chapter twenty four

623 46 0
                                    

What!!?” Innalillahi wa inna-ilaihirrajiun!! Wane asibitin?? Ok I’ll be on my way” Abunda General ya iya cewa kenan da Mujaheed ya sanar da shi abunda ake ciki a waya, Hankalin kowa ya tashi saboda haka Inna ma tace bata ga ta zama ba,tare suka nufi asibitin da Dad d’in Imtihaal mutumin da ba’a ma sanar da shi halin da y’ar shi ta shiga ba….

       “Doctor pls do your best to save him!! Pls I beg of you!  Plssss!!” Cikin rudani da tashin hankali Sadiq yake maganar, Dr ya sa aka dakatar  dashi daidai kofar emergency room. “You have to stay here sir ,wait outside pls” Abunda d’aya daga cikin nurses d’in ya fad’a kenan yayinda suka k’arasa tura Rasheed dake Kwance rai a hannun Allah a kan stretcher…….

        Inna ta kasa zama sai kai kawo suke daga ita har Sadiq. Abbah ya k’araso kusa da Sadiq gami da dafa kafad’ar shi yace ” Be a man my son in shaa Allah He’ll be alright I know he’ll fight through it instead of being worried why not pray for his wellbeing! Nasan yadda kake ji a ranka yanzu coz baka da wani wanda ya wuce Rasheed but I want you to be strong my son”
      Sadiq ya sake fashewa da kuka, cikin kuka yace “Abbah in da nasan haka zai faru bazan tilastawa Rasheed sai Mun fita ba a wannan lokacin, kuma sannan da bamu je wajen ba da motar su kawai zasu shiga su koma gida, amma saboda sun ga Rasheed a tsaye ne suka taho, and now my friend is hospitalized because of me and his fiancé Imtihaal is being kidnapped !! Dum!!!! Kirjin Inna ya buga ta juyo cikin rudani tace ” Imtihaal!! Ta rik’e hannun Sadiq iya  k’arfin ta ” Yaya akayi haka ? Ina aka kaita? Su waye suka d’auke ta?? Ka sanar da ni mana Sadiq ba magana nake maka bane ??!!” Tana magana tana jijjiga shi. Da kyar ya bud’e baki yace “Inna nima ban sani ba, hankali na baya tare da ni ,am very confused! Bansan ta ina zan fara ba ya sulale ya zauna kan wani waiting chair yayinda Major Ali (Dad d’in Imtihaal) tuni ya riga ya saddaqar, suna cikin wannan yanayin likita ya fito daga emergency room, da sauri suka ruga domin suji lafiyar Rasheed.

       Doctor !!yaya jikin nashi ? How is he?!! I hope he’s alright ? Likitan yayi murmushi gami da dafa kafad’ar Sadiq yace ” yes !! D’an uwanka yana nan lafiya ,he just suffer some cases of suffocation ,kasan hayak’i ne yayi masa yawa hakan ya sa duk wani air pass way nashi suka kusa daina function ,its good kun kawoshi Twenty minutes earlier da ina tabbatar muku da cewa we couldn’t have save him ,kuma ku godewa Allah (S.W.T) Domin shine me yin yanda yaso kuma a lokacin da yaga dama, ya kaddara cewa d’anku yana da sauran kwana a nan gaba. In kun gama ina son ganin mahaifin patient din a office nawa pls akwai wasu papers da zai yi signing a kai da kuma wani muhimmiyar magana da zamuyi……..

    

         Sadiq ya d’an nisa sannan yace ” doctor, zamu iya ganawa da patient d’in kuwa?” Likitan ya juyo da murmushin shi yace ” No my son! Yanzu bazai yiwu ba har sai Mun yi transferring patient din zuwa VIP room tukunna sai ku duba shi but for now yana buk’atar Hutu saboda, ka ‘kara hak’uri……

          K’arfe takwas na dare Inna tana zaune kan kujera as a gefen gadon Rasheed tayi jigum ta k’ura masa ido Sadiq ya jingina da bango ya nad’e hannuwan shi a kirji idonshi a kan Rasheed baka jin k’arar komai a d’akin sai na na’urar da take aiki. Bud’e kofar da likita yayi ne ya dawo da su daga tunanin da suka shiga duk suka maida duban su ga likitan.
      ” Har yanzu soja bai tashi bane? Inna ta d’an yi murmushin dole tace Eh bai tashi ba. Likita ya gama dube duben da zai yi sannan yace” zai iya farkawa a ko wanne lokaci daga yanzu you need to stay closer to him because zai iya tashi cikin ko wanne yanayi depending on abunda ya faru da shi, don’t worry we’ll also stay alert:)
    Inna kai kawai ta girgiza ba tare da ta tanka ba……

                                                        

       Gudu motar take yi kamar zasu tashi  sama tun da Imtihaal ta hango yadda motar Rasheed ke cin wuta yayin da yake bin bayansu ta saddaqar babu wani mai cetonta sai mahaliccin ta saboda haka ta yanke shawarar amfani da k’arfin da Allah yay mata, mutanen da suka sa ta a tsakiya sukayi mata alluran bacci ganin tana neman zubar da su gaba d’aya da motar a take ta sulale ta zube k’asa sannan suka samu natsuwa suka nufi hanyar zuwa Lagos..,……..

        A hankali yake motsa hannun shi ,idanuwan shi suna bud’ewa kafin su ankara yayi wuf ya mik’e yana faman fizge cannular dake hannun shi Sadiq yayi kokarin rik’e shi ya fizge kamar mahaukaci da kyar ya iya furta sunan Imtihaal. Sun ga hauka iya hauka kam a wannan daren don saida akai mishi alluran bacci tukunna hankalin kowa ya kwanta ,shi dai buk’atar shi ya fita neman masoyiyarshi bai kuma damu da halin da yake ciki ba…….


CAPTAIN RASHEEDOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz