[ 25/10/2018 ]
🌷 *BARKIN'DO*🌷
*[ very interesting story ]*
*Story & Writing - By AUFANA*✍
✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®📚
*[ ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ ]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious And dropping a kinda lights to readers }*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HERT TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW......*✔🌷 *END*🌷
🌷 *END*🌷
*Page 80*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Around 10:00am jirginsu yad'aga izuwa masarautar JAMNAZ saikusan 12:00pm sannan suka isa, da'isarsu kuwa dalla dallan motocin mai martaba suka d'aukesu izuwa gida,,,...
Koda suka kuwa har meesha da kyawawan yaranta sun iso ihsan da iman meerah kuwa tin jiya ta'iso da yaranta uku hunais hamid saikuma k'anwarsu hanifa nan su MUDASSIR aka had'e anata faman k'iriniya, "...
Masha Allah nafad'a ganin gida yacika da jikoki gwanin birgewa, BARKIN'DO yasaka ancaccanzawa masarautar tsari izuwa nazamani sannan yaginamasu k'aton gida wanda yazu acan suke suntashi acikin gidan sarauta,,,...
Aranar suna ne su hunayya kejin labarin fainus da mahaifiyarta gimbiya laila dai anrasa k'afa wani ciwone yakamata wanda yakaiga saida aka yanke k'afar fainus kuma batada lafiya itama ciwo ne yakamata yanzu har wasu ruwa ke fita a gabanta masu warin gaske kowa baya iya zuwa gunta abincima ta window ake jefamata gawasu k'uraje dasuka fitomata ajiki,, hmm dama dikwanda yace tukunyar wani bazata tafasa ba tikuwa tashi ko zafi bazataiba Allah dai yak'ara shiryardamu ameen, "....
Bayan angama shan shagalin biki ne mai martaba yace kamin suwuce su shirya zasuje masarautar DUMNAH domin nad'a sabon sarkin wannan yanki,, nan suka shirya suduka suka wuce, kwanansu biyu da zuwa aka nad'a sabon sarki mijin Aunty salma sarkin gida na masarautar JAMNAZ shine mai martaba yanad'a saboda halinsa na kirki dayagani, bayan angama ne hunayya tawuce rugar su saida sukai kwana biyu sannan suka dawo inna da Abba nata kewar su MUZAMMIL,,,....
Aranarda zasu wuce ne hunayya tace tanasan tafita tad'an zaga gari nankwa aka shiryawa su MUDASSIR da k'anwarsu hauwa'u jiddah wacca suke kira da mimi saboda sunan ummin BARKIN'DO ne, bayan sun shirya suka fito harsun fara tafiya saiga BARKIN'DO nanshima yace aje dashi,"...
Sunacikin zaga gari sai suka isa wata 'yar k'aramar kasuwa gun masu bara almajirai mata da maza, tausayi hunayya taji yakamata saita bud'e jakarta tak'arasa gunsu tafara raba masu kud'i, tanacikin rabawa ne takaiga wata taciro kud'i tabata zata wuce saitaji anrik'e hannunta nantajuyo domin ganin ko waye,, kallonta matar keyi hunayya takasa ganeta saikuma taga kwallah na zuba a idon matar tsayawa tai tana kallonta sannan tace "baiwar Allah lafiya" shuru matar tai sannan tace "B'ingel kece gimbiya sailuba ce" a tsorace kuma cikin mamaki hunayya takalleta sannan tace "ammi kece kika dawo haka ina marwa take dabazata taimaka maki ba" kwallah ke zuba a idanun gimbiya sailuba "hmm B'ingel ai marwa yanzu sai addu'ah" sai addu'ah kuma anmi banganeba, "B'ingel dikyanda zanmaki bayani bazaki tab'a fahimtar irin halinda marwa take cikiba sai idan kinganewa idanunki" shikenan bara nak'arasa rabama sauran saimuje kikaini gunta. Nan tak'arasa bama sauran sannan tajuya taje gunsu BARKIN'DO ta rok'eshi dan Allah yabarta taje saidatai kamar tanayi dakyar ya'amince sukaje,,,...
Koda sukaje kuwa wani kangon gida ne suke aciki saboda tin lokacinda mai martaba yarokesu suka rasa inda zasuje gashi mijinta shima yasaketa saboda mugun halinta itakuma marwa duniya ta juya mata baya, acikin wani d'aki suka shiga mai kama da akurkin kaji dan su MUDASSIR ma tsoro suka kamaji, can suka hangonta kasa k'arasawa sukai saboda wani mugun bala'in wari gawasu ruwa masu mugun d'oyi nafita a gabanta. Tana ganinsu tabuga ihu tana b'oye b'oye a bangon d'akin sailuba ta kalli hunayya tace "B'ingel ki yafewa marwa saboda wallahi idan bakuyafe mata ba tanacikin masifa kiyafe mata kotasamu sauk'in halinda take ciki kinga taji da sauran, nima dan Allah ki yafeman" kwallah ne suka zuba daga idon hunayya saboda tsananin tausayi "ammi nayafe maki kuma itama wallahi nayafe mata Allah ya yafemana baki d'ai kuma Allah yabata lafiya insha Allah zanyi iya k'ok'ari naga na taimaka mata a asibitinmu nasan bazasu k'asa ganin bayan wannan lalurar tata ba" saboda farincikin abunda tafad'a har saida sailuba ta risina mata har k'asa tana godiya, dazasu tafi kuma kud'i masu tsoka hunayya tabama sailuba tace suyi amfani dasu kamin tadawo,, Allah sarki kaga mai rama sharri da alkhairi baiwar Allah, "...
Suna komawa gida kuwa hunayya tashiga yak'i da mai martaba da BARKIN'DO cikin ikon Allah kuwa taci nasara nan tasaka aka d'auko marwa da sailuba aranar suka hau jirgi izuwa Australia, saida suka kwashi tsawon wata 7 anakula da marwa sannan aka samu tad'anji sauk'i ammafa har yanzu ruwannan masu d'oyi basu daina fita agabanta ba kuma batadaina kuwace kuwace ba norses kuwa data ishesu da kuwace kuwace saisumata injection na bacci,,,....
Haka rayuwa tacigaba da tafiya ranar wata saturday ne marwa rai yayi halinsa hmm zokuga ikon Allah saboda marwa tai muguwar tafiya akai akai k'asa tak'i karb'anta saida aka k'one gawar sailuba kuwa sai kuka take hakama hunayya tai kuka saboda tausayi, "....
Kwance yake akan gado shigowarsa kenan saiyaga baigantaba danhaka yazauna yana jiran fitowarta kasancewar yaji motsinta a toilet, tajima sosai tana wanka sannan tafito tana tafiya dakyar saboda k'aton cikinda take d'aukedashi, kallonta yai sannan yai murmushi "uwar biyu k'ila yanzuma wasu biyun ne" hararansa tai daidai lokacinda take zama kan gadon, mai tajanyo dakyar sannan tashafa tasaka riganta ta bacci takashe masu fitilar d'akin sannan tahau gadon takwanta, akan k'irjinsa tad'ora kanta shikuma gogan yacusa hannunsa acikin rigarta yana wasa da dukiyar fulaninta tariga da tasaba da halinsa shiyasa yanzu baya damunta ahaka kar sukai bacci,,,....
Cikin dare nak'uda ta tada hunayya ba shiri yad'auketa yasaka mota sannan yak'ira wata makwabciyarsu yace dan Allah tazauna tareda yaran kada su farka bakowa,, dazuwansu aka karb'eta izuwa labour room cikin ikon Allah tasantalo kyakkawan baby boy d'inta mai kama da mai martaba aikwa nan BARKIN'DO yaita murna, saida aka tabbatar bawata matsala sannan suka sallamesu, kwana d'aya da haihuwa suka dawo JAMNAZ aranar suna yaro yaci sunan mai martaba ABDULK'ADIR sukamasa inkiya da Abul khair,,,...
Haka rayuwa tacigaba da gudana cikin so dakuma k'aunar juna kodayaushe BARKIN'DO yana tareda iyalinsa abun alfaharinsa hakama mai martaba da yara sunyi hutu yake cewa akawomasa su ummi kuwa yanzu ba abunda take sai godiya ga ubangiji saboda shine abun godiya.... Tabbas maganarki dutse ummi.
*TAAMMAT BIHAMDILLAH*
*to jama'ah kunga dai yanda k'arshen marwa yazo inafatar masu aikata bak'ar d'abi'ah irin tata yaji tsoron ubangiji yadaina kodon tsoron k'arshensa dakuma makomarsa saboda wannan bak'ar d'abi'ah ce mugun kasuwanci ne wanda ba'acin riba saidai fad'uwa Allah yak'ara shiryardamu dakuma zuriarmu baki d'ai ameeen**ANAN KUMA NAKAWO K'ARSHEN WANNAN LITTAFEN NAWA INA ROK'ON ALLAH YA YAFEMAN KURA KURANDA NAI ACIKINSA YAKUMA SHAFESHI AZUKATAN DIK WA'DANDA SUKA KARANTASHI AMEEEN*
*SAIKUMA MUNHA'DU ASABON LITTAFENA MAI ZUWA INSHA ALLAH AMMA A WHATTPAD*😝😎
*MA'ASSALAM*
'''AUFANA for life '''🌷🌷
