[1/7, 4:28 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄
*_DR SAHEEB*_
💋💋💋💋💋
By maman noorul
Hudah🌟 GORGEOUS WRITERS FORUM🌟
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my fans
_____________
🅿5⃣3⃣_5⃣4⃣
____________
Bismillahir Rahmanir Rahim
Ta kalli humaira tace"kedai a bar maganar kawai"Humaira da a sane take dibewa saheeb albarka hararan Iman tayi tace"barni in fad'a karta kashe ni"
Murmushi yake iman tayi tace"ai gaskiya ta fad'a"
Hira suka cigaba dayi fareeda tace"wai har yanzu shiru ke da Umar"
Tsaki humaira tayi tace"tuni Muka rabu cewa yayi beso inyi karatu toh ni ina zan iya shiyasa nace ya nimi wata zamanin nan da tsofofi da sufar su suna niman ilimi balle ni ai karatu tayi da a ce bakiyi karatu ba wanan d'an iskan yayi Miki iskanci Nan da daga Ina zaki fara"
Fareeda tace"kedai kin fiya fad'a"
Tace"na kaiki? ai kin fini shiyasa kika shiga abinda bana naki ba ya janyo Miki matsifa tsohon na nan hankali kwance gashi an raba ki da wanan suman larabawan"tayi kwafa fad'a take sosai babu abinda ke bata haushi sai suman da ya yanke
Tun abin na bawa Iman haushi har ya fara bata dariya kallonta kawai take,in humaira tayi shiru sai ta Kara kallon fareeda tace"wai da gaske ya aske suman?"
Tashi tayi tace"bari in Yi alwala inyi sallah"
Shiga toilet tayi tayi alwala ta fito rike da d'an kwali da tulin ribborn na a cuce maza
Kallon kanta Iman tayi tace"no wonder yanzu na gane dalilin fad'an ki ashe dai babu suman ne kamar na gemu"
Hararan ta tayi ta d'aura d'an kwalita tasa hijab
Itadai fareeda dariya takeyi
Tana idar da sallah ta d'auki Jakarta tace"ni na tafi sai na sake zuwa"
Har gate suka rakata a nan take fad'a musu tayi wani saurayi sunan sa Mahmud
Murmushi fareeda tayi tace"Allah yasa shine mijinki"
Tace"amin"
Komawa gida sukayi bayan ta samu abin hawa
Fareeda ta zauna suna hira
Mummy tace"shikenan yanzu ranan Monday Zaki fara zuwa school ko?"
Tace"eh mummy"
Mummy tace"ok asa ido a karatu"
Kallon mummy tayi tace"mummy kamar kina da damuwa ko"
Tace"me kika gani?"
Farida tace"na gan cikin kwana biyunan sai kiyi zurfi cikin tunani"
Tayi murmushi tace"stress ne"
Fareeda ta kama hanunta tace"mummy nasan kina tunanin Dr ne tunda ya tafi baki ji shi ba"
Mummy zatayi magana fareeda ta katseta da cewa"ba sai kin ce komai ba nasan ke uwace ta gari kuma na dade da gane ran ki ya b'ace akan abinda saheeb yayi kuma kin d'au alkawarin koya me hankali Amma ai ke kika haife shi dole wata rana tausayin ki na mahaifiyarshi sai yafi karfin zuciyarki but ya zakiyi? kin kasance mace Mai adalci Wanda take so kwato min yanci"
Rungumeta mummy tayi tace"nagode da fahimtar ki Amma wallahi duk randa saheeb ya dawo ni dashi ne"
Fareeda tace"nagode mummy Amma karkiyiwa d'ankin komai sabodani ni na fita harkanshi bana son ganin shi na tsan...."
Shiru tayi sakamakon kallon da mummy ke mata
Murmushi mummy tayi tace"ki fadi zuciyar ki bazan gan laifin ki ba sweetheart"
Tashi tayi cikin jin kunya tace"mummy ni zan Shiga ciki in huta"
Mummy tace"ok"
Da misalin karfe 8:pm
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/7, 4:28 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄
*_DR SAHEEB*_
💋💋💋💋💋
By maman noorul
Hudah🌟 GORGEOUS WRITERS FORUM🌟
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my fans
_____________
🅿5⃣5⃣_5⃣6⃣
_______________Bismillahir Rahmanir Rahim
Da misalin karfe 8pm
Tana kwance tana posting hotuna a Instagram da charting a watsaap sai ga Iman ta shigo da sallama
Kallonta tayi tace"ana nan dai ana ta charting"
Tace"eh wallahi"
Iman tayi murmushi cikin sigar zolaya tace"mu dai Kar ayiwa Yaya mun kishiya"
Ai sai fareeda ta hade giran sama da kasa tace"gaskiya karki kara kira sunan shi a gabana bana so"
Iman ta sauke ajiyar zuciya tace"ki zo in ji mummy kin Yi bako"
Zaro ido tayi tace"bako kuma waye?"
Tace"kije zaki ganshi"
Tashi tayi tasa hijab ta sauko
Tun tana saukowa Dr musty ya gan ta wani canja ta Kara haske da kiba fatan jikinta sai kyali yake domin yana Shan hutu
Hade rai tayi domin ta lura dashi tun a asibiti yake ta wani irin kallonta
Zama tayi a kusa da mummy tace"mummy an ce nayi bako"
Mummy tayi murmushi tace"eh mustapha ne ya zo"
Turo baki tayi cikin shagwab'a da yanzu mummy ne ta shagwab'a ta
Tace"toh mummy ni miye hadi na dashi da za a kirani wajen ki ya zo"
Mummy tace"ke bana son shashanci kaishi falon baki ki bashi abin Sha"
Tashi tayi tana kunkuni ya bi ta a baya yana murmushi
Suna shiga falon ya zauna yace"haba my faree ba gaisuwa ne?"
Turo baki tayi tace"Ina wuni"
Bata jira ya amsa ba ta bar falon ta koma ta d'auko ruwa da juice sai snack ta dawo ta ajiye ta cigaba da lasar waya
Fisge wayar yayi yace"haba Mana babu kyau wulakanta mutum ai sai saurareni ko?"
Tace"toh Ina ji"
Yace"fareeda I will go straight to the point nidai na kamu da son ki tun randa aka kawo ki asibiti na please ki bani dama in nuna Miki nawa kalar soyyaya"
Tace"a gaskiya kayi hakuri yanzu bani da ra'ayin soyayyaya makaranta zan koma"
Yace"kina nufin in baki lokaci?"
Tace"no ka nimi wata saboda Kar in b'ata maka lokaci domin zan Kai 3years kafin in fara kula wani"
Yace"ko ten years ne zan jira amma taimako d'aya Zaki min ki bani number ki"
Zatayi magana yace"please"
Tace"ok"number ta kirame yayi saving sanan sukayi sallama"
Yana wucewa ta dawo falon ta gan daddy zaune
.Murmushi tayi tace"lah Ashe ka dawo"
Yace"eh amma Ina kike na tambaya ance kinyi bako"
Tace"eh Dr mustapha ne"
Yace"me ya kawoshi"
Tace"daddy cewa yayi Yana sona zai aure ni"
Ai sai daddy ya zaro ido yace"
Maman
Noorul.hudah
Share
