❄❄❄❄❄❄❄❄
*DUK A SANADIN SOYAYYA*
❄❄❄❄❄❄💐
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞( _WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ 💪)
https://www.facebook.com/100452275039839/photos/a.100452311706502/100452611706472/?type=3
*P.W.A*✍️
1⃣5⃣
*STORY*
*&*
*WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
Bismillahi rahamanin Rahim
Hira suke sosai saidai gabaki ɗaya hankalin labiba nakan halinda raihan yake ciki, ganin basuda niyyar mayar da ita gida yasa ta ɗanyi murmushi tana kallon Hafsah tace, "Lil sis Sallah nake so nayi kinga lokaci yana tafiya sonake natafi gida.
Mararrace Fuska tayi tace,"haba aunty labiba na ɗauka anan zaki kwana ai?
Cefa maganar sadiq yayi yace, "barta ta tafi Lil sis tunda nanɗin daji ne.
Kallon sa tayi taga Ya Turbune Fuska kamar bashi yayi maganar ba, mum kuwa kawar da kanta gefe tayi kamar bata wajan, ita kuwa ilham jitake tamkar akanta labiba take tsabar kosawa da tayi ta tafi.
Yake labiba tayi dan gaskiya batason batawa mutum ɗaya daga cikin ahalin nan Dan irin kaunar da suka nuna mata musamman sadiq tace, "shikenan mayar da wukar Lil sis na fasa tafiya sai gobe zantafi.
Duk kansu Dariya suke dan sunsan Sarai da sadiq take bada Hafsah ba, Dan asalima ita bata ɗauka da zafi ba.
Ilham kuwa mikewa tayi ta nufi ɗakin su,tana Shiga ta faɗa gado wani irin kuka ta fashe dashi tana tausayin kanta Dan tasan yanda sadiq yake mattukar kaunar labiba muddun yasame ta tofa babu makkawa ita da samunsa har'abadan.
Jin motsin sune yasa tayi saurin goge kwalla ta shige toilet, tsaf Hafsah ta fahimci halinda take ciki, itadai kullum addu'ar ta daya ALLAH yazaba musu abinda yafi Zama alkairi a tsakanin su.
Saida tayi mintina aciki sannan ta fito, ganin yanda idanuwan ta suka canza launi yasa labiba tambayar ta abinda yasame idonta, saurin wayan cewa tayi tace, "wallahi tun jiya wani kwaro yafada min,amma yanzu yayi sauki.
ALLAH yakara sauki sukayi mata sannan suma suka shiga suka gabatar da Sallah,bayan sun idarne, kiran Sadiq yashigo wayar Hafsah , cikin sauri ta ɗaga, kuyi sauri ku sameni amota yanzu,bai tsaya jiran amsarta ba ya kashe Dan Sarai yasan saita tambaye shi inda zasu tafi.
Sanar dasu sakon sa tayi, amma kememe ilham tace, "babu inda zata tafi idonta na ciwo, haka sunaji suna gani suka fita suka barta, koda sadiq yaga basu tawo da itaba sosai yaji daɗin hakan,saidai gudun kar labiba ta zargi wani abun yasa ya tambaye su ita, koda suka faɗa masa shiru yayi baice komai ba, yaja motar sa sukayi gaba.
Wani makeken
Shopping moll yakaisu,umartar su yayi dasu ɗauki duk abinda suke da bukata,Hafsah lodan kaya take babu kakkautawa, juyawar da zatayi taga labiba hannu aninke tana binta kamar rakume da akala, zungurar ta tayi tace, "aunty labiba baki ɗauki komai ba.
