*COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻
*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻_dedicated to my brother_
*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*
~~•~~•~~•~~•~~
TYPING... *WA'YA KASHE ZAHRA'U?* *#200*(My No ga masu bukatar siya 08165550116)_my wattpab_@Fateemah0
_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘
____________________
_Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*____________________________________*
*page°°°°15&16*
Basu zarce ko ina ba sai gidan Anty Ummu, sallama suka yi, Anty Ummu ta fito da sauri daga kitchen sakamakon jin murya ɗan uwa gudan jiki.
Tana ganinsa kuwa annurin fuskarta ta ƙaru, shi ma Ubaidullah dariya yake yi wanda har ya bayyana hakwaransa.
Hannu Anty Ummu ta miƙa masa cike da murna, tana cewa.
"Ɗan uwa kai ne ko kuma dai idona ne yake min gizo?"
Cike da zolaya Zaidu ya ce.
"Anty Ummu abu daya zai sa ki tantance ko shi ne, ko ba shi ba ne, bari na miƙo miki wancan tabaryar, ki shemesa da ita daga nan za ki gane gaskiyar tambayarki."Anty Ummu ta kwashe da dariya, ta ce.
"Daga haka ma na tabbatar ƙanne na ne a gabana ku shigo daga ciki."Su na shiga Anty Ummu ta cike musu gabansu da kayan ciye-ciye da shaye-shaye,sai nan nan take yi dasu.
Sai da ta tabbatar basu buƙatar wani abu tukunna tazo ta zauna kusa da kaninta suka gaisheta ta amsa,su na hira su na dariya.
Anty Ummu ta ce.
"Amma dai ina fatan bana zaku kwana biyu kafin ku koma ko?"Zaidu ya ce.
"Ina kuwa jimawa Anty babba, wallahi 5days General Of Army ya bamu dan kwanan nan zamu tafi bakin bordern nijar domin kamo wasu y'an ta'adda.""Oh Allah ni Ummu kenan yanzu shikenan ku haka rayuwarku zata ƙara a fagen da ga?"
Sai yanzu Ubaidullah ya bude baki yayi magana.
"To big sister ya zamu yi ai ya zama dole tun da munyi alƙawari tare da rantsuwar gare kasarmu ta gado wato nigeria, gashi mune jami'ai wanda aka fi ji dasu bana gaya miki a waya an yi mana ƙarin girma ba, to ai yanzu kam bamu ga wani hutu ko zama waje daya ba, kawai ku dinga tayamu da addua."
Anty Ummu ta numfasa ta shaƙi iska, sai ga hawaye yana zuba daga idonta wanda yayi sanadiyyar hankalin Ubaidullah tashi nan ya shiga jero mata tambayoyi ba ƙaƙƙautawa.
Girgiza kai Anty Ummu tayi ta ce.
"Ba komai dan uwa ka kwantar da hankalinka,Allah ya taimake ku Allah yasa ku gama da duniya lafiya,Allah ya ƙare ku da ga sharrin masu sharri."

ESTÁS LEYENDO
COLONEL UBAIDULLAH
Chick-Litlabari ne akan wani saurayin Soja akwai (tausayi soyayya cakwakiya hassada munafurci kar dai na ciku) kudai ku bibiye labarin