41

4.2K 212 2
                                    

Bayan kwana biyu akayi discharging dinta suka dawo gida,

Komai daga sashenta Ya cnxa an sanya mata sabo, ga masu aiki birjik kamar irin na mufeedah, dakinta ma an cnxa komai kamar nashi dakin illah banbancin colour an qayata nata dakin da white and purple, murmushi Tayi Tana cije labbanta

'sai kace xn tabbata a gidannane, yake wahalar da kansa haka very soon am living ba xn iya xama da mutumin da bana so ba,

Ta xame Dan kwallin kanta,gashinta Ya xubo a kafadunta ta xauna bakin gadon tana kallon dakin, kyawunsa da tsarinsa Ya Birgeta,

'can't believe, Wannan dakin nawane, Nima Inada masu aiki xn bada umarni kamar Anty mufeedah, komai xaa riqamin, Idan akamin girki bana so fa, ta tunxure bakinta hade da dafe goshinta
'oh bana so, I dnt like it a girkamin wani, ta saki murmushi,馃槉
Idan suka min mopping baiyi ba,  how I am going to talk to them, ta daga kanta sama kamar mai naxari, oh I remember ynda Anty mufeedah keyi,
'Ke Wannan wane mopping ne haka da Kissa Idan baxaki iya ba sai in koreki in nemo wani, nooooo ta girgixa kanta
"ba haka xn ce ba, Dan Allah Ki qara mopping Wannan bai yi ba, ta saki murmushi馃槉
'correct Nainah ,ta fada ta baya ta kwanta a luntsumemen gadon,

Duk Wannan abin da take Mus'ab na tsaye bakin qofar dakin hannuwansa rungume a kirjinsa Ya xuba mata narkakkun idanuwansa, yaga tana mgn tana murmushi amma baiji me take nufi ba, a tunaninsa Nainah is happy with the room, yaga murmushi a fuskarta did she mean she is happy with the house, sai yaji yana so agama Wancan gidan da ake Dan yakai Nainah aciki baisan wane farin ciki xatayi da gidan ba, yana son ganin murmushi a fuskarta, yana son ganin qaramin bakinta na motsi dimple dinta Ya lotsa it shows her beauty,  ya juya Ya fice yana murmushi.

*

Kwanan ta biyu bata sanya mufeedah a ido ba, Mus'ab kuwa kusan kullum xai shigo dakinta ganin lfyr Jikinta,
'kina da matsala?
'ba inda Ke maki ciwo?
'me kike so?
'ina kike son xuwa?
'kina buqatar kudi?
'me xan siyo maki Idan na fita?  Duk amsar dayace babu shima fuskarta ba Walwala take amsa masa, zai juya a sanyaye ya fice, baisan mexaiyi Nainah ta saki jiki dashiba, bai San Meyasa bata sonshi ba, ya kaiwa Rauda Wannan complain,
'Nainah bata San komai akan aure ba Mus'ab Kai xaka koyarda ita sannan akwai Kunya atare da ita, ya girgixa kansa

'nooo sister ba Kunya a tare da Nainah, she hate me sister, tell me what to do.
' kanada gardama Mus'ab, nainah ta taso ba mahaifiya, yakamata ka gane, inna baxata xaunar da ita ta koya mata wani abu dangane da rayuwa ko Ta aure ba, sannan bahijja ma kanta Tana buqata ka tuna basu da lokacin kansu daga tallah  sai bauta da reno tell me taya Nainah xatasan ynda xata Tafiyar da Rayuwar ta you have to teach her ko kana tunanin majeed xai koya mata ne,  ina so ka fahimci wani abu Nainah batasan miye so ba hr ynxu, majeed shaquwa ce dake tsakaninsu hr take ganin so ne,

'ka koya mata Yanda xata soka Mus'ab, ka xauna tare da ita ko bata so, kuyi hira tare, ku ci abinci tare, kuyi wasa tare, ku yi barci tare, Meyasa ma nake Gayama kasan komai ai,

'sister amma ai bn koyawa  mufeedah hakan ba, kafin muyi aure kina ganin she takes care of me, sannan matan dake Sona a waje bn koya masu ynda xasu soni ba rushing dina suke fa ki tambayi Fahad.... Ta katsesa

Nainah dabance da mufeedah, Nainah batayi ilimin mufeedah ba, Nainah batada wayewa kamar ta mufeedah, Nainah batayi wayon mufeedah ba sannan Nainah ta taso cikin rashin gata da kulawa, a ynxu Nainah Ke tasowa kanta na wayewa, ka Barta ta shiga cikin mutane qawayenta she will have more experience ka fahimceni,

Ya gyada Kai yana kallonta,
Gobe ka Kaita inda surayya matar Fahad Ta yini a can hr dare, ka Kaita inda hajiya, kaxo da ita nan, ka Kaita gun umman mufeedah, Idan xaka iya ka Kaita family house ma, ka Kaita inda frnds dinka masu aure xata rinqa ganin ynda ake tfyr da rayuwar Aure,daga nan ma shaquwa mai qarfi xata iya shiga tsakaninku ,you get me?,
Ya riqo hannunta,
'proudly to Have you sister, kina Raina Ya sumbaci hannunta,tayi dariya sosai ta tashi Tana fadin xn shiga kitchen Abban jabir yana hanya,
'oh nama tuna munada contract da shi akan wani fili,ta juyo tana kallonsa
'bai taba gayamin ba ,me xaiyi da fili kuma?
'Amarya xai miki.... Ta soma dariya
[9/7, 12:27 PM] Pherty 馃帳馃懐: Ai ni kishiya bata bani tsoro niba irin mufeedah bace tazo mu xauna,

Mus'ab ma dariya yayi ya tashi yana laluben makullin motarsa a aljihunsa yana fadin
'Nima baxan gaya miki ba tunda bai fada miki ba inajin yana so ya baki surprise ne.

Ga dambun nama ka kaiwa Nainah in yamata dadi Idan taxo xn koya mata,

Ya Karba yana murmushi
'sister kina ganin xata Karba,
'me xai hana ta Karba ,dayan kuma ka bawa mufeedah,
'suna Godiya sister but ni fa?
'Kaci tare da Nainah ai yanada yawa.... Murmushi kawai yayi ya fice...

*

San da ya iso harabar gidan yayi parking Ya fito suka ci Karo da Inna xata shiga gidan, yasan ba dan Allah Ta xo ba sai ya tare ta,

'Inna Nainah bata gidan?
'ina taje ta tambaya tana kallonsa,
'na Kai ta saloon,
'miye saloon kuma? 馃檮
'inda ake gyaran gashi,
'Chabdi Wannan gashin akwai mai iya gyaransa ne kasan ynda gashinta yake kuwa, inta sakeshi haka take komawa kamar aljana, dama kasa scissors ka rage matashi , ya kalleta da mamaki ba abinda yafiso a jikin Nainah kamar gashinta da dimple dinta,

'tor kayi shiru ni xan tafi,
'a gaida baffa,
'baxaka ban kudin keke napep bane,
'banda kudi ynxu, ya juya Ya fice ta bishi da kallo kafin tayi kwafa ta fita daga gidan,

Sai da ya kaiwa mufeedah nata kana ya nufi sashen Nainah,
Ya shiga dakin hade da sallama Tana xaune a qasa tana sanya sajan a hannuwanta bayan ta gama sanya na qafafu, ta sanya na hannu daya bata San ynda xata sanya dayan ba,

Ta amsa sallamar batare da ta dago ba,gashinta Duk ya xubo Ya rufe mata fuska tana son tattara gashin ba hannu Ya matsa kusa da ita ya tattaro shi bayanta, Silbin gashin da tsantsinsa yasa Ya manta duniyar da yake sai ya cigaba da Jan gashin,

'Enough pls, muryarta ta katse shi, ya saki gashin yana fadin
'am sorry pls Nainah, ya dawo gabanta Ya xauna ya miqa mata dambun,
'sister tace na kawo maki dambun nama ne,
Ta saki murmushi Tana kallonsa Karo na farko da ta soma kallonsa da murmushi kusan rikicewa Ta tashi yi,
'ina son dambun nama, sau daya na taba ci馃槷a Skul dinmu, kayiwa sister Godiya Naji dadi,
'Rilly? Ya fada yana kallonta da murmushi a fuskarsa, ya gyara xamansa馃槀,ta gyada Kai
'sister tace xata koya miki Idan kina so, kuma xn iya sa a koya maki a gidama tunda kinaso,
'thanks ta fada bayan ta maida hankalinta a lallen da takeyi,
'in my life ban taba ganin mace na sanyawa kanta Lalle ba sai akanki, ina ganin su mufeedah ana xuwa ana yi masu ne sannan ban taba ganin irin Wannan naki ba su naga Idan Anyi masu xanen basa rufewa da Leda kuma flower ake xana masu asanya masu wani abu ja,

Ta Dan dubeshi kafin ta dauke kanta
'Kai ashe kanada surutu haka, yayi murmushi kawai
'tun a gida ma Nike sawa da kaina Idan anti bahijja bata nan, Wannan sajan ne ba iri daya da wanda kake nufi ba,ta miqo masa yatsunta

Help me I can't, wani dadi yaji Nainah ta sanyashi yayi mata abu, ya ajiye wayoyinsa da makullan sa ya riqo hannunta kamar Karen tankada馃槀saboda rashin Qiba,
'kamar Wannan hannun haka xakayiwa yatsun, koma barshi bana so ka bata hannunka da Ja xan barshi haka,
'no Nainah Kibari xn maki karki damu, ya soma Samata kamar gaske Ya iya, bata ankara da abinda yake ba sai da ta juyo taga Duk ya game yatsun da Tafin hannun Ya shafesu da Lalle hr bayan hannun kamar dungu (lallen tsohuwa馃槀),ta xare idanu sosai hade da sakin yar qara ta fisge hannun tana kallonsa a fusace, shima kallon ta yake da mamaki baisan dalilinta na Wannan Ihu ba hade da fisge hannunta.....

NAINAHTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon