LABARINA 21

330 15 0
                                    

*☪💗 LABARINA💗☪*

*By*
*SHAMSIYA ABDULLAHI (Mrs Yahaya)*

My social Accounts👇
FB Page *https://www.facebook.com/UmmuDilshadSmilebeauty/*

FB Account *https://www.facebook.com/shamsiya.yahaya.1*

FB group *Ummu dilshad Novels*

Instagram *@Official_ ummu _dilshad*

WatsApp *07013872581*

Wattpad *@UMMU_DILSHAD*

*OkadaApp... coming soon....*
~~~~~~~~~~~~~

*Dedicated to my fans Love you all😘😍*

*👩‍👩‍👧‍👦Muna Tare🤝 Writers Association* ✍

*✨M.W.A✨*

*Motto: we stand and fall together .*

*BISMILLAHIRRAH MANIRRA HEEM*

*Tunatarwa*

*A'uzu bikalmaatillahittaamat min sharri maakalaq*

Wannan addu'ar daya take daga cikin addu'oin mu na azkar din safe da yamma ana karantata kafa 3, koyarwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad sallallahu Alaihi Wasallam, Allah yabamu ikon aikatawa,🤲

🅿__8⃣6⃣To9⃣0⃣

Kallon da Khaleesat din tayi ma khalid din ne yasashi ya natsu Dan ayanzu matukar tsoranta yakeji ganin gabadaya ta canja kamar ba Khaleesat dinshi daya sani bace, baya son yarasata, yasani ba'a neman aure cikin aure toh Amma yazeyi tunda yayi nauyin Baki dole yayi duk wani Abu dazesa tafahimci irin tsabar son dayake Mata kozata tausaya tadawo gareshi, ganin hakanne yasa ya daure zuciyar shi yamikama Aahil din hannu tareda kakalo murmushin kafi kuka ciwo, yace wa Alaikumussalam.

Bayan sungama gaisawane Aahil ya waigo ya kalli Khaleesat yace *my Queen* Allah yakara lafiya zandawo anjima, harya juya ze fita tace *my Hero* yajuyo tace Allah ya tsare Amma Dan Allah karka bari kowa yasan banajin dadi hatta Arwa, murmushi kawai yayi yace in Sha Allah bawanda zesani ki kwanta kihuta, yajuya yafita abinshi.

Wani irin mugun kishi ne ya mamaye khalid ganin ko kunyarshi basaji agabanshi suke Kiran junansu da sunan soyayya, To Amma daya tuna yadda yake awurinta yanzu ba khalid din da bane Wanda take mugun so duk da yasan har yanzun tana sonshi tsabar rashinshine da son tanuna mai matsayin shi ada yasa yanzu take nunamai tsana karara, seya Kara kakkabe ragowar girmankai yashigo dakin cikin yanayin sanyin jiki da rarrashi, yayimata sallama ta Amsa tareda maida kanta akan fillo, kallonta yakeyi tareda marairaicewa sannan cikin yanayi na nuna tsantsar so da kulawa, sannan yace, Khaleesat, daga Kai tayi ta kalleshi da mayatattun kwayoyin idanuwan ta masu tafiya da dukkan wani karsashi najikin Wanda ke cikin yanayin shaukin so, wata irin sabuwar kaunarta yakaraji atake zuciyar shi takara bashi kwarin gwiwar cewa wannan kallon datakema Yana tabbatar da irin son datakema Wanda ayanzu nadama yakoma ganin bazata iya samun kaba, Kara narkewa yayi sannan ya daure yace yajikinki jiya bakiyi bacci bane ko shiyasa kika tashi da zazzabi? Batace Mai komaiba shiyasa yacigaba da fadin, Dan Allah kiyi hakuri ninaja Miki, kimin afuwa gawannan bawai nabiyaki bane Amma nakawo Miki ne domin inbaki hakuri, yafada tareda Miko Mata leda me dauke da kwalin sabuwar waya kallon ledar tayi sannan tace meye aciki? Yace wayace, kauda Kai tayi tareda yimishi nuni da wata leda dake kusa da ita tana fadin nagode kabarshi kawai my Hero yasiyomin dazu dayaje siyo magunguna, harda ze hasala seya tuna da shawarar da zuciyar shi tabashi, yace Ok Allah yasaka da Alkairi, limshe kyawawan idanuwan ta tayi tareda fadin Ameen, sannan tazuba mishi ido tana fadin yau meyasa bakaje aiki ba kasan dai kana da lecture yauko? Dadin tanbayar ta yaji sannan yace bazan iya zuwaba indai bakya taredani, zuba ma juna ido sukayi na Dan sakani 5 itace tafara kauda Kai.

LABARINAWhere stories live. Discover now