https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY**°•ѕadaυĸarwa ga Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα•°*
*°•ιnтellιgenт wrιтerѕ aѕѕo✍•°*
_____________________________________💥
*Թɑցҽ 1⃣4⃣*
"Hajiyata amma kina ganin....... "
Da sauri Haj.Babba ta tari numfashinsa"A'ah Faruq kul kada naji ka furta komai,mahaifinku ya riga da ya gama magana,yanxu ya rage gareku ne kuyi biyayya tunda har kun riga da kun amince,ya rage gareku ku kara fahimtar juna kafin lokacin biki,ubangiji Allah ya shi muku albarqa da biyayyar da zaku mana bawai don kunso ba,kuma ina mai tabbatar muku da cewar insha Allahu bazaku taba tab'ewa ba don d'a meh biyayya ga iyayensa,Allah kan saka yaga daidai acikin lamuran rayuwarsa,Umar Faruq,Najmiy Allah ya shi muku albarqa,shi kuma Hayatudden Allah yasaka hannu cikin lamarinsa ya karkato da hankalinsa xuwa gida.... "
Gabaki daya suka amsa da "Ameen Ameen Hajiyarmu... " Faruq ya mik'e ya fice zuwa fadar mai martaba don tayashi ƙarban gaisuwa kamar kodayaushe,don tunda akayi rasuwar kullum makale yake da mai martaba,tare suke ƙarbar gaisuwar mazaje,Haj.Babba kuma su karbi na mata,wasu matan ma da biyu suke xuwa kawo gaisuwa don kawai suyi tsegumi,dake kuwa maganar b'atar Hayat ya gama zaga gari,da yawa cewa suke ta dalilinsa mahaifiyarsa tabar duniya.
*WANNAN KENAN*
_______________•°•___________________Bawan Allah Hayat kuwa,duk wani information na gidansu yana samu tare da taimakon abokinsu Ibrahim Spanzy wanda shine ke basu labarin komai awaya.Spanzy ne ya samu mai gadin gidansu mai martaba,dake shi din yaro ne mai wayon tsiya sai da yasan yadda yayi suka saba da tsohon,kusan kullum sai yazo kofar gidan sai su zauna abenci awaje,spanzy sai yayi ta bugar ruwan cikinsa,shi kuwa Mal.Madu mai gadi sai kaga ya shagalta yana kora masa bayanin komai dake faruwa tun daga batar Hayat har xuwa rasuwar mahaifiyarsa,idan Spanzy zai tafi sai kaga yadan zaro naira dari ko dari biyu ya bashi,shi kuma tsohon ya karba yana mai washe baki tare da shi masa albarqa,Mal.Madu bai taba kawo komai aransa agame da zuwan Spanzy wurinsa akodayaushe ba,ya dauki hakan ne kawai akan haduwar jini ne.
Alokacin da rasuwar Haj.Karama ya riski Hayat,ranar sadakar uku ne ma aka gaya masa,har suma sai da yayi,bayan ya farfado kuwa kamar zai haukacewa Roughcoin,cewa yake yana dada nanatawa"wayyo kaicona Hayat na cuci kaina,nayi sanadin barin mahaifiyata duniya,ta tafi da tsananin fushina adalilin biyewa son xuciyata,babu makawa makomata gidan wuta ce... " Ya fashe da wani irin wahalallan kuka mai ban tausayi,Roughcoin kuwa fashewa da dariyar iskancinsu yayi,sai daya dan zuƙi tabarsa kana yace"See diz idiot ooo,u don already judge urself,hahaha thank God da kasan cewa gidan wuta straight zaka shiga.... " Ya sake zuƙar tabarsa ya fesar akan fuskar Hayat,azuciye Hayat ya mik'e ya yankawa Roughcoin mari yace"Mahaifiyata ta rasu shine kake shan taba agabana?atleast she need a sign of respect and a sympathetic face from you,kodayake ita din uwatace ba uwarka ba shiyasa baka damu ba,toh bari kaji ni gida zanyi yanxun nan kuwa. " ya juya ya soma hada kayansa yana kuka yana ambaton "Hajiyata pls ki yafemin wallahi na tuba,ubangiji Allah yayi miki rahama. "
