15

805 33 0
                                    

☠TSAFI ☠

          15

Hafiz yay shiru jikinshi na kakkarwa.  Malam ya daga kai ya kalli agogo karfe 6:30Am na safe. Ya kalli Hafiz yace"munada number iyayen Bilal ko? "Hafiz ya gyada kai Malam yace "jeka kirasu,kace suzo harda iyayen Julaibib, Idan kagama ka dubamin Farida idan maganin dana samata ya saketa kazo kafada min". Hafiz ya gyada kai yafita daga dakin.

Malam yaje gaban table din magunguna yahada wasu hadehade yazo ya shafa akan jirwayen jikin Julaibib sanan ya koma kan gadon Bilal yana karemai kallo ahankali ya sauke ajiyan zuciya "ka kusa warkewa da izinin Allah". Bude kofan dayaji anyi yasa ya daga kai ya kalli Hafiz dake shigowa yakaraso wajen Malam yace"Abba Baban Farida yadau wayan nafada mai kana nemanshi yau, dukya rude nafada mai Julaibib da Farida duk suna nan, yace yau zasuzo zakuma sutaho da Hajiyar Julaibib dan baida Baba". Malam ya gyada kai"Masha Allah,Farida fa?"   Cike da damuwa ya kalli Abban shi "Abba maganin ya gama cinyewa,bata komi tana zaune a tsakar dakin, bandaiga fuskarta ba,dan ta rufe fuskarta da gashin kanta" Malam yace"Masha Allah,wanan karan zan riketa a wajena na wata daya dan saina tabbatar ta warke zan barsu  su tafi da ita, bari naje nabata maganin safe".  saida yakara sauti karatun Al qur'anin dake tashi kadan kadan a dakin sanan yadau jakar magani katuwa ya mikama Hafiz yarikemai suka fito tare ya kulle kofar.
Wani Bangare daban suka tafi ahankali Hafiz ya bude kofan Abba ya shiga Hafiz ya ijiye jakan akasa. Abba ya maida kofan ya rufe ya karaso cikin dakin da babu komi ciki sai gadon marasa lafiya da katon radio da karatun Al qur'ani ke tashi daga ciki kadan kadan, Ahankali Malam ya tsugunna ya dau wata yar kasko yabama Hafiz "samomin rushi wurin Babar ka" Hafiz ya karba yafice da sauri,Malam ya zauna akan kujera ya ijiye jakan a gefe "Farida " ya kira sunan Eeel cikin tattausan murya amma shiru saima dakin daya amsa sunan. ahankali malam yakara cewa "Farida bazaki fito kizo ba"  shiru dakin babu wanda ya amsa, gyara zama Malam yayi akan kujera ya zage jakan maganin yana kokarin ciro jan al miski daga jakan, karan dayaji kaman na karfen gado yasa ya dago kanshi da sauri amma ina tuni wata da banga fuskarta ba saboda gashin daya rufe fuskarta harzuwa cikin ta, tahau kan jikin Malam ta shakema Malam wuya cikin wani irin murya kaman ta maza guda Biyar tai magana "Abu Talib karabu da Farida,wlh duk wanda yace zai taimaki Farida halaka, fitina,mutuwa shine sakamakon shi, karkaga jiya ka wuni kana konamu, kana shakamana turare, ka kyalemu ka rabu da Farida kafin mu nakasa ka" ahankali Malam yakarasa ciro Al miskin hanunshi daga jaka yana karanto addu'oi da dama a ranshi ta baya ya bude Al miskin ya juye shi akan Farida wacce da sauri ta sakeshi tafadi akasa warwas, yayinda wani irin iska ya bude windunan dakin, tsugunnawa Malam yayi a saitin Farida ya lakaci al miskin ya samata a hanci da gefen kunne sanan yafara mata ruqya. Hafiz ya shigo dakin ya ijiye kaskon rushin ya zauna kan kujera tsawon awa daya Malam ya dauka yanama Farida karatu aka kafin ya koma gefe ya zauna "jeka karbomin kayan Baddiya kala daya" Hafiz yace "to" yafita.
Ahankali Farida ta tashi ta zauna tana tattara gashinta kakkyawar fuskarta ya bayyanah, kallon jikinta tafarayi da inda take Malam ya kira sunanta "Farida " dago kai tayi ta kalli wani magidanci ma'abocin yalwataccen gemu.  Kuka tafara sosai  tana kallon shi tana matsawa baya dan wani irin tsoranshi taji tanaji taga kaman ta sanshi amma ta manta fuskar "kinajin yunwa?" Ta girgiza mai kai da sauri,bude kofan da akayi yasa ta cigaba da kuka Hafiz ya mikama Abban shi kayan yana kallon Farida. Wani yar roba Abba ya dauka ya shiga bayin wurin da kanshi ya hadama Farida ruwan dumi a bucket ya zuba garin magani aciki ya sahannu ya jujjuya. Ya ijiye mata wani sabulun salon magani sanan ya fito kayan da Hafiz yakawomai na Baddiya ya dauka yabama Farida dake kuka "tashi ki shiga bayi kiyi wanka da ruwan dana hadamiki a bucket da sabulun,ga kayanan kisa inkingama saiki fito,ki dena kuka yanzunan zan baki abinci kinji" da kyar ta mike tsaye ta karba tana share hawaye  ta juya shiga bayin dayake nuna mata.
Maman Abd Shakur 😘

TSAFIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora