65

2.4K 257 10
                                    


🔺6⃣5⃣🔺
Sabida sanin kanki ne bazan ta6a iya kashe Muhammad Basheer ba,
ko don sonda nake masa da irin hallacin da kuka min a rayuwa, ban kuma rabaki da shi ba sai don kinyi sanadiyar rabani da farin ciki na, shine na rabaki da naki farin ciki,duk da cewa a duk lokacin da na kalli  Muhammad Basheer ,yakan tuna min da abinda mahaifin sa ya min na rashin bani damar na fahimtar dashi, ya yarda da cewa abinda kika gaya masa gaskiya ne,
wanda hakan ya sa ya sake ni saki mai muni.....Alhj Basheer ya qatse ta da cewa umma wai zancen me kukeyi haka da yaso ya rikita min tunani, kuma wane Muhammad Basheer ne kuke magana akansa?Kaine Muhammad Basheer din da muke magana a kansa,kaine danta muhammad din da take fada.....ban fahimce me kike nufi ba umma?kafin ta ce dashi wani abu sai da ta kalli kowa dake cikin dakin wanda ta fahimci kowa na cike da son jin yanda abin yake.
tace
"ina son kowa ya zauna ya saurari ,labarin da zai fito daga bakina,dmn ku fahimci zancen da mukeyi nida hajiya.

Ta fara da cewa "na kasance ni marainiya ce bani da kowa ban san su waye
iyaye na ba kasancewar koda na taso na same ni a gidan marayu, Allah ya min kyau na fitar hankali ta yanda duk wanda yaje ziyara a gidan marayu sai ya nemi ya raba ni da gidan,amma shugaban gidan marayun baya bari sbd tsananin sha'awa ta da yake,haka yasa naci gaba da rayuta a gidan marayu wanda kullum nice ke sharewa shugaban gidan marayu office din sa, yayinda ko yaushe sai yazo ne yake bani damar naje na share masa office sbd kawai ya riqa kallona idan ina aiki, wanda ni a tunani na yana min haka ne sbd kawai na masa aiki mai kyau kasancewar sa mutum ne da baya son a masa kissa a aiki.

A kwana a tashi wata rana ina masa shara a office ban ankara ba sai jin nayi ya rufe office din ya kuma rufe ko wacce taga ta yanda ko ihu nayi baza a jiyo ni ba.

Na shiga rudu ba kadan ba ganin abinda yake shirin aikatawa,
ta qarfin tsiya yayinda na shiga yin kuka ina bashi haquri amma kwata kwata baya da niyar tausaya min,sae da Allah ya taimake ni na qwace kaina na nafi da gudu ina dukan qofa ta qarfin tsiya,wanda yayi dai dai da isowar Ahj Ilyasu da kuma matar sa hajiya Rabi'a,
wato Mahaifin Muhammad Basheer da kuma hajiya,wanda sun zo ne gurin shugaban gidan marayu dmn samun jinjirin sbd Allah bai basu haifuwa ba har tsawon shekaru goma sha daya da aure.

Jin dukan qofar da nakeyi ne yasa suka shiga dukan qofar suna tambayar lafiya me yake faruwa ne?hakan yasa shugaban gida marayu yayi saurin kimtsa kanshi yazo ya bude qofar yayinda na fito da gudu a tsorace, kan suce wani  abu yace wai fa kenkeso ne ya firgita ta haka gashi ni kuma ina bayi shiyasa duk ta rikice har ta kasa bude qofar......nan na nuna musu ba haka bane na gaya musu abinda yaso aikatawa dani,nan ya qaryata ni sai dai ganin tufafi na duk sun yage yasa aka bani gaskiya.

sosai ran alhj ilyasu ya 6aci yayinda  ya nemi a dakatar da shugaban gidan marayu har na tsawon wata uku.

Alhj ilyasu mutum ne mai kudi kuma ana ganin kimar sa shiyasa duk ya nemi alfarma ake masa ita a nan take.

Wanda har neman alfarma yayi kan yana so ya tafi dani gidan sa ba musu aka amince masa da hakan.

Ban jima da zuwa gidan su bane, hajia ta fara ciwo sosai kamar bazata tashi ba, da suka je asibiti akayi gwaji aka sanadar dasu cewa hajiya na dauke da juna biyu sosai sukayi farin ciki da jin hakan tare da godewa Allah.

Haka suka ci gaba da zama dani ba wani  abu na sa6ani da ya ta6a shiga tsakani na dasu sai mutunci,har lokacin haifuwar hajiya yayi ta haifo danta Muhammad bashir.

Allah ya dora min son dan, wanda ako yaushe yana a baya na shan nono kadai ke rabani dashi sai kuma lokacin kwanciya bacci.

Muhammad ya taso ba wanda yake yarda da ita sama dani kwata kwata baya yarda da hajiya,
shan nono kadai kesa ya tafi gurinta,daga baya ma ya cire kansa daga shan mamma tun yana da wata goma a duniya.

IMTIHAL (COMPLETED) .Where stories live. Discover now