BARRISTER ALEEYAH part 36-40

1K 52 0
                                    

🌷🌷🌷B͓̽A͓̽R͓̽R͓̽I͓̽S͓̽T͓̽£R͓̽ A͓̽L͓̽££Y͓̽A͓̽H͓̽ 🌷🌷🌷

*Story & Writing - by AUFANA*✍

*Dedicated  to -* '''My sweet mother Nana Asma'u Abbakar mahaifiyata abar alfaharina akodayaushe kuma a kowanne lokaci ina alfahari dake ubangiji ya saka maki da mafificin alkhairi yasa al'jannar Firdausi ce makomar ki ameeen'''

    *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*📚®
                   *{ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ}*

  *℘ąɠɛ 36-40*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Karatu suke sosai bawasa saboda wannan itace exam ta k'arshe dan haka babu wasa

Saidai karatunda take zuwa wato islamiyya ya tsaya saboda karutun exam

                       **********   *********

K'wanci tashi ba wuya awurin ubangiji yau saura kwana biyu su *Aleeyah* sufara exam

Zaune suke suna cin abinci saishan fira suke akan exam dinda zasu fara jawahir ce ta kalli *Aleeyah* bestie lfy dai naganki so silent

Murmushi tai bestie banajin dadi ne wlh

"Meke damunki ne "

Marana ke ciwo tin jiya da dare nake jinsa nadauka zai daina shiyasa amma gashi har yanzu baidaina

"To aikwa bamuga ta zama ba muje ki karbo magani saikisha kinga exam muke fuskanta dan haka yakamta muzama ready

" OK bara mukammala cin abinci saimuje "

Bayan sun kammala suka wuce ta karba tasha sannan suka dawo hostel

Alhmdllh su jawahir anfara exam cikin sa'a saidai fa sunashan wuya cox karatun kasar waje ba dai yake dana nan gida ba saboda haka yasa suke zage dantse domin fito da result mai kyau

Yau ma dai sai 4:15pm suka fito saboda haka agajiye suke suna cin abinci kowa yanemi wajen hutuwa a k'wancenda suke ne sukeshan fira *Aleeyah* kece bestie wlh tinanin ranar rabuwarmu nake dake na saba tin muna yara har izuwa yanzu damuka mallaki hankalin kanmu

Fatana Allah yakara hadamu wani lokaci kuma yahadamu a aljannar firdausil a'ala ameen suka karba

"Wlh nima kawata ina wannan tinanin haka Allah yake lamarinsa gashi muba yan'uwa ba amma Allah yahadamu zama kuma harmuka zama kawaye tamkar yan'uwa "

Nan dai sukaita jimamin ranar rabuwarsu har bacci yadaukesu

Yau kimanin 3weeks da fara exam dinsu *Aleeyah* dik ta fada ta rame ga karatu ga tinani

Yaudai basu exam danhaka jawahir tace su shirya su fita mika kafa daganan suje su gaida yayansu Aryan *Aleeyah* taji sosai koba komai zata dan rage yawan tinani da damuwa

Sun shirya tsab cikin shiga maikyau jallabiyya ce baka da Rollin din mayafi red colour sunyi kyau matuka dikda ramar da *Aleeyah* tai amma hakan baihana bayyanar kyanta a fili ba

Aryan yay murnar ganin k'annensa cikin shiga mai kyau hakan yamatukar burgeshi hakan yasa shima ya shirya yaje dasu yawon shakatawa awurare daban -daban na hutawa aik'wa sunci sunsha harda tsaraba daga nan yawuce yakaisu school sannan shima yawuce

                      ************     *************

Alhmdllh gobe takasance ranar farinciki agun su *Aleeyah* saboda gobe ne zasu zana jarrabawa ta karshe ta kammala secndry ss3 kenan saboda haka yau cikin farinciki suke sosai ko bacci sunkasayi sai shan fira suke suna tina baya wato lokacinda sukazo suna yara idan sun tina wannan su tina wancan susha dariya

Saidai fa a dayan bangaren basa farinciki idan suka tina fa rabuwa zasuyi kuma basusan ranar da zasu sake haduwa ba cox duk ba'a kusa suke ba *Aleeyah* na abuja jawahir na kebbi inda hanifa kuma take a yola bafulatana ce

Kowannensu yasan kasar da dan'uwansa yake amma basusan ainihin inda yake da zama ba

Kimanin 12:30pm suka fito daga exam school din dik ta hargitse koina sai celebrating ake su jawahir nacan zaune suna kallo dik sanye suke da uniforms saidai su sunsaka abaya a sama

Wasanni ake kala - kala gwanin birgewa gwanin ban sha'awa nan school din tasaka ranarda zata masu biki ai kwa sai murna suke

Ranar Monday itace ranar da aka saka domin yin shagalin bikin kammala secondry nasu *Aleeyah*

Yau takasance Thursday tin 10:20am Aryan yazo ya dauki su jawahir sukaje kasuwa sukayo siyayyar kaya wasu hadaddun abayoyi da jallabiyu hade da takalma saikuma kayan cosmetics ne yasaya masu wadanda zasu saka ranar bikin

Hukumar makarnta ta shaidawa kowanne uba daya kawo dansa cewar ranar Monday zatayi bikin yaye dalibai

Aryan yakira gida ya shaida masu komai sun tsara yanda yakamata tindaga masaukinsu har komai ma

Dadyn *Aleeyah* ma yakirata ya shaidamata suna nan zuwa nan ta nunamsu farincikinta da irin missing basu da tai amma saidai azahiri tsoro da fargaba ne fall afuskarta nan yake shaida mata tarin kyaututtukan da zai mata idan har tazama best student amakarantar ta nunamasa farincikinta sosai daga bisani suka rabu ta kashe wayar

Juyowa tai tadubi jawahir fuskarta ba walwala yar'uwata dady na da momy na zasuzo bansan ya zanyiba inatsoro wlh

"Kafadarta da dafa yar'uwarta ki cire tsoro ko fargaba azuciyarki karfa ki manta Allah yana tare da mai gaskiya "

Murmushi tai tace hakane yar'uwa ta

Nan suka wuce hostel dinsu hanifa cox yanzu ba karatu sai fira dakuma shirye - shiryen biki .........................



🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀'''Kubiyoni'''

     '''AUFANA for life'''🌷🌷🌷
               *I.W.A*🖊

BARRISTER ALEEYAH Where stories live. Discover now