Babi na bakwai

5.3K 335 60
                                    

💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
    🌺💖🌺💖🌺
       🌺💖🌺💖
          🌺💖🌺
              🌺💖
                💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺    ▶2⃣1⃣


_yar fadakarwa_

_*shin ko kinsan gwalagwalan kwanakin da muke ciki 'yar uwa?,kwanaki ne masu matuqar tsada da daraja har agun Allah madaukaki,kwanaki ne da ayyukan alkhairi suka fi soyuwa agun ubangiji a cikinsu,kwanaki ne mafi daukaka cikin kwanakin shekara,an karbo hadisi daga imamu bukhari r.a,annabi s.a.w yana cewa(babu wasu kwanaki da kyawawan ayyuka sukafi soyuwa agun ubangiji kamar kwanakin goman farko na watan zulhijja,sahabbai suka ce da annabi hatta jihadi saboda Allah?,annabi yace eh har jihadi,saidai mutumin da ya fita jihadi da ranshi da dukiyarshi bai dawo da komai ba),shin me kike aikatawa na neman lada?,kada ki yarda su shude ba tare da kin amfana da komai ba,baki da tabbacin ganin na wata shekarar,Allah ya karbi ibadun mu yasa mu dace ameen*_

🕋🕋🕋🕋🕋🕋🕋

Minti talatin suka isa asibitin da nasir ke aiki,ta taradda marasa lafiya da suka rigata zuwa,hakan yasa tabi doka itama ta hau kan layi,don ta sani indai tace masa ta zo babu makawa sawa zaiyi ta shiga kawai ita kuma ba zata so shiga haqqin wani ba.

ko kafin azo kanta tuni ta qosa,jira ne na tsawon awa guda da rabi kafin ta samu shiga,da mamaki yake dubanta tare da fadin
''yau kuma an tuna da mu kenan''
dan qaramin murmushi tayi kan ta haye kujerar da masu buqatar ganinshi ke zamansa
gaisawa sukayi yaso ya dan tsokaneta yadda suka saba sai kuma ya fuskanci yanayinta ba yadda ya saba ganinta bane.

madaidaiciyar handbag dinta ta zuge ta fiddo da leda bag din ta dorata saman table dinshi
''taimako nake buqata daga gurinka nasir ko zaka iya yimin shi?''
''me zai hana maryam indai ba kaucewa addini ba''
''abunda ke cikin nan nake da buqatar a duba min ko akwai poising a ciki?''
ido ya dan zuba mata kamar mai buqatar qarin bayani,ganin bata da niyyar qara masa haske yasa ya kauda idonshi kana yace
''ok,ba damuwa,ga kujera can zauna bari na kira lab azo a dauka''

cikin mintina uku kacal wani matashi ya shigo sanye da farar labcoat ya dauki ledar ya fice.

mintina arba'in din da yayi kafin ya dawo jinsu tayi kamar awa arba'in ne,tuna ni babu kalan wanda bata yishi ba,dawowarshin tayi daidai da kammala ganin patient da nasir yayi,hakan ne ya bawa matashin damar zama tare da miqawa nasir result din ya ajjiye ledar a qasa yana duban fuskar nasir din.

nuni ya yiwa maryam din da hannu kan ta taso idanunshi na cikin takardar,a sabule ta iso gaban teburin ta samu kujera daya cikin biyun dake gun ta zauna
''maryama....taya aka samu irin wannan mummunar gubar cikin abinci?,kinsan nau'in guba iri wannan bamu da ita ma sosai cikin qasar nan?,guba ce da ke iya kashe mutum cikin mintunan da basu gaza biyu ba,baya ga haka hatta da gawarka ma bata qyaleta ba sai ta narka duka kayan cikin mutum,dubi yadda ta maida wannan dankalin''ya mata nuni dashi dake cikin ledar da yasa matashin ya bude.

A hankali ta maida firgitattun idanunta kan ledar,dankalin ya zagwanye ya koma kamar ruwan kunu,hakanan gabaki daya kalarshi ta sauya zuwa kore da baqi,kumfa ce kawai ke tsattsafa a samanshi tamkar ya shekara ne da sarrafawa ba kwana daya ba,wani irin tsoro ya sake kama maryam,da sauri ta maida idonta kan nasir,cikin rawar murya tace
''ko zan iya ganinka kai daya?''
''why not?,sadam dan bamu guri''

office din ya rage daga ita sai shi,a hanakali ta zayyana masa dukkan abunda ta sani,ya jima yana jinjina kai kafin yace
''maryam akwai hadari mai girma tattare da gidan,saidai abu guda da ban goyi bayanki ba barin gidan da kike shirin yi,barinki gidan ayanzu dai dai yake da mutuwar abdallah da maharfiyarshi,bayan kin gano matsalar da su basu san da ita ba,shawarar da zan baki shine kawai ki zama mai matuqar kula da takatsantsan,abu na gaba shine ki riqe addu'a,qarfinta da kaifinta ya sha gaban duk wani kaidi da zalunci''

ABADANWhere stories live. Discover now