LABARINA 11

210 12 0
                                    

*☪💗 LABARINA💗☪*

*By*
*SHAMSIYA ABDULLAHI (Mrs Yahaya)*

My social Accounts👇

Facebook *Shamsiya Yahaya*

Facebook group *Ummu dilshad Novels*

Instagram *@Official ummu dilshad*

WatsApp *07013872581*

Wattpad *@UMMU_DILSHAD*

OkadaApp... coming soon....

👩‍👩‍👧‍👦Muna Tare🤝 Writers Association ✍

*✨M.W.A✨*

*Motto: we stand and fall together .*

*BISMILLAHIRRAH MANIRRA HEEM*

*Tunatarwa*

*Bismillahillazee Laa yadurru ma'a'ismihi shai'un fil'Ardi Walaa fissamaa'i Wa huwassami'ul Aleem*

Wannan addu'ar daya take daga cikin addu'oin mu na azkar din safe da yamma ana karantata kafa 3, koyarwar fiyayyen halitta manzon tsira Annabi Muhammad sallallahu Alaihi Wasallam, Allah yabamu ikon aikatawa Ameen🤲

Dedicated to, *Yuhanis* *(Ummu janan soupnass)*
Tareda yimiki ta'aziyyar uwa mahaifiya suruka Allahu subhanahu wata'ala yamata Rahama yasa kudawo lafiya, yasa Aljannal firdaus ce makoma, Ameeeen.

New Writer✍

🅿__3⃣6⃣to4⃣0⃣

Toh kwatan kwacin irin amsar daya banice yau Dana mishi tanbaya akanki, cemata yayi momi shakuwa ce kawai irin wacce ke tsakaninki da mahaifiyarta Wanda business din laceses da atamfofi yahadaku, irintace ke tsakanin dadi da Alhaji mahaifinta, Wanda kasancewar suna aiki wuri daya yasa, sannan irin sabonne dayake tsakanin Arwa da Nuruddeen, toh waima momi meyasa bakuce akwai wani abu tsakaninsu Arwa ba seni?.

Murmushi kawai momi tayi sannan tace kafin inbaka amsarka zan fara fada maka cewa irin shakuwar ce ke tsakaninku amma ku sakamakon soyayya da Kuma haduwar jini, sannan  amsarka Kuma itace su Arwa da Nuruddeen akwai kuruciya sosai in akayi la'akari da cewa Arwa ko 10 yrs batakaiba , Amma kaga kaida Rabi'atu you are all above 10.

Daka tsalle yayi waishi Sam babu wani abu tsakaninsu.

Dadai sukaga abun yaki yiwuwa se suka kyalesu.

Bayan yin maganar da watanni ne wataranar Monday da safe Yaya Aahil da Rabi'atu sukayi fada kome yahadasu oho banmantawa ranar Ina bayan mota da uniform dina ajikina mukaje kofar gidansu Rabi'a yayi tayin horn sannan megadin gidansu yafito bayan sungaisane Aahil yatanbayeshi Ina Rabi'atu yamata magana tafito sutafi aikuwa nan megadi yasheda mishi ai Rabi'a yanzunnan tafita, take yaya Aahil yajuya kan motarshi muka bi hanyar makaranta tunkafin muyi nisa da gidane muna kan titin unguwar mu irin titinnan ne da zakaji shiru se  karar motoci Abunka da Abuja kowa gudu yake zubabawa da tafka tafkan motoci.

Akai sa'a kuwa muka fara hangota tana tafiya akafa Wanda yayi dai dai da zuwan wata katuwar mota feeeewwww tawuce mu da karfi.

Innah nillahi wa innah ilaihirraji'un Rabi'aaaaaaaah!!!!!.....

Haka Yaya Aahil yadinga Mai maitawa cikin yanayin tsananin tashin hankali da rudewa me, gaggawar tsaida motar yayi waje yafita da gudu.

Nima bude kofar nayi nafito domin ganin meke faruwa?.
Ina karasawa inda naga mutane suntaru ne, na kutsa , muryar Yaya Aahil nafara ji yana fadin,  kitashi Dan Allah Rabi'a karki tafi kibarni please, kiyi hakuri kitashi , kitaimaka min kucemata Rabi'a ta tashi bazan iya Rayuwa babu itaba , kitashi nafahimci komai yanzu, kece Rayuwata zuciyata tana bugawane tare da taki inkika bari taki ta tsaya nima tawa tsayawa zatayi, karkimin haka please help me you are my everything, don't leave me hanging out in the field, all alone, my life is just a field without you, yana kuka me karfi, jijiyoyin kanshi Dana wuyanshi sun fito sunyi baro baro, ga hawaye masu kama da wutar Kira suna zuba daga idanuwan shi.

Ina karasawa wurin naga kan Rabi'a akan cinyar Yaya Aahil sanye da farin hijjabinta duk yajike da jini ko motsi batayi, daya daga cikin mutanen dake gurinne naji yana fadin yauwa ga Ambulance dinnan ma sunzo, tana karasowa yaya Aahil ya dauke ta be tsaya ma aikatan sun dakkota yayi cikin motar da ita, shima samun wuri yayi yazauna yana fadin mutafi,  kuyi sauri please kuceci Rabi'atu na itace Rayuwa ta karku bari tamutu tabarni , ahaka dai suka isa asibitin yanata sanbatu .

Nikuma anan yatafi yabarni yama manta Dani dama dayake bamuriga munyi wani nisa sosai ba, gudu nayi nakoma gida nafada masu momi da abunda ya faru, Jan hannuna momi tayi muka nufi gidansu Rabi'a muka sheda ma mamanta abunda yafaru, anan momi takira wayar Aahil tana tanbayar awani asibiti suke? Yace mata suna wani asibiti ne mafi tsada Wanda yawanci manyan masu kudi da masu mulki kezuwa, Ashe Wanda ya bigetane yakira Ambulance din asibitin, yafada ma momi sunan asibitin.

Tanimu driver ne ya kwashemu a mota dukkan mu, muka nufi asibitin.

Bayan mun isa gurinne muka tarar da Aahil yanata safa da marwa, muka karasa muka tanbayeshi Ina take, yace anshiga da ita Emergency, Kuma likitoci 4 akanta.

Guri muka samu mukayi jugum jugum, kiransu dadi momi tayi tafada musu abundaya faru bayan wasu lokutane suma suka karaso.

Shi kuwa Aahil nemanshi mukayi awurin muka rasa, Nuruddeen ne yace karku damu momi bari inje innemo shi, bayan fitan Nuruddeen yayita dubashi ko Ina Amma be ganshiba sedaga baya sannan yaduba masallacin cikin asibitin, acan ya hango shi yanata sallah tare da yin sujjada masu tsayi, dawowa. Nuruddeen yayi yafada mana cewa yana masallaci.

Allah sarki Hajiya maimunatu duk wadannan abubuwan da akeyi tana zaune Babu abunda takeyi se fadin, innah nillahi wa innah ilaihirraji'un, yaa Allah katashi kafadar yata Rabi'atu, tare da zubar da zafafan hawaye, mijinta Mesaka kuwa yana gefenta yanata faman bata hakuri tareda fadin in Sha Allah zata tashi.

Bayan lokuta masu tsawone sega likitocin da suka shiga yimata aiki sun fito, arude kowa yamike, muka nufi inda suke tare da yimusu tanbayoyi lokaci guda, amsawa sukayi da cewa dasauki ina babanta ko mijinta?, Mesakane ya nuna dadi yace gashinan, dadi Kuma yace doctor kafadama komai dukkan mu members din family dayane, to gaskiya kanta  yadan bugu,  sekuma she lost alot of blood, sannan kidney dinta yatabu gaskiya se anyimata aiki an canja domin me amfanince, sannan cikin gaggawa muke bukatar komai musamman jini munason leda2, zan bada koma me ake bukata muryar Aahil mukaji yana fadar haka tareda karasowa inda muke.

nikuma zan biya konawa ake bukata inji Wanda ya bigeta da mota, Hummm *ZulfiQar Abubakar khamis* kenan daya daga cikin yayan manyan kusoshin masu mukami a Nigeria nawancan lokacin, dagudu Aahil yazo yayi kanshi ya shakeshi tareda dawata irin Kara yana huci idanuwan shi sunkada sunyi jawur bakinshi yanata kumfa yana masifa yana fadin wallahi in har wani abu yasamu Rabi'atu Sena kasheka.

Tureshi ZulfiQar yayi da karfi Amma Ina yakasa kwatar kanshi kawai shima seya shakeshi yana fadin Kai kasan koni waye kuwa nizaka kashe?.

Kai din banza komai matsayinka Kai banza ne awurina Kuma zan iya yimaka komai indai akan Rabi'a ne, da kyar su dady da likitocin suka kwaceshi daga hannun Aahil.

Yi hakuri sir inji daya daga cikin likitocin, bakomai kabarshi kawai besanni ko waye bane shiyasa yafada yana shafa wuyanshi tareda yin wani irin murmushi me dauke da alamomin tanbaya, sannan yace doctor ka kirani kafadamin bill din, betsaya jiran abunda zece ba yajuya yafice.

Har alokacin hannun Aahil rike yake acikin na dady, yana huci.......

*Comments and share*

*SHAMSIYA ABDULLAHI (UMMU DILSHAD Mrs yahaya)*✍✍

LABARINADonde viven las historias. Descúbrelo ahora