BARKIN'DO part 48-49

1.5K 89 0
                                    

[ 3/10/2018 ]

🌷 *BARKIN'DO*🌷

*[ very interesting story ]*

*Story & Writing - By AUFANA*✍

✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®📚
      *[ onward together ]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HERT TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

    *Page 48~49*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

    Ciwon Mai martaba yad'aga hankalin kowa saboda tinda yake baita'ba irin wannan ciwon ba,,cikin gaggawa suka wuce dashi babbar asibiti Mai zaman kanta wato [ private hospital ] nan take likitoci suka Kar'besa domin bashi taimakon gaggawa saboda ganin irin mawuyacin halinda yake ciki, ta hanyar amfani da gwajin jinindake zuba ta hancinsa da bakinsa suka gano abunda ke damunsa saidai basu sanarda kowa ba,,'yan gwaje gwaje suka masa suka tabbatar ba wata matsala sannan suka fito dashi d'akin hutu nan suka masa k'arin jini saboda jinin da ya zubda tareda masa injections nantake bacci ya d'aukesa,, saikusan 3:00am sannan yafarka nan su humair sukaje suka kira doctors, y'an gwaje gwaje suka masa suka tabbatarda babu wata matsala ganin jininda suka saka masa ya k'are ne yasa suka sake saka masa k'arin drip domin yak'ara jin k'arfin jikinsa,'...

Cikin ikon Allah kuwa Mai martaba yana farkawa yaji yafara samun lafiya nan take humair yakira waya a gida yashaida masu saboda kowa hankalinsa yakwanta musamman gimbiya Laila da takasa zama sai kuka take da salati ta d'auka ko mutuwa zaiyi sab'anin Ummi wacca taduk'ufa tana kaiwa Allah kukanta,sunji dad'i sosai da wannan albishir da humair yamasu sosai,,,...

Tinda aka kira akace mai martaba yatashi kuma yaji sauk'i sosai hunayya tashiga kitchen domin yiwa mai martaba tsadadden girki nagani kuma nafad'a tinkan tafara saida ta tambayi su meesha abunda yafiso kuma yafi sha'awar yaci saida suka gama mata dariya sannan suka fad'amata aikau batai sanyi ba ta zage dantse tamasa tsadadde kuma shahararren girki wanda su kansu su meesha saida suka jinjina mata saboda irin namijin k'ok'arin da tayi, araund 12:00am humair yazo yad'aukesu yakaisu suka gaisheda Mai martaba da jiki tin a gabansu meerah tazubawa Mai martaba girkin yaci yacisa sosai kuma yaji dad'insa sosai dansai zuba santi yake acewarsa tagwayensa ne suka girka masa, hmm baisan sirikarsa ta b'oye bace ta girka masa hhhh Lol, '....

Tinda hunayya taga yanda Mai martaba yaci girkin har yana yabasa yasa tak'ara zage dantse wajen cigaba da girkamasa wasu kalolin girkin,batareda yasan asalin mai girka masa tsadadden girki ba yake kwasar gararsa san ransa yanzu ma sau biyu takeyi datadawo daga school take shiga kitchen tad'ora na rana da ta saukesa kuma tad'ora na dare, haka hunayya tadinga yi batareda ta nuna gajiyawarta ba,,ahalin yanzu zan iya cewa hunayya takoma mai girkin Mai martaba dandai bayacin kowanne girki sai nata kasancewar su meesha ke kai yasa har yanzu yake d'auka a su ke girka masa,,,...

              **********

   *AUSTRALIA*

A b'angarensu BARKIN'DO kuwa zan iya cewa a yanzu komai yataru yamasa yawa idan yafita tin 7:00am baya dawowa sai 6:00pm hakan kuwa yabama marwa damar yin iyashegenta san ranta daya fita itama take fita abunta sai lokacinda zai dawo take dawowa, abubawa Sun taru sunmasa yawa ga wata matsananciyar buk'ata dayake fama da'ita marwa kuwa ko lokacinsa batada balle yad'ebe kishirwarsa akanta, hakan ne yasa yake matuk'ar kewar abar k'aunarsa wacca bata gajiyawa da buk'atarsa adik lokacinda yazo mata dikda k'arancin shekarunta amma tafi marwa dake da yawan shekaru tinani dakuma hak'uri da juriya, dik lokacinda yatinkari marwa da neman biyan buk'atarsa nantake zata fara mitar ita tagaji bazata iya da jarabarsa ba,,wannan matsalar ce tajanyomasa matsananciyar damuwa wacca tasa yakamu da matsanancin ciwon Mara saboda yawan tara sha'awa dayake batareda yabiya buk'atarsa ba,'....

Yauma dai kamar kullum zaune yake akan kujera yana aiki da laptop d'insa marwa kuma tana d'aki,,kwance take sai juyi take tana kwallah saboda wani azababben ciwon kai da amai Datakeji tayi aman yafi a k'irga yanzuma fitowarta kenan daga toilet, abun yafara damunta tarasa meke damunta ga wani azababben zazzab'i datakeji yana tasomata,tanacikin tinanin neman mafita saiga wani sabon amai yasake zuwarmata da sauri tamik'e tsaye zuwa toilet hakan kuma yai daidai da shigowar BARKIN'DO,nan taita kwara amai kaman ranta zai fita,,dikda haushinta dayakeji amma yad'an tausaya mata bayan tagama yace ta shirya suje hospital,batai musu ba tinda itace ba lafiya nan tashirya cikin wata fita mara kyan gani riga ce matsattsiya kad'an tawuce guiwarta sai wani munafukin mayafi wanda dashi gwanda babu,wani kallo yamata ya watsar sannan yace "ke wai ina zakije haka gwanda ma kiyi gaggawar sauya wad'annan Kayan dan wallahi ba inda zanje dake a haka"  yana fad'ar haka yajuya yafita abunsa dole badan tasoba tacire ta tasaka jallabiyya bak'a Itama dakyar taganta dan dik acikin kayanta itace wacca bata matseta ba,'...

Bayan tasaka tafito tacimmasa a mota sannan sukawuce,wata private hospital sukaje nan aka turasu gun wata doctor ta mata,y'an gwaje gwaje tamata a gwajin farko ta tabbatarwa da BARKIN'DO cewa marwa nad'auke da juna biyu na tsawon wata uku,,dikda k'iyayya da rashin sonda yakeyiwa marwa amma hakan baihanasa yin murna da samun jininsa ba saidai kuma yai bak'incikin fitowar jinin ta b'angarenta,alluran bacci suka mata sannan sukamata k'arin drip saboda amanda tai,,,....

Bayan angama komai sai yawuce gida kasancrwar tai bacci,baijima aosai da fita ba aka kawo result marwa na farkawa taga result d'in nantake hankalinta yamugun tashi jikinta har b'ari yake wajen karanta result d'in  "ciki wata uku nashiga uku ni marwa wallahi dole inyi gaggawar d'aukan mataki tinkan wannan cikin yafara bayyana"  wayarta ta d'akko tai dialing wata number ringing d'aya tai a nabiyu aka d'aga batajira ace komai ba tafara magana "meelat nashiga uku wai ciki ne dani dan Allah kizo ki taimakaman musan abun yi tin kan cikin nan yabayyana"  banji abunda aka fad'aba daga d'ayan b'angaren sai tace "shikenan yanzu ina a *JAWAHIR Private Hospital* ina jiranki please kiyi sauri kizo"  tana gama fad'ar haka takashe wayar sannan ta tashi tsaye tafara zarya a d'akin sai kai kawo take a tsakiyar d'akin zuwa k'ofar fita,'....

          ******   ******

A b'angaren hunayya kuwa abun Alhamdulillah sai godiyar ubangiji karatunta sai cigaba yake ga kwazo ga k'ok'ari ga tsananin basira wacca tasaka kowa na makarantar yasanta musamman principal nasu dakuma teachers nasu saidai fa dikda hakan hunayya bata saki jiki dasu ba saboda tasan matsayinta na matana aure wanda bawanda yasan da hakan sai mutum d'aya itace sabuwar k'awarta wacca tai anan school d'in Mai suna NASREEN, saboda kyawawan d'abiunta da basirarta yasa malamai da dama maza suke kawomata harin  tareda tayin so gakuma uwa uba tsadadden kyanta wanda yanzu yak'ara fitowa saboda samun sauyin rayuwa,,dik acikin teachers nasu maza ba wanda take bama fuska asalima ita bamai yawan magana bace kuma bata yawan fita balle har tai yawo any time tana class tana murajiah da tilawa ita da k'awarta nasreen,'...

Zaune suke alambu ita dasu meesha sai nasreen datakawomata ziyara kasancewar yau weekend ne, cikin farin ciki take yau tsintsa humair yasiyomata dalleliyar waya [phone] sabuwa dall a leda tareda sabon simcard nansu meesha suka sakamata number d'in maigidanta tareda hotunansa saikuma sababbi wad'anda suka d'auka yanzu,,,...

sanyin la'asar yasakko iska sai kad'awa take mai dad'in gaske acikin lambun yayinda suke shan firarsu suna cin y'ay'an itatuwa masu dad'in gaske,, adik lokacinda hunayya ke cikin nishad'i saita tinada Abbanta inama ace yana a raye shima yaji wannan dad'in datake ciki, a b'angare d'aya kuma inta tinada haryanzu fa Mai martaba baisan ita sirikarsa bace matar d'ansa yarimansa hakan yana matuk'ar d'aga mata hankali koya zaiji wane mataki zai d'auka akanta idan yagano gaskiya,, to uwargijiyarta fa wacca ta aurewa miji kuma abun k'aunarta idan ta tina da irin gargad'i da kashedinda tamasu wanda yai sanadi yakumayi silar barin mahaifinta duniya hakan namatuk'ar d'aga mata hankali to idan marwa taji wane mataki zata d'auka kasheta zatayi kome zatamata,, wannan damuwar itace ke faman d'agawa hunayya hankali ba kad'an ba,,Sai dare sannan nasreen tawuce gida sukuma sukafara shirin bacci,'...

Alhamdulillah mai martaba yasamu sauk'i sosai satinsa d'aya aka sallemasa, a sakamakon gwaje gwajenda aka masa ne humair yagano cewar wani poising ne aka sakamasa a abinci yaci,wannan abun yamatuk'ar bama Ummi dasu meesha mamaki to waye ya aikata wannan abun, oho amsar tanagun ubangiji saboda shine baya bacci baya angaje,'...

         ******  *****

*AUSTRALIA......*

Koda BARKIN'DO yadawo saiyaga wayam ba marwa ba alamunta nan yabud'e toilet kotaje yin amai amma nanma shuru......


🏃‍♀🏃‍♀'''Muje zuwa '''

'''AUFANA for life '''🌷🌷
   *I. W. A*🖊

BARKIN'DO Where stories live. Discover now