page 3-4

170 11 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_.
☘☘ ☘☘ ☘☘

*AMATULLAH*
_baiwar allah..._

☘☘ ☘☘ ☘☘

©
ZEENAT DEEN SHAXEE
_________________

FACEBOOK
zeenat deen shaxee

WATTPAD
@zeenatdeenshaxee

EMAIL
zeenatdeens@gmail.com

ina godiya dunbin masoya allah yabar kauna ina farin cikin addu ar ku agare ni nagode sosai🥰


PAGE 3-4

------------------------------------------

Suna zuwa suka,nuna katin shedar su aka,barsu suka,kutsa kai,ciki Abdullahi ne ya,kalli Sadiq yace." Kaga office din ajiye fayal din masu laifi mu fara tanan abun saiya fi zuwar,man da sauki." " Aiku kakawo shawara ni duk,hankalina,yana kan in fara ganin yarinyar ne to maza muje gun Mariya kasan munfi shiri da ita gata da tausayi." kai tsaye wani gu sukayi suka shiga wani karamun office inda in bursuna bashida lafiya ake kaishi nan aduba shi wato asibintin su kenan kai tsaye gun wata mata suka nufa wacce bazata huce shekara 46yr ba cikin kaya farare tana rubutu waje suka samu suka zauna." Sistar Mariya yakike." cikin fara a ta dago kai ta kallesu tace." Kannena yakuke yanaga yau kundawo kuma ina fatan dai lafiya kuke."

Murmushi sukayi sannan Abdullayi yayi,mata bayanin komai kasan cewar,akwai,wata alaka mai karfi atsakaninsu jimm tayi sannan tashare wata kwalla afuskar ta.

Ganin kwallar ta ba matukar tashin hankali suka shigaba tashi tsaye tayi tace musu." Kubiyo ni muje." tana gaba suna baya sun shiga rudu suna son yimata tambaya amma,bata basu dama ba.

Wani katon daki suka shiga idda yake dauke da fayal kala kala benci ta nuna musu tace." Kuzauna anan kubani muntuna kadan ina zuwa."

Zama sukayi suna kallonta wata durowa ta bude tana cike da fayal ne sauke su tayi daya bayan daya sannan ta dakko wani fayal ta kakkadeshi ta nufo gurinsu ta zauna ta ajiye fayal din sannan ta kallesu tace." Amatullah yarinya ce mai matukar hankali tausayi dakuma mutunta manya harma da wadan da suka girmeta tana mutuntasu, shekara daya baya aka kawota gidannan saka makon yanke mata hukuncin rai da rai da akayi mata ana zargin ta kashe wasu samari guda uku a SHU'UMA HOTEL." shiru tayi tana kallonsu dan taga awane yanayi suke.

Bakaramun tashin hankali suka shigaba sunata zazzare ido murmushi tayi wanda,bai kai zuciba sannan ta cigaba da cewa." Bayan zuwanta gidannan nafara kula da yanayin ta inda nafara zargin akwai,wani abu akasa wasu lokutan takan zama taita kuka kamar tanta zai futa tana magana kasa kasa dana takura mata sai take cemun inma nagaya miki,gaskiyar lamarin ba abunda zaki iya yi amma nayi komai saboda iyayena ne kuma. Saitayi shiru taki rasamun har yanzu danake muku,wannan zancan bata,gayamun komai ba amma abunda yake sani takaici shine wasu mazan ma aikatan mu,nanan suna rashin tsoron Allah kaga sun bata wasu da aka kawo kosun kulla muguwar alaka dasu shiyasa nake kula da ita sosai."

Cikin karfun hali Sadiq yace. "Yanzu ta ina kike ganin zamu fara wannan abun dimun nima daha jin wannan guntun labarin nakara jin wani karfin gyiwa da son yin bincike akan wannan lamari ko kira mana ita zakiyi." " a a baza ayi hakanba ku,ungo wannan fayal din copy ne damuke,ajiyewa kuje ku duba shi anute sosai saiku fara buncike ta hotel din gashinan hadda karamun hotonta aciki daga naya kwa hadu da ita." " To babbab yaya hakan kuwa za ayi bara muje sai ajima." tashi sukayi suka futo suna kara tattauna maganar cikin jimami,da daure kai.

WASA FARIN GIRKI,YANZU AKA FARA WANNAN BADAKALAR.🥰

AMATULLAHIWhere stories live. Discover now