55,56,57 and 58

6.5K 394 6
                                    

55



Zuhra na hada kayan wanki a dakinta Hamza ya shigo yace su shirya yaji jiya suna zancen zuwa salon ita da su Adabiyya. Taji dadin hakan sosai dama a dalilin bata son auren taki yarda a saka mata relaxer a kanta wai kada ya rinka hanata zuwa tunda yace kuntata mata zai yi a gidansa. Dubu ashirin ya bata ita da su Hamida kowa yayi abinda yake so. Zuhra ta bude baki, wannan kudin yayi yawa har ka manta zancen da muka yi dazu? Ban manta ba baki nayi ki rike a hannunki koda bukata zata zo miki. Tayi ta masa godiya duk da a ganinta kudin sunyi yawa. Shabiyu saura suka fita tare ya sauke su yace zai je unguwa idan sun kusa gamawa su kira shi. Zuhra tace ai babu nisa sosai muna tafe muna hira ma sai mu koma. Su Adabiyya dake bayan motar yacewa su fita su jirata a ciki. Suna tafe suna waige da yiwa yayan nasu dariya har suka shige. Ya mayar da hankalinsa gareta. Akwai abinda kike so na taho miki dashi ne? Ta girgiza kai Allah Yasa kaje lafiya ka dawo lafiya. Allah Ya bada abinda ake nema. Ya nuna mata jindadinsa da adduarta yace nagode sai na dawo. Da ta fito wata mata ta gani ga baby a hannunta ga jaka da zanin goyo duk kayan sun mata yawa. Da sauri ta karasa ta tare mata jakar da ke shirin faduwa. Matar tayi murmushi kai amma nagode miki. Sai da na zo nan hannun jakar ya tsinke ga Muhsina ta min kuka. Zuhra ta karbi yarinyar matar ta hade bakin jakarta da zanin goyon suka shiga tare. Har su Adabiyya sun kama mata layi da yake weekend ne wurin ya cika. Wuri daya Zuhra da matar suka zauna tana ta yiwa yarinyar wasa ita kuma tana dariya. Matar tace ni sunana Sa'adatu ke fa? Zuhra ta fada mata sunanta tace ina son baby dinnan. Sa'adatu tayi dariya ai naga alama kema tana sonki don kyuya take yiwa mutane amma gashi tana miki dariya. Suna hira matar tace ita har lalle zata yi. Hamida ta taso daga inda Adabiyya ke tayata tsifa Anti don Allah kema kiyi lallen wallahi Yaya yana so. Duk sallah baya fashin bamu kudin lalle ko Adabiyya. Adabiyya tace ce eh. 

A wani daki ake yin lallen Zuhra tabi bayan Sa'adatu ta shiga. Ai kuwa mutum daya suka tarar ana tsara mata ado sosai. Sa'adatu tace ni dai kada kiga ina ta kallonki wallahi kamar na taba ganinki a wani gida. Zuhra tace kila mun hadu, a wace unguwa ne? Sa'adatu ta soma bata labarin wasu da suka tare a unguwarsu ana walima aka yiwa wata April fool. Wallahi sai kuke dan yimin kama da yarinyar duk da ba kare mata kallo nayi ba. Murmushi Zuhra tayi sannan tace nice yarinyar. Sa'adatu ta bude baki don Allah da gaske? Ana ta rade radin mijin matar ya auri yarinyar. Don Allah ke ce? Zuhra tayi ajiyar zuciya. Nice, har an kusa wata biyu da auren. Sa'adatu tace lallai Zuhra rayuwarki ishara ce ga wawayen mata. Duk yawancin matan unguwar nan da Izzatun nan ta gayyata walimar tarewarsu sai da suka zageta ranar da abin ya faru. Yadda kika san kanwata aka yiwa wulakancin nan, har maigidana na bawa labarin abinda ya faru. Mai lallen ce ta fita karo leda Sa'adatu ta matso kusa da Zuhra. Ko baki fada ba nasan aurenku da mijin Izzatu bazai zama na jindadi kamar na kowa ba duba da irin abinda ya faru da farko. Amma zan baki shawara ki rike mijinki sosai yadda har abada idan Izzatu ko mai hali irin nata tayi niyyar daukan al'adun wasu zata sake tunani. Kinga yau muka fara haduwa amma haka kawai naji ina sonki da alkhairi. Zuhra dai sai murmushi take yi. Auren da yake da lokacin karewa wane rike miji zata yi?... Sa'adatu tace kina son mijin naki? Kanta ta sunkuyar kasa kawai tana murmushi. Ai an gama wannan murmushin naki ya isheni amsa. To kalleni da kyau bari na koya miki karatun saye zuciyar mijin matar da bata san inda ke mata ciwo ba. Ina ma da Ummu Sudais muka zo wurin nan. Don baki ga yadda tafi kowa jin haushi ba ranar. Kada kiga kamar cin fuska amma ko ba'a fada ba wayewarki da ta Izzatu ba daya ba. A irin haka tayi miki wayo har hakan ta faru. Abu na farko da nake so dake shine daga yau mijinki ya ga kin canza masa gabadaya. Canji irin wanda zaisa ko fita yayi yana tunanin Zuhra a gida. Ki rike TSAFTA  sosai domin ita ce abu na farko da kowane miji yake nema daga matarsa. Duk kyaunki da iya kwalliya idan baki da tsafta ko jiki na wari miji bazai so kusantarki ba. A hankali kuma zaki fice masa a rai ya fara neman wata. Na biyu ki iya KWALLIYA irin ta zamani amma fa ba mai yawa da za'a kasa ganeki ba saboda tsabar fuska tasha fenti. Na uku SHAGWABA,Zuhra ba sai na bata lokaci ba a nan. Duk mijin da zaki mayar da kanki yarinya a gabansa dole ya soki. TATTALI DA ADANI yana da kyau ga dukkan matar aure. Babu namijin da zai so ya auri matar da take da almubazzaranci. GIRMAMA IYAYE da son 'yan uwan miji shima yana karawa mace daraja a idon mijinta. IYA ABINCI wannan kowa yasan shine jigon dorewar zaman lafiya a gidan aure. KULAWA, maza nason mace ta kula dasu tamkar yara kamar yadda muma muke son hakan. Ki rage kunya domin ba'a son don kinyi aure ki ajiyeta gabadaya, ki nunawa mijinki so da kauna ta sigar da zai manta da yadda ya auroki ya rike ki da zuciya daya. Ke kike aurensa saboda haka kinsan bukatunsa, idan baki sani ba kisa ido sosai ki nemi soyayyar mijinki da gaskiya. Abu na karshe kuma mafi mahimmanci shine ki rike ALLAH SWT DA MANZONSA SAW, idan kika yi haka to in sha Allahu komai zai zo miki da sauki. Mu 'yan unguwar nan duk 'yan bayanki ne wallahi. Abinda duk ya shige miki duhu zan baki numberta sai mu rinka zumunci.

AL'ADUN WASU (Complete)Where stories live. Discover now