Babi na sha uku

8.3K 339 65
                                    


💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
   💖🌺💖🌺
    💖🌺💖
      🌺💖
          💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
      🌺💖🌺💖
        🌺💖🌺
          💖🌺
             💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
  *_home of expert and perfect writers_*

        ▶3⃣9⃣

🎶🎶🎶🎶

*_alqawari ki riqeeee..komai wuya karmu rabu kinji..._*
*m sharif song for dis page*
😜😂

A hankali ta dinga bude idonta da taji ya mata nauyi sakamakon kumburar da sukayi,tana gama budesu tarwai komai ya dawo kanta,abu na farko hawaye ne ya fara bin idanunta kamar yadda ya ta kwanta da shi,jin alamun motsi daga qasa ya sanyata wurga idanunta can,abdallah ne zaune kan sallaya,ta dubi agogon dakin qarfe bakwai saura na safe,da sauri ta miqe cikin zuciyarta tana istigfarin rashin yin sallar asubahi akan kari,jiki babu qwari ta zuro qafafunta qasa motsin wannan ne ya juyo da hankalin abdallah kanta

sai ta kasa tashi don batasan ina toilet yake ba,da suka hada idanu kuma sai ta dauke kanta gefe guda
''ga toilet din can''ya fada yana kada yatsunsa tare da yi mata nuni,ta jishi sarai saidai ba zata so ta tashi ba saboda rigar baccin jikinta gajeriya ce,gashi ta wuwwurga idanunta ko ina bata hango kayanta ba,zanin gadon ta yayaye kawai gaba daya duk da girmansa ta lullube jikinta da shi kana ta samu sukunin shigewa bandakin

kuka ta zauna yi riris kan daddumar,tana ji har cikin zuciyarta abdur rahim ya zalunce ta abdallah ya cuceta,don ko kadan bata da plan din auren abdallah akundin rayuwarta,sai gashi dare daya wata qatotuwar qaddara mai wuyar afassara ta fada mata,abdallah mai girmankai,mai izgili mai taqama da dukiyarshi,mai tutiya da kyawun surar da Allah ya bashi,abdallah mai tarin 'yammata,ko baya ga haka ma sama ai ta yiwa yaro nisa,ina zata kai abdallahn,batajin cikin tarin masoyansa ita din karanta ya kai tsaikon da zata daga hannu,me take da shi da zata nunawa duniya amatsayin matar abdallah abdulkarem mai nasara?,yaro dan gata gaba da baya da daya tilo tamkar tsoka daya cikin miya,mai tarin kyau asali dukiya da arziqin ma baki daya,ta ina tarayyarsa da maryam diya ga malam amadu zatayi daidai,masu nema da qyar suci da kansu da qyar,diyar da ta taso cikin qunci hantara da takurar rayuwa?,rufin asiri take nema da girma ba bankada da tonon sililin asirinta va,ta iya talaucinta haka zalika ta iya tsayawa iya matsayinta,to akan me yanzu zata yadda ta sarayar da dukka wadan nan abubuwa?,ko ta zuba ido abdallan ya sarayar mata da su lokaci guda

tasha ji daga bakunan wasu matan yadda auren mai dukiya quruciya da kyau yake zamewa mace qarfan qafa alaqaqai,don me zata zira kanta rijiya mai gaba dubu?bata taba sha'awar auren mai tarin dukiya irin abdallah ba,balle shi din da tasha jin kalmomin nuna ko shi waye da matsayin da yake ji ya taka daga bakinsa,idanuwanta sunsha nuna mata kala kalan 'yammata dake hauka akanshi,tana cikin wanna tunanin ta tsinci tafin hannunshi dafe da saman qafafunta,da sauri ta janyesu ba tare data daga kai ta dubeshi ba
''maryam''ya kirata asanyaye
''ko baki fada ba kuka kike''
''kuka na ya zama dole,auren dole qiriqiri?,irin auren dolen da ko a fina finai ban taba cin karo da shi ba sai gashi yau ya faru a kaina?,ka fada min wanne mataki ka dauka game da zaman mu,zaman mu ba mai yiwu bane''
''ki bani dama maryam ni zan mai da shi mai yiwuwa,indai matsalar taki ta zuciya ce,zuciyarki bata san abdallah,ta bawa abdallah dama na kwana talatin cif na rantse miki sai taso abdallah fiye da yadda take son kanta''
''ka taba ganin inda ruwa da wuta suka cakudu suka zauna guri guda lafiya lau?''
ya fuskanci mai take nufi da maganarta don haka bata buqatar amsa

kusan mintina goma shiru ya ratsa tsakaninsu,ta qagauta ya janye jikinshi daga inda take,ganin babu niyya tasa ta bude bakinta murya can qasa
''ka matsa daga kusa da ni,kuma ka cika min alqawarin da ka dauka min daren jiya yanzu ba sai anjima ba''
gayara zamanshi ya kuma tamkar ma bada shi take maganarta ba
''naji,zan sakeki.....amma bisa wani sharadi guda''
tunda suka fara maganar bata dago ta kalleshi ba sai a yanzu
''ba buqatar wani sharadi daga gareka ko wanne iri ne saki nake so,kuma dole ka sakeni''
ya sanya fitinannun qwayoyin idanunshi cikin nata kana ya tabe baki
''babu dole fa maryam,abdallah ne mijin ba wai maryam ba,idan kin amince zan gaya miki sharadina daya ne zuwa biyu da zarar kin cika sharadina ba tare da bata lokaci ba agobe ma kina iya tafiya da takardarki''idanunta ta lumshe saboda yadda ya nutsa qwayoyin idanunshi cikin nata yake mata magana haka kanshi tsaye kamar ba mai laifi ba

ABADANWhere stories live. Discover now