🐍🐍D'AN ADAM🐍🐍-1

1K 45 2
                                    


    🐍🐍 *D'AN ADAM* 🐍🐍

Written by:Sa'adatu Ahmad
Wattpad:mssfana
Facebook: Sa'adatu Ahmad Yandoma
Dedicated to my beloved sis *Hadiza Ahmed Yandoma*

1

Tun da muka iso tashar motar ingawa nake jin 'yan union suna kiran Katsina katsina mutum daya,ba tare da wani dogon tunani ba kawai muka isa wurinshi yace hajiya ina kukayi?nace mishi katsina, tun daga nan ya tsaya yana kallona daga sama har kasa,sai a sannan ya lura da wani ruwa da ke bin kafafuna yace wannan ruwan da ke binki fa?yace gaskia ban ma tunanin zaku daidaita da mutanen da ke cikin motar balle har aje ga direba,nan da nan ta fara hawaye tana cewa don Allah ka taimaka mana wallahi lalura ce ta kama ni,kasan kuma *dan adam* baya wuce kaddarar shi,tunda suka fara magana idanun mutanen da ke wurin ya yo caa akansu kowa da abinda yake fada,sai wata dattijuwa da baza ta wuce shekara hamsin ba ta leko tana kallon yadda wannan dan union yake ta ci ma baiwar Allah mutunci jamaa suna kallo,tace babu komai ni zan zauna kusa da ita sai mu tafi,yace haba hajia kina ganin fa tana matsala ta yaya zaayi a tafi da uta?tace wannan ba damuwarka bane ai ni nace naji zan iya ko? wani dan union da ke gefe ya kalli dan uwanshi yace kai Sale ka rabu da ita ai wanda yace zai iya hadiya gatari sai a sakar masa bota ko?yace hakane kuma garbati,ya kalli yarinyar nan yace to ke samu ledar da zaki zauna akai sai ki shiga,tana goge hawaye taja kanwarta suka karasa wurin motar ,yace ita wannan yarinyar da kuke tare sai ta zauna boot din mota tare da kayanku,tace to ba matsala nawa ne kudin?yace dari hudu ne,sai da ta zauna ta rungume yaron hannunta sannan ta warware gefen zaninta ta ciro dari biyar ta bashi ya bata cikon naira dari. Suna shiga motar da juya tana ma yi ma wannan matar godiya tace hajia na gode na gode Allah ya saka da alkhairi,tayi murmushi tace ba komai ai aikinmu ba na kyamar mutane bane.Daga nan gefen direba ya zagaya yana kiranshi ya bashi kudin mota sannan yace mota ta cika sai a sallame mu,direba ya amshi kudi ya kirga sannan suka ya shiga ya tada mota suka kama hanya.
Tunda suka shiga motar bakajin maganar kowa a cikin motar,kowa da abinda yake tunani,ina daga boot ina kallon yadda yayata ke hawaye tana goge fuskar ta cikin dabara,na leqo ta kaina nace yaya ki bar kuka don Allah,nan da nan nima idanuna suka fara kawo ruwa,ta juyo da kanta a hankali tana kallona tace to na bari kema karki fara sarkin kuka. Nayi murmushi nace yauwa ko kefa yaya. Hajia tace baiwar Allah zan maku shisshigi ina tambayeki idan babu matsala don Allah. Tace to ina jinki Allah yasa na sani,tace yauwa naga kamar baki san garin da kikace a kaiku ba ko?tace Hmm ,hajia tace idan kina ganin kamar da wata manufa nake tambayarki ki barshi,ni da zuciya daya nayi niyyar taimaka maku. Tace wallahi hajia ba haka bane,kiyi hakuri don Allah,wallahi lalura ce ta sanya muka baro gida ba tare da munsan inda zamuje ba. Hajia tace to idan kina ganin babu damuwa da mun isa cikin garin katsina,muka isa ku samu abin hawan da zai kaiku assibitin babbar ruga,in shaa Allahu a can zaa magance miki matsalar da ke damunki,tun lokacin da ni da yaya muke ta zabga godia ga wannan hajia da ta taimakemu,tun daga lokacin naji son wannan baiwar Allah ya shigeni sosai,tayi murmushi tace babu komai ai ni sunana Hadiza Ahmad,ke fa?tace sunana Bilkisu sai kanwata kuma sunanta Aisha muna kiranta *WARDAH* ta juyo ta kalleni tace ma shaa Allahu nayi mata murmushi kawai.Tun daga lokacin babu wanda ya sake magana har muka isa cikin garin katsina. Tafiyar da ta dauke mu kusan awa biyu daga ingawa zuwa katsina.
Muna isa tashar katsina mukayi bankwana da hajia muka samu adaidaita sahu da zai kaimu assibitin muka tsadance dashi akan dari biyu.
Muna isa daidai bakin assibitin mai adaidaitan ya tsaya tare da juyowa ya kallemu yace mun iso,nace mishi toh muka fito wardah kalleshi tace kayi hakuri yayata ta bata maka wurin zama bata da lafia ne. Sai a lokacin hankalinshi ya kai wurin ya kallesu cikin tausayawa yace bakomai kinji Allah ya bata lafia,suka amsa da amin suka biya shi ya kara gaba.

*NATIONAL OBSTETRIC FISTULA CENTRE* assibiti ne da ke jihar katsina a wani kauye da ake kira da babbar ruga. Assibiti ne na kula da duk wasu masu lalurar fata da kuma masu lalurar fitsari da ake ce ma *vesico vaginal Fistula*. suna zuwa bakin assibitin suka samu wasu mutane zaune a waje suka nufesu tare da yi musu sallama. Wani daga cikinsu mai sanye da uniform da gani shine mai gadin wurin ne ya amsa musu,tace don Allah tambaya muke ko nan ne assibitin babbar ruga?mai gadin yace eh nan ne gaskia amma lokacin ziyara daga karfe biyu ne zuwa karfe biyar ku kuma sai yanzu zaku jawo jiki ku taho. Tace aa bawan Allah likita nazo gani ai,sai lokacin yace au to ai nasan halin mutanenmu na kauye ne ba tare da sun ce komi ba ta kama hannun kanwarta suka nufi hanyar shiga ciki. Suna fara tafiya suka jiyo shi yana cewa yana cewa to kuma wannan ko daga ina suke,dubi don Allah yadda fitsari ke bin kafarta,ni na rasa irin wannan hali na kauyawa ace wai a rinka yi ma yara auren wuri hat wannan lalurar ta kamata,daya daga cikinsu yayi dariya yace halan an ga mai kudin kauye ne aka like mashi shiyasa,ya tsaya yana kallonsu sannan ya mike yana kwaikwayon yadda take tafia saboda robar da aka saka mata,dukkansu wurin suka sa dariya,bansan lokacin da zuciya ta zo min wuya ba na juya da niyyar in musu rashin mutunci amma yaya ta hana ni ta hanyar kama hannuna tace kayya 'yar uwa kin mance halin *dan adam* ne? Ko kin manta dalilin da yasa muka baro gida ne?ki rabu dasu duk wanda yayi da kyau zaiyi da kyau. Da haka ta saketa suka idasa shiga cikin assibitin.

Hey readers, am back with my new novel hope am welcome and you'll all like it.😊
your corrections are welcome all the time
Don't forget to like or vote nd comment please
Your likes and comments gves me the strength to write more chapters for you

Fana Miss💕

🐍🐍DAN ADAM🐍🐍Where stories live. Discover now