11

5.1K 241 18
                                    

*_~A DUNIYARMU~_* 🌍

© _*MAMUH GEEE*_

*Dedicated to*
_Ummy Aisha_
_Mammy wambai_

*_Ashe haka a duniyarmu keda masoya_*
*_to Emraan da A2 sun gode da soyayya_*💋

*34*
A mota kafin sukai farin ciki yake matuqa da labarin bayyanar ayshar sbd farin cikinsa na ganin matar yayansa da 'yayanta ya cika.
Allah yaji qanka Yaya Abu""yafada cikin ransa lokacinda yake parker motarsa a harabar asibitin.

Tashin hankalin ganin iyalan gidansu Emraan yasashi tsayawa cak bakin qofa

Emraan kuwa tasowa yayi yana auna masa kallon tuhuma.

Gabansa ya tsaya tareda zuba hannuwansa biyu aljihu cikin kakkausar murya yace,

Where is she?

Dad,mum da asheer suka matso kusa dad na cewa,

Yaya akayine Emraan?

Batareda ya 'dauke idonsa daga kan fuskar Alh manga ba yace,

Dad wannan mutumin banzar da kake gani shine Alh manga Wanda ya lalata rayuwar shukrah kuma a yanxu ina mai tabbatarda kowa zaiyi mamakin abinda zanyi masa ciki harda 'daukar ransa matuqar bai fadamin gidan uban dayakaimin mataba.

Mommah da mufeeda atare suka kallesa cikin tsoron abinda Emraan yace.

Shi kansa Alh manga ba qaramar zana da 'dimuwa yashigaba daya fahimci kenan A2 itace Aysha 'yar 'dan uwansa uwa daya uba 'daya dasuke nema tun ranar daya hadu da mommah yasan dasuna raye Ashe.

Mommah kuwa jikintane yayi mugun sanyin cikin jin zafi da tausayin 'yarta tace,

Manga ka ruguza rayuwar 'yar 'dan uwanka da kanka kayi mata tabon mugun suna dan kwadayin abun duniya,
Kayi mata barazana da kudi ta saida maka 'yancinta yau gashi kanka kayiwa tunda 'yarkace.

Kasa magana yayi sbd mugun sanyi da jikinsa yayi tareda kunya da baqin cikin abinda ya ringa sa A2 Ashe 'yarsa ce gashi a duniya ba abinda yakeso sama da 'dan uwansa yanxu da babusa 'yayansa yakeji kamar shi amma son kudi da rashin sani yasa ya wargaza rayuwar Aysha.

Jan Emraan asheer yayi suka bar asibitin sbd yasamu fresh air zuciyarsa ta lafa.

Mum ce tayi qarfin halin bawa mommah hkr tana qara jinjina alamarin tareda fayyacewa mommah komai har auren ta da Emraan.

Dana sani da tausayi tareda sabuwar soyayyar 'yartane ya rufeta ta rintse idanu tana adduar Allah ya bayyana musu ita duk inda take.

******
Bayan kwana biyu aka sallamosu suka dawo gida Wanda yanxu duk wata 'dawainiyarsu Emraan ne keyinta.

Tausayinsa sosai mommah takeji sbd tana lure da yanda damuwarsa kullum take tsananta.

A gefe guda kuwa fushi mai tsanani ta 'dauka da manga Wanda tai alqawarin idan ba ganin shukrah akaiba babu ita babushi har 'yayanta.

Al'amura sun qara tsananta garesa sbd dukiyarsa daketa lalacewa ga matarsa data shirga masa uwar sata ta gudu gashi ko 'dan kansa bayada da yana murna yasamu 'yayan yayansa to gashi Abu ya kwa6e.

Lokaci ya tafi sosai babu wani lbarin za'a ganta,

Emraan kuwa kullum yanxu a gidansu mommah yake rabin yini harsun saba dashi bama kamar mufeeda da ameerah.

******
Zaune take ta rafka tagumi tana tunanin a ina zata samu kudin dazata sayi kayan haihuwar shukrah sbd ko wane lokaci haihuwa zata iya zuwar mata sbd harta wuce edd nata.

Shukrah dake kwance tana bacci taji kaman an mintsineta ta tashi da sauri saikuma taji mararta ta riqe da wata irin azaba.

Washi Anty kubrah cikina ciwo.

A DUNIYARMU✅Where stories live. Discover now