11-15

5.1K 279 4
                                    

Sauri take tana qarawa tana tafe Tana share hawayen fuskarta saboda dukan da Inna tayimata safiyar yau Dan kawai ta makara bata tashi da wuri ba, gashi kuma tayi lattin xuwa wurin aikinta,

Tafiyar minti talatin tayi a qafa kafin ta qarasa gidan, flat ne hawa daya Wanda aka gina da red bricks wato Jan bulo,irin tsarin gidajen ingila furanni sunyi yawa gidan, rumfa daga sama hr qasa sannan ga springs na bubbugowa daga cikin dutse .....

Tana shiga cikin falon ta ci Karo da mufida fuskarta a murtuqe, gabanta yayi mummunan faduwa ta durqusa qasa tana fadin
Anty ina kwana?
Tace Ke Nainah karki maidani wata shashasha aiki na daukeki Idan baxaki iya bane Ki gayamin na sallameki akwai mutane da yawa dake neman aikin.

Idanun Nainah sukayi rau rau hawaye fal a idonta
Tace kiyi haquri Anty baxan qara makara ba dan Allah Ki yafemin 馃憦馃徎

Taja tsaki Tana fadin ku talakawan nan kamar gareku aka somajin kalmar haquri, ta juya, Nainah tace Anty ina sulaimi?

Tana gun mahaifinta idan ya gama wasa da ita xn kawo maki ita kuma Ki fitar min daga falo tun mijina bai fito ba,

Da sauri Nainah tabar falon, mufida taja dogon tsaki hannuwanta a qugunta tana kallonta hrta fice tana jin haushin Nainah sosai ba dan komai ba sai dan kyawunta,

Duk da yarinyar na cikin talauci da rashin samun kulawa kyawunta bai taba gushewa ba,  kasancewarta buxuwa take da fari sosai kamar Ja, tana da manyan idanuwa da dogon hanci, bakinta dan qaramine jawur dashi kamar tasa jan baki amma haka halittarsa take,  gashinta shine yafi daukar hankali, ga tsawo ga cika kuma baqi sosai, lokacin da mufida taga gashin Nainah sai da ta tsorata, bama mufida ba hr Inna tsoron gashinta take, shiyasa mufida Ke kishin Nainah sosai hrtake kwankwanto anya ba aljana bace ita komai tanada?

Bahijja ma haka take sai dai Nainah tafita gashi da hasken fata sosai, yasir ma da yake namiji daka ganshi kasan ciki daya suka fito dasu Nainah suna da kamanni sosai na mahaifiyarsu hrdai Nainah.

Bayan fitowar Nainah ta nufi inda masu aikin gidan ke xama, ta gaidasu kafin ta sami guri ta xauna, hajjo yar dattijuwa tana cikin masu girki ta matso kusa da Nainah....

Yar'nan mai ya hana maki xuwa da wuri hajiya na ta fada? Nainah ta janyo hannun tsohuwar suka matsa daga gefe Tana girmama tsohuwar dn tana sonta sosai,

Tace hajjo kinga yau ma Inna tayimin duka ta hanamin Karin safe dan kawai na makara ban tashi da wuri ba, Ya Yaye mata bayanta duk yayi shatin bulala rudu-rudu abinka da farin mutum duk bayanta yayi jawur, hajjo ta girgixa kanta cike da takaici

Tace kiyi haquri Nainah kibarta da Allah haqqinku Dana mahaifinku ma Ya isheta ganin isharar duniya, Ki daina kukan haka idanunki sunyi jawur, Nainah ta share hawayen fuskarta da gefen dan kwalinta,
Hajjo tace waina na nan na ajiye maki xo muje kici, ta juya Nainah nabi bayanta cike da qaunar tsohuwar,

Ta matsa kadan daga su ige dake gyaran kifi ta xauna ta soma ci suna hira sama sama cos batason surutu ko kadan, bata dauki wani lokaci sosai ba ta cinye tas,  hajjo taxo da ruwa a bokiti

Tace taso Nainah tun aiki baiyi yawa ba na wanke maki Wannan Kan, tubarakallah gaki da gashi hr baya bakya gyaransa ynxu fa ke kin girma kin xama budurwa yakamata ace kina tsabtace jikinki,

Nainah ta tashi Tana warware tubkar gashin kanta wnda da kyar bahijja ta iya daure mata shi, Duk wurin suka Xuba mata idanu kowa da abinda yake saqawa a xuciyarsa game da gashin, ta tsugunna hajjo ta wanke shi fes sai sheqi yakeyi,

Tace kije dakinmu damuke kwana akwai toilet aciki kiyi wanka Ki taje kan Ki shafeshi da mai,

Tace hajjo bnda kayan sanyawa
Tace akwai towel aciki Ki daura, kisanya hijabina na wanke maki kayan Idan sun bushe ki sanya kafin akawo maki raino.
[26/08, 10:40 a.m.] Pherty馃帳馃懐: Nainah kallon tsohuwar take, itace mutum ta biyu bayan majeed dake nuna mata qauna haka, da hanxari taje tacire ta dauro towel bayan ta xumbula qaton hijabi hr qasa taxo ta kawo wa hajjo Kayan........

Ya fito dauke da sulaimi daga part dinsa Ya nufi part din mufida bata nan Ya nufi Dakinta bata nan, jin motsin ruwa a toilet Ya tabbatar masa tana ciki tana wanka,

Ya juya Ya nufi part din masu aiki dauke da sulaimi akayi sa'a Duk suna kitchen suwaiba ce kawai Ke wanke wanke
Yace keee ina mai rainon sulaimi? Jikinta  na rawa ta nuna masa dakin da Nainah take ciki, yaja dogon tsaki Ya nufi dakin ita kuma Tabishi da kallo Tana fadi  a ranta ashe haka yake da kyawu shiyasa hjy bata bari muganshi?

Batare da tunanin komai ba Ya fada dakin da sallama, Nainah na tsaye tana taje kanta duk Ya xubo bayanta, towel ne ajikinta jin sallamar  namiji Ya sanyata qin juyowa sai dai ta amsa Sallamar qasan maqoshinta Wanda ba lallai bane Ya jiyo,

Shi kuma mutuwar tsaye yayi jikinsa hr rawa yake saboda tsabar rudewa da ganin gashinta, Duk matan da yake gani bai taba ganin mai irin gashinnan ba, bugu da qari hasken  fatarta Ya qara Jan hankalinsa,

Jin shiru a xaton ta kowaye Ya fita ya sanyata juyowa idanunta na sauka akan yatsun qafafunsa sai ta juya da Sauri batare data Kalli fuskarsa ba, hankalinta a tashe ko waye miye dalilinsa na tsayuwa bayanta? Jikinta na soma rawa kamar daga sama taji muryarsa mai sanyin gske yana fadin
Ga sulaimi nan, ya ajiyeta a saman gado Ya juya da Sauri Ya fice xuciyarsa na harbawa,

Sai da taji bugawar qofa sannan ta sauke ajiyar xuciya ta juyo tana kallon sulaimi, aikuwa tana ganinta ta wangale baki tana dariya Tana tsalle hade da miqo mata hannu alamar ta dauketa....

NAINAHTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon