1-10

18.3K 435 15
                                    


Yarinya 'yar kimanin shekaru goma sha takwas ce a cikin wani daki,
sanye take da riga da wando na sanyi (pyjamas)tana kwance akan gado rabin jikinta lullube yake da bargo(blanket)me laushi,kyakkyawar fuskarta dauke take da murmushi duk da kasancewar bacci take.
Mahaifiyar ta ce ta shigo dakin ,tana kiran "Imtihal badai har yanzu bacci kike ba,maza ki tashi baccin ya isa haka mutum yai ta bacci se kace matacce"yarinya tayi mika tare da addu'ar tashi daga barci(Alhamdulillahi lazi ahyana ba'ada ma amatana wa ilaihi nushur )ta diro daga kan gado tare da duba agogo,idanuwa ta zaro ganin cewa har 12 tayi,da hanzari ta fada toilet tayi brush ta jawo towel tare da shirin wanka,fitowarta ke da wuya taje gaban dressing mirrow tayi simple make up,a nutse take tafiya zuwa wardrobe inta domin ganin kayan daze dace da lallausar fatar jikinta,ta gama dubu-duben ta,daga karshe ta tsaya akan Wata hadaddiyar Riga Maroon colour ta saka,ta jawo mayafin rigar ta saka akanta,ta fito falo domin yin break fast,tana saukowa daga matakalar bene taci karo da mahaifinta ya dawo daga office domin Friday ce, tayi saurin karbar briefcase insa tare da russunawa tana gaidasa,ta tambayansa ya aiki,ya dafa kanta tare da fadin "Alhamdulillah maminah dafatar kina cikin koshin lafiya"Imtihal tayi murmushi hade da fadin "lfy qlau Abbanah"
Ta bishi daki ta kaimasa kayansa sannan ta juyo ta fito zuwa dinning domin yin break fast,kunun tsamiya ta fara zubawa tana hadawa da kosai wanda yaji nama da kayan lambu, bayan ta gama taje kusa da Mummynta tare da gaidata,ta Shafa kanta tare da cewa "Auta kin tashi lfy?Imtihal ta gyada mata kai,sannan ta tashi daga gun zuwa main falo domin kallo,tauraron dan Adam ta fara murzawa wato (satelite) domin kallo, sae taji wayanta na neman agaji, cikin kasaitacciyar tafiyar ta me daukan hankali ta isa dakinta ta dauko wayanta tare da karawa a kunnenta tana magana a hankali cikin muryarta me laushi da dadin sauraro,bansan me aka fada mata ba amma dai naga tayi murmushi tare da cewa "am sorry Islam na sha'afa ne but yanzu Abba na gida bara na tambayesa"ta juya zuwa inda mahaifanta suke zaune ta duka gefen Abbanta tare da cewa "Abba pls ina neman iznin zuwa gidansu Islam ne"
Abbanta yace "a dawo lfy Maminah, but kada ayi dare,Mummy tace "kinga kuwa Imtihal inaso na bada sako gun telana tunda tanan gurin zaki bi se ki wuce min dashi,Imtihal tayi murmushi tace "to Mummy bara naje na shirya kafin ki fito da kayan"ta wuce dakinta ta fesa turare tayi rolling da mayafin rigarta,ta dubi kanta a madubi,tajawo takalmin ta high heel ta saka tare da fitowa daga dakin zuwa gun Mummy kar6an sakon,
kar6an sakon ta keda wuya suka fito tare zuwa gun Abba,Imtihal ta russuna ta gayama Abba zata wuce,Abba yasa hannu a aljihunsa ya fitar da key ya bata tare da ce "mata ayi driving a hankali"Imtihal tayi hamdala ga ubangiji ta duka tawa mahaifinta godiya,ta rungume mummy tana cewa ta tayata godiya,Mummy tace "Abban Afnan mungode Allah ya sanya alhairi ya kuma kara budi"ta dawo da hankalinta gun Imtihal tana cewa "ki kula da hanya banda gudu a kiyaye dokar titi"tayi Murmushi tace "nagode Mummy"tare suka fita harabar gidan domin ganin motar.

Farar mota na gani fara kirar picanto me mugun kyau koni kaina Nafeesat Anka ta tafi da imanina bare Billy giro da naga ta saki baki tana kallon Motar, a raina nace bara inje in nemi Adda Bena tare da sauran yan uwana writer's muje muyi karo2 mu siyama Jabo kalar motar nan don naga alaman zatayi kyau aciki,naji tana complain ta gaji da shiga taxi a Iran😜lol.

Imtihal ta shiga motar tare da bata wuta,tayi smiling tare da daga ma mahaifiyarta hannu,ta saki horn me gadi ya wangale mata gate tare da cewa "a dawo lfy uwar dakina"Imtihal ta harba motarta kan titi,tana tafe a hankali har ta isa shagon Adamu tela dake kan titin Abdullahi fodio tayi parking Motarta tare da shiga gurin.

🔺2⃣🔺
Ta shiga shagon tare da sallama,ta nemi ganin Adamu tela aka kirasa ta bashi kudin tare da masa bayanin cewa "tazo karban dinkin Mummy ne"ya karbi kudin, hadi da umurtar yaronsa daya hada mata kayan,ana cikin hadin kayan ne mukaji bugawar abu se kace taya ce ta fashe, Imtihal ta fita cikin sauri dmn ganin me ne ne,ai kuwa tana fita taga abunda yasa ta zaro ido, tirkashi wato sabuwar motar ce naga anfashe ma duka signals inta da hanzari muka ga Imtihal tayi gurin motar tana dudubuwa fuskarta da alamun kuka, wanda ya fasa mata signals in mota ne ya fito tare da duba gaban motarsa ba tare da yace komai ba ya juya ze koma motarsa,Imtihal ta bude kasalalliyar muryarta tare da cewa "malam baka gani ne kamin barna"juyowa yayi tare da cire glass insa tare da mata kallon uku saura kwata sannan ya tabe baki tare da cewa "haka ake parking a garinku ko kuwa titin na gidanku ne"Imtihal taji haushi sosai tace "Malam ba kada tunani ne!ya za'ayi kama mutum laifi Kuma ka dawo kana blaming mutum"ba kada ido ne, Ko kuwa ba kaga (L) learner bane,ya kara kallonta ya tabe baki,ya juya ya shiga motarsa kaman wanda zeyi wani abun kirki alokacin ne kuma yaron Adamu ya iso da kayan ya bude front seat ya Sama ta kayan.

IMTIHAL (COMPLETED) .Donde viven las historias. Descúbrelo ahora