallon da yayi yana ganin yarda take tafiya kamar yanga, wanda halittarta ce haka da kuma jikinta dake rawa domin ganin Khaleed karo na farko da tayi.
Sam bata taɓa kawo ma zuciyarta cewa Khaleed ɗin ya haɗu haka ba, ita bacin gata da Allah yayi mata aitasan bata kai matsayin da irinsu Khaleed zasu kalleta ba balle suce suna so harsu aura.
Lalle dole ta ƙara gode ma Allah da Ummu da tayi sanadin aurensu.Khaleed da ƙyar ya samu kuzarin tako ƙafafunshi ya idasa shigowa cikin falon kai tsaye ya zarce ɗakinshi.
Ta buɗe ko wace leda domin ganin abinda ta ƙunsa, sannan ta adana komai inda ya dace, ledar kajin kuma ta kai kan dinning table ta aje tare da plate da kuma wuƙa da cukali mai yatsu.
Sannan ta wuce ɗakinta, shi kuma can yana shiga wanka yayi ya shirya cikin kayan baccinshi masu taushi sai tashin ƙamshin turarikan daya fesa yake, daga baya ya fito falon.
Ganin bai ganta ba sai yaji babu daɗi haka kawai, dan haka ya ɗauki ledar da plate ɗin ya nufi ɗakinta, awani ɓangare yana mamakin kanshi.
Yayi sallama har sau biyu jin ba'a amsa ba yasa ya murɗa ƙofar ya shiga kawai.
Cikin takunshi guda-guda jiki asanyaye ya nufi cikin ɗakin domin hangota da yayi kwance ta juya ma ƙofa baya.
Ahankali ya aje kayan hannunshi agefe guda, sannan ya ƙarasa bakin gadon ya miƙa hannu kan kafaɗarta yana ɗan bubbugawa alamun tashinta.
Cikin baccin daya soma ɗibarta mai daɗin gaske taji wani ɗumi da taushi kan jikinta tare da murya mai daɗin gaske ana kiran sunanta.
A firgice ta ware idanuwa tare da juyowa gaba ɗaya wanda yayi sanadin afka mashi da tayi suka zube kan carpet ɗin dake malale gaban gadon.Gaba ɗaya suka zuba ma juna ido domin fuskokinsu na dab dana juna dan tsinin hancinan su suna shafar juna, sannan dukkansu suna shaƙar numfashin juna.
Second wajen arba'in suna ahaka dan gaba ɗaya sun fita hayyacinsu na wasu daƙiƙu, domin gaba ɗayansu wannan ne karo na farko da jikunansu suka taɓa haɗuwa dana banbamcin halitta.
Jawaheer ce ta soma dawowa cikin hayyacinta dan haka ta miƙe da sauri daga kan jikinshi tana zazzare idanuwa, shi kuma yana a kwance ya lumshe ido sannan ya matse kafafuwa domin karo na farko da yajishi cikin wani baƙon yanayi da bai taɓa ji ba.
Ya dinga sauke numfashi ahankali har ya ɗan samu natsuwa, sannan ya miƙe yana kallon yarda ta takure guri guda kanta aƙasa kamar wacce tayi ƙarya ko aka kama tayi wani babban laifi.
Murya ashaƙe yace mata, kinci abinci?
Ta ɗaga mashi kai alamar eh, yace toh juye mana kajin can a plate ko?
Ba tace komai ba ta miƙa hannu ta ɗauko ledar ta juye, duk yana ƙare mata kallo.Cikin zaman kurame sukecin naman, gaba ɗaya ya zuba mata idanuwa hakan yasa duk tajita atakure, ta dinga tsakurar naman kaɗan-kaɗan tana turawa kamar mai cin magani.
Gwanda ki zage kici kinsan ita kazar amarci bata cika daɗi ba dama, taji saukar furucin asama kawai ya shiga kunnuwanta.
Ta ɗago da sauri tana zare ido ta kalleshi, ganin haka yasa yayi murmushi domin yana sane yayi mata wannan zancen danya kawar da shirun dake tsakaninsu.Ganin ta maida kanta ƙasa ta daina cin naman yasa ya kawar da maganar ta hanyar kawo ta makaranta.
Yaushe zaki koma school? Cikin sanyin murya tace yau aka koma ai.Ke yaushe zaki koma? Ya sake jeho mata tambaya, duk lokacin daka ce in koma, ta bashi amsa, ya ɗanyi shiru yana nazarinta sannan yace, ki shirya gobe ki koma makarantarki, akwai wani abu da kike buƙata na makarantar?
Ta girgiza kai, magana zakiyi ba da kai ba, a'a tace ataƙaice.
Shiru ya ɗan biyo baya na daƙiƙu, zuwa can ya miƙe yace mata sai da safe toh, daga haka yayi gaba tabi bayanshi da kallo.
Sai da ya fice ta sauke ajiyar zuciya sannan sai tayi murmushi ta gyara zama ta hau cin kazarta hankali kwance.
Ƙarfe sha biyun rana take da lectures dan haka sai data gama gyara gidan tas tayi masu abinci sannan ta shirya cikin wata doguwar riga ta lace maroon da ratsin lemon green mai ɗigon-ɗigon stones masu ƙyalƙyali.
Ta gama shirin ta ɗauko hijab ɗinta lemon green ta sanya wadda ta sauka har ƙasa, sai jakka da talalman ƙafarta suma kalar hijab ɗin.
Tayi sallama afalo Khaleed yana tsaye yana ɗaura agogo sanye yake cikin ƙananan kaya sunyi mashi matuƙar kyau.Lokaci ɗaya suka kalli juna suna yaba kyawon da kowannan su yayi ma ɗan uwanshi.
Har cikin zuciyar Khaleed yaji daɗin yarda yaga Jawaheer tayi shiga cikin kamala ta mutunci.
Kanta aƙasa taje kusa dashi ahankali tace na gama shirin, toh muje in saukeki domin nima zani gidan Umma.
Saida ya shiga da ita har cikin makarantar bayan yayi fakin ya waigo yana kallonta, ita dai kanta na ƙasa danta soma fahimtar mayen kallo ne.
Ya miƙa hannu ya ɗauko jakkarta, tana kallonshi ta gefen ido, bundle na 200 ya jefa mata aciki ya maida mata kan cinya yana faɗin Allah ya bada sa'a.
Ahankali tace Amin sannan tace na gode Allah ya saka da alheri, daga haka ta kama motar zata buɗe zai ji tayi ya riƙe mata hannu, jikinta yayi wani ƴar lokaci guda, shima tana jin saukar ajiyar zuciyanshi.
Babu sallama zaki tafi ko angaya maki haka ake sallama da miji?
Dam! Taji zuciyanta ya buga, bari innuna maki yarda ake, ta waigo da sauri tana kallonshi ganin yana matso da kanshi inda take sai jikinta ya kama rawa.~MACHIKA~
