#Duk a asanadin soyaya#
#By SAFNAH ALIYU JAWABI#
#Bismillahi rahamanin rahim#
Sosai jikin labiba yaye sauki tunda yanzu zagewa take su kwashi hirar su Mai tsayi da afeeya ,tun tana nokewa harta saki jiki da ita, mummy MA tazo har asibitin ta gaishe ta, sannan ilham MA ba'a barta abaya ba tana zuwa lokaci lokaci, Abu ďaya ke damun labiba 'idan ta tuna kwanakin daya rage ayi bikin raihan,raihan kuma nata amma bada ita za'ayi auran ba.
Duk lokacin data tuna da hakan takan tsinci kanta awani mawuyacin halin, takanyi kukanta iya son ranta hakan yasa har yanzu magungunar da Dr yake bata basa aiki sosai Dan sosai take cikin damuwa.
Tunda sayin safiya Sadiq ya nufi asibitin yana shiga wayar sa ta fara ruri, koda yaduba raihan ne yarya tsinke bai ďauka ba, murmushi yayi yace, "ina kwana aisha, yanda ya kira sunan nata saida taji yarrr acikin jikin ta, kasa Ďago Kai tayi tace, "kayi hakuri naga kamar zaka amsa Waya ne, ina kwana?
"lafiya lau aisha ya jikin naki?
Bata kaiga buďi baki ba Dr ya shigo da murmushi asaman fuskar sa ,musabaha sukayi sannan ya shiga tambayar ta yanda takeji,rike kansa yayi yace, "kash aisha kina da matsala wai sai yaushe zaki cire damuwa acikin ranki ki bari ki samu lafiyar jikin kine wai?
Tsareta da ido Sadiq yayi yana karantar yanayin ta, kasa buďi baki tayi dan ganin yanda duk suke mata kallon tuhuma.
Juyuwa yayi ya fuskanci Sadiq yace, "yallabai inaga zamu cigaba da riketa anan Dan gaskiya har yanzu bugun zuciyar ta bai daidai taba, nod dakai kawai sadiq yayi dan zuwa yanzu ta fara bashi haushi, har zuwa yaushe zata cigaba da saka kanta a damuwa saboda wani banza can wanda baima San tana Raye ba.
Saida dr ya ya tabashi sannan ya dawo daga duniyar tunani daya faďa, takarda magungunar da za'asaya ya Mika masa, karba yayi yayi masa godiya sannan suka fice harshi.
Kuka Mai ďan sauti ta shiga rerawa gwanin ban tausayi,harya dawo bata Sani ba sai jin muryar sada tayi daga sama yana cewa, "aisha make damun ki?
Cike da firgici ta Ďago Kanta Sam bata so yadawo yasame ta acikin wannan yanayin ba, duk tunanin ta yatafi ne, to Ashe sayo magungunar ya tafi ,shiru babu amsa banda hawaye babu abinda ke zarya kan fuskar ta.
Zama yayi dan nisa da ita yana sauraron yanda kukanta ke taba duk wata gaba ta jikin sa,sam kaunar ta da tausayinta sun kasa barin ilahirin ruhi da gangar jiki sa,buďi idanuwan sa yayi cikin muryar sa Mai daďin sauraro yace, "aisha nasan damuwar ki,ki Sani da ina da ikon dawa da raihan cikin rayuwar ki da tuni na yi miki hakan, Dan jinki nake kamar yanda nake jin afeeya da ilham a jiki na, 😲😲Waro ido nayi nace, "Kaidai faďi gaskiya malam Sadiq.
"ki Sani idan kika cigaba ahaka tofa rayuwar ki tana cikin hadari duba da abinda Dr yafaďa mana akan ciwon ki ko sokeki ki rasa ranki kan wani can wanda harkar gabansa kawai yake.
Girgiza kanta tayi cikin sauri alamar aa ,Murtuke fuskarsa yayi yace, "idan har kina so mu shirya to ki cire duk wata damuwar raihan aranki, kinji?
Nod dakai kawai tayi masa, murmushi yayi yace Yauwa labiban afeeya.
Murmushi ne yasubuce mata jin sunan daya raďa mata.
