🌷🌷🌷 *BARRIST£R AL££YAH*🌷🌷🌷
*Story & Writing -by AUFANA* ✍
*Dedicated to -* '''my lovely and my sweet Mother Nana Asma'u Abubakar'''
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*📚®
*{ơŋщąγɖ ɬơɠąɬɧɛγ}**Am back my fan's ina maibaku hak'urin jina dakukayi shuru masu kirana a waya damasu nuna damuarsu dik inamai baku hak'uri wlh commitment ne sukayi yawa shiyasa amma insha Allah zakucigaba da ganin posting very soon amma yanzu kan kuman uzuri alk'awarin danai yasa yanzu ma nai tyaiping kucigaba da hak'uri Aleeyah ma tai missin naku kamar yanda kukai nata Allah yabar k'auna gayanan yaukam kushoshale abunki muje zuwa*
*℘ąɠɛ 61-65**BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Jin sallamar da sukayi yasa suka juya domin ganin mai sallamar,'...
"wata kyakkawar Mace ce fara tas tamkar balarabiya,d'auke take da kyakkawan yaro ahannunta cikin tafiya irinta manyan mata masu ji dakansu takaraso cikin Falon,,'
Gun Abdallah tai wanda yake tik'e da belt ahannunsa *Aleeyah* kuma nadurk'ushe agabansa, wani wawan mari ta sauke masa tareda fizge belt d'in ahannunsa sannan tace "amma wlh Abdallah kabani kunya kuma kabani mamaki wanne irin laifi ne tamaka dahar zaka dinga jibgarta da belt ba'akan Mace yadace ka nuna k'arfi ba idan har zaka iya d'aukar hannu ka daki mace to tabbas zaman aure da Mace saiya gagareka",....
Nan tasake juyowa gun umma tace "haba hjy hafsa wannan wane irin rashin tausayi ne karfa kimanta ke uwa ce zakiji dad'i idan har akace y'arkice akayiwa haka, ak'allah nayi kimanin 5minutes atsaye amma saboda tsabar zalinci dikkaninku ba wanda yaganni,,'
"haba hjy zulaihat kamin kifara fad'a yakamata kifara tambayar abunda ke faruwa, yarinyar nan fa sata taman sark'ana ta gold tad'auke kinga kuwa ai ta cancanci kowanne irin hukunci daga gareni",...
Ganin abunda ke faruwa tsakaninsu yasa masu aikin bakid'ai suka wuce
Shima Abdallah yawuce zuwa 'bangarensa *Aleeyah* kuwa dakyar Ta'iya d'agowa daga durk'ushenda take, kuka take sosai bakinta sai zubarda jini yake ko'ina na jikinta yayi kwanciyar belt, ahankali take tafiya hartashige d'akinta inda umma kebinta da harara har tashige,,...Ganin kowa ya watse yasa umma jan hannun matar suka wuce d'akinta, itadai mamakin sune yacikata hartakasa magana sai binta kawai tai suka shige coli, "
"dashigarta tafad'a kan gado tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro zuciyarta namata k'una zafafan k'wallah ne ke fita daga idanuwanta tarasa meke mata dad'i aduniya, ya Allah kagani kaine shaidata wlh banta'ba aikata sata ba Allah kaine gatana kataimakeni kafitardani daga wannan k'angin wuyar dikda nasan bawai kamanta dani bane " haka dai tadinga maganganu ganin babu sarki sai Allah yasa ta tashi tawuce toilet, ruwan d'imi tahad'a tai wanka tareda gasa jikinta sannan ta d'auro alwala tafuto ,"...
Mai tad'an shafa sannan tasaka doguwar riga bak'a nantad'akko hijab tasaka tafara sallah tana kaiwa ubangiji kukanta, nafilfili tadinga yi harsaida tagaji sannan tatsaya bayan tagama ne takwanta nantadinga zancen zuci "oh ni *Aleeyah* yazanyi tabbas idan nacigaba da zama a gidannan wata rana zasu kasheni gwara kawai nabarmasu gidansu nahuta, wasu k'wallah ne suka zubo mata datatina da irin gatanda ake bata amma yanzu wai itace abar k'yama Allah sarki duniya kenan,"
Gari Yayi duhu sosai lokacin sallar isha danhaka tasami yanda takeso nan tasaka takalmanta tafito taci Sa'a kuwa bakowa falo ahankali tadinga tafiya har tafito waje nanma dai bakowa Masu gadi basanan alamar sunyi wajen sallah aikwa nantasamu tabud'e gate tawuce abunta,
Tafiya take tarasa inazatadosa dikda hasken fitilu amma bakowa ko'ina tsitt abunka da bariki, tafiya kawai take hartabar unguwar tashiga wata unguwa can tahango wani shago nantaje tala'ba kasancewar dare yayi sosai ga gajiya ga wata iriyar yunwa datakeji bata ankara bacci yai awon gaba da ita,"....
Kiran sallar asuba ne yafarkarda ita ta tashi domin sanin abunyi wata gorar ruwa tahango nantaje tad'akko tayi alwala tazo tashimfid'a d'ankwalinta tafara sallah,,,,,
Tana cikin sallah ne wasu maza Su biyar suka zo gabanta sukayi tsaye kowannensu dakaganshi kasan abige yake sai faman gyangyad'i suke ,tana kammala sallah ta mik'e a tsaye tana fad'ar innalillahi Wa'inna ilaihi rajiun....!!! atsorace Kuma a firgice cikin tashin hankali tace "bayin Allah lfy meke faruwa ne ??,,
"wata sabuwar dariya suka dinga yimata kamar sababbin mahaukata, d'aya daga cikinsu yace "woww gsky oga wannan fulawar tayi amma saidai kash batada banruwa", wanda yakira da oga yace aikwa yanzu za'afara mata banruwa yafada'a yana shafa sumarsa nanyakai hannunsa yacirewa *Aleeyah* hijabi, "dasauri taja da baya tana cewa dan Allah kuyi hakuri menamaku karku cutardani narok'eku " ganin basuda alamun k'yaleta yasa tagudu,,,....
Gudu take suna binta tagaji sosai amma dikda haka bata tsaya ba harsukazo bakin titi, saboda gajiya gudunda take ga hak'i Yarufeta sam bata ma ganin gabanta balle tasan inda take gudu aikwa bata ankara ba saiga wata mota agabanta nantai sama do'ita, ganin haka yasa sukuma dasuke biyarta suka koma, kankace me tini mutane sun zagaye *Aleeyah* wacca take a kwance Kamar gawa sai jini kezuba daga kanta dakuma hancinta,,,
Wanda ke acikin motar kuwa agigice yafito ko takalma babu ak'afarsa, fuskarta yafara cinkaro da ita ganin jininta akan titi zube yasa hankalinsa yak'ara tashi cikin sauri yazo kanta yana fad'ar innalillahi WA'inna ilaihi rajiun subhanallah jama'ah dan Allah kutaimakaman nakaita asibiti nankwa aka Kama masa tad'auketa yasakata acikin mota, sit d'indake gaba yakwantar yad'orata akai sannan yarufe marfin shima yazagayo yashiga dasauri yatada motar izuwa asibiti,'......
Tuk'i yake amma time by time dik yajuyo yakalli fuskarta wacca dikda idanuwanta Na arufe tamkar mai bacci amma murmushi takeyi aransa yakecewa "tsarki yak'ara tabbata ga mahalicci wannan kyakkawar halitta hak'ik'a dik zamanda nai ak'asashen waje banta'ba ganin kyakkawa ba kamar wannan tabbas ikon Allah dagirma yake " ahakadai yadinga zancen zuci haryakaraso hospital d'in cikin sauri yayi parking motar sannan yafito wayarsa tad'akko yai dialing wata Nmbr nantake kuwa d'aga magana sukayi cikin k'ank'anen lokaci saiga noses tareda wasu doctors mace da namiji nan yabud'e yad'akkota cikin sauri yake tafiya da'ita tiater room suka wuce kaitsaye cikin k'ank'anen lokaci suka shiga tiater da ita,,'.....
Kimanin 30minute's suka d'auka sannan aka kammala operation d'in alhmdllh komai yazo cikin nasara dikda dai and'an shawuya amma dai anci nasara saidai tarasa jini sosai hakan yasa suka maidata d'akin hutu tareda mata k'arin jini,,....
*************
*U. S*
Aryan yakoma u.s da mamakin *Aleeyah* wai tanasansa Sam yakasa wace amsar zaibata coz shi tinda yake da ita baita'ba jin santa azuciyar shi ba, yau kimanin 3week's da dawowarsa damuwa tashigesa yakasa zama yakasa tsayi dik yarame yayi baki komai nasa nanema yajagule masa kuma yakasa sanarda kowa saboda Sam baiyarda da abunda zuciyarsa ke sak'a masa ba, a dik kwanan duniya idan yakwanta bacci *Aleeyah* ce yake gani amafarkinsa idan yakuma yana a farke to tinaninta ne ketayashi fira akodayaushe ita ke masa gezau yarasa meyaasa haka din,,'Yaumadai kamar kullum kwance yake yana bacci sai yai mafarkin yaga *Aleeyah* cikin shiga mai Kyau d'auke take da kyakkawan yaro ahannunta tana zaune acikin falo tanayiwa yaron wasa sai dariya take shima babyn datakeyiwa wasa dariyar yake ahankali yak'araso a kusa dasu zaimata magana kawai saiya farka daga bacci,,..
Abun yamatuk'ar bashi mamaki, abu kamar wasa amma saicigaba yake Wani saiyadinga tina kuruciyarsu *Aleeyah* da jawahir idan suna rigima lokacinda suna makaranta idan yakai masu ziyara, komai na Aleeyah birgeshi yake yanayin tafiyarta murmushinta tsarinta harma da miskilancinta gakyau ga diri na mata kai komai nata yayi, amma saidai shi haryanzu yakasa yarda cewa fa san *Aleeyah* ne yamasa shigar bazata, ahalin yanzu bashida burin dayawuce yaga kyakkawar fuskar ta kokuma yaji muryarta saidai kashh adik lokacin da yakira umma yace tabawa *Aleeyah* su gaisa sai tacemasa batanan idan kuma yakira Abdallah saiyace masa ta aiketa hakan yasa dole yake hakura saidafa yashiga damuwa yana san yajita kodan yatambayi lafiyarta sai ayanzu yake danasanin rashin kar'bar nombarta,,'..
******** *******
Kimanin 1week kenan dayiwa *Aleeyah* operation amma haryanzu bata farkaba saidai duk wata kula tana samunta saidai fa abun yafara d'agawa likitocin hankali rashin farkawarta da wuri bare Susan wane cigaba akasamu sundai yi iya nasu k'ok'ari yanzukam sunzubawa sarautar Allah ido,,...
"Zaune yake a office d'insa akayi nocking yabada umarnin sannan mai Nocking d'in yashigo..............
🏃♀🏃♀🏃♀'''Muje zuwa'''
'''AUFANA For life''' 🌷🌷🌷
*I. W. A*🖊
