_______________________
_*MINENE MATSAYINA...*_© _Hafssatu Musa_
*Indon K'auye*_*NO...35*_
_*Maijidda &Mairo ta Ado thank u inayinku inajindadin Comment dinku*💕_
Murnar da farin cikin da suka shiga baya misiltuwa Aliyu Sauqar Al'aqur'ani yasa aka dinga yi da rabon Abinci da kujerun hajji yana godiya da Allah da wannan kyautar dayayi mishi wadda babu wadda ya isa yayi mishi ita sai shi,Gwagoo sai gashi takara nadama ta kuma jawo Fatyma jikin ta ta roki ta yafe Mata duk wani Abu datayi mata,Fatyma cema gwagoo tayi ''Gwagoo kidaina fad'in hakan don Allah Kefa a matsayin mahaifiya nake kallon ki a hakan Ku ma nadauke Ki a cikin zuciya ta." Gwagoo k'ara kaunar Fatyma taji Cikin ranta dama can bata tsane ta ba domin Fatyma kullum cikin yimata biyaya take da kyautata Mata kawai rashin haihuwar da batayi ne,
Kulawa ta Mussaman Fatyma take matuqar samu daga Aliyu gwagoo harta Abdul ba'a barshi baya komai yasamu zai ba Fatyma ''Umma kiba Baby,..Umma ki Ajema Baby Umma na yaushe zanga Baby inason ganin sa Amjad yana brother &sister nibani dashi Umma"
Fatyma shafa kanshi tayi ''Zan haifa sister ko Brother kanaso dai zaka kula dasu kau." Sosaima Umma na bazan duke su ba bazan bari suyi kuka zansa su ta dariya sai inji Dadi"..Umma shafa kan Abdul tayi tanajin wata k'aunar Yaron ta na shigar ta "Abdullahi Allah yayi maka Albarka ya jikan Aunty jamila..
💫💫💫💫💫
Akwana Atashi Fatima tana ta rainon cikin ta wadda yazama tamkar tsoka d'aya A miya kowa tarairayar ta yake da bata cikakikayar kulawa Gwagoo House girl's 2 ta dauko suna kula da lafiyar Fatyma kawai sai doctor daya da nurse da koyaya Fatyma taji ciwo yanzu sunfara duba lafiyar Abinda ke cikinta ya fawwaz kullum cikin bugowa waya yake tambayar lafiyar bayan zuwan da yayi sau 2 Nigeria.. Inda ya roki Aliyu yabashi Fatyma ta haihu kusa dashi Aliyu Murza ma idon shi toka yayi yaba yah Fawwaz hakuri Akan shima yana son ganin Fatyma a kusadashi..Ya fawwaz baiji komai domin yasan Aliyu ya na matuqar kula da tilon k'an war shi fiye da tunanin shi...
Cikin Fatima ya tsufa inda kulawar takara yawa akanta inda yanzu motsa jikinta kawai take wadda doctor yace ta d'an dinga motsa jikin ta ko yayane Amma ko cokali gwagoo ta hana ta d'auke gwagoo da kanta take ma Fatima girkin duk Abinda takeso...Wani dare ne nakuda takama Fatima dama tuni gwagoo tadawo gidan part 1 inda ta maida Fatima d'akin gado daya suke kwana.. gwago tashi tayi ta tado Aliyu Suka nufi wata Private hospital wadda sai kusoshin gwammanti da yan kasuwar da suka shahara suke zuwa kwararin Likitoci ne Akwai Turawa indiyawa larabawa harda bakaken fatar, Nanda nan Aka karbi Fatyma aka shiga da ita Labour Room Aliyu da Gwagoo sai zarya suke suna Add'uar Allah yasaukeki Fatyma lafiya, can kimanin kamar 1 hour saiga wani doctor yafito dasauri gwagoo da Aliyu suka nufeshi ''yadai Doctor?'' Doctor Kafad'ar Aliyu ya taba Congratulations My Friend Madam tasauka lafiya tasamu Baby girl itada Baby suna cikin koshin Lafiya Aliyu hango Famfo yayi can gefe Ablution yayi ya shiga masallacin dake gefen sa yayi Nafila raka'a biyu d'aga hannu yayi kukan farin ciki ya fashe dashi yana kirari ga Ubangiji tahalikkai..*After 2 Hour's*
Duk wata Add'ua da ake ma jinjiri yaro Aliyu ya tofe d'iyar shi dasu yabata dabino da ruwan zamzam
Rungume yake da baby girl din da ya kura mata idanuwa wadda tuni an nad'eta cikin tawul blue da kayan ta na sanyi blue sai bacci take Doctors sai yabon kyawun Baby girl d'in suke saboda tsananin kyawunta lol dole tahada kyawu tahada jinin larabawa da jinin Fulani.Gwagoo ce ta turo kyauren d'akin taga Aliyu rungume da Baby girl baima San shigowar ta Fatyma bacci take, samun kujera tayi ta zauna gyara murya tayi ''Gwagoo yaushe Kika shigo?" ''Haidar yaxa'ayi kasan nashigo dama"
Murmushi yayi tare da sunkuyar dakai kawai....*Washe Gari*
Fatyma takara warwarewa Ankara dubata batada wani problem itada Babyn ta akabasu sallama suka tafo gida Abdul tunda ya kyalla ido yaga Baby hannun Umman sa dasauri ya nufe ta ''umma na yaushe Baby yazo baki Fadamin ba" Afuwan Yaron Umma kana bacci ne shiyasa ban tasheka ga sister d'inka"..Umma d'ora mashi Babyn tayi a jikin sa kura babyn kallo yayi "Umma na sister nada kyawu inasonta sosai.sumbatar Fuskar babyn yakara riketa kamar za'a kwace mishi ita, yan unguwa da suka Fara shigowa saidai su ganta hannun Abdul ya hana kowa ya d'auke ta daga jikinsa shima yaki matsawa ko nan da nan yana rungume da ita
💫💫💫💫💫💫💫
Fadar irin shagalin da akayi ranan suna bata baki ne Anyi shagali iya shagali inda Jaririya taci Sunan Gwagoo wato Bilkisu Amma xa'a dinga.Kiranta da *AMAL* Ya fawwaz yazo dawasu daga cikin danginsu ya fawwaz mabukata yasa aka Tara mishi ya dinga musu kyauta Mai tsoka wadda basu da jari ya basu jarin da zai ishe su sana'ar da basufi karfin cida sha ba, gidan marayu haka yaje ya kaimusu kayan masurufi,da kayan Abinci..
_Da yawa sunce nacika saka indai za'ayi kyauta nakan saka mabukata da kuma marayu Burina kenan A rayuwa in har Allah ya azurtani a rayuwa na kyautata marayu fiye da wadda suke da iyaye nazama uwar Marayu nayi kyauta ga mabukata..na kyautata ma matasa mararsa aikin yi Allah kacikamin buri na Ameen ...._
∆∆∆∆¶¶¶¶
*AFTER 8 MONTHS*
Gabaki d'aya rainon Amal yadawo hannun Abdul A kullum yana tare da ita babu Abinda ke rabashi da ita makaranta komai kuma yaci akwai na Amal sai yakawo mata inbata lafiya kuka yake har ya kwanta jinya shima In Kashi Amal tayi baijin kyankyami haka zai wanke kayan kashin datayi in Amai tayi baiji komai haka zai d'auraye kayan wata irin shakuwa ce tsakanin Amal da Abdul inda itama data ganshi zata Fara zillo da dariya farin ciki umma kuwa itada Abba tuni sun hasasho wani Abu a ransu haka itama gwagoo dayanzu tadawo gidan baki daya saboda Amal da Abdul tace domin yanzu bakaramin kaunar Abdul take ba tadaukeshi daya da Amal..kulawa da tsananin kauna take nuna musu,
Abdul duk ma'aikatan dake gidan ba yarda kowa yayima Amal wankin kayanta shike wanke Mata su Tas ya goge kuma masu karatu duk wani Abu da kukasan uwa nayi ma yarta Abdul shikema Amal shan nono kawai ke had'ata da Umma....
_*AFTER EIGHT YEARS*_
# Follow me on wattapad
@Hafssatu
#Vote
#Comment
#Share

YOU ARE READING
MENENE MATSAYINA...
Mystery / Thriller"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin ki ya gayamiki nafada miki banza..." Fuskar jike da hawaye ta d'ago ta kalleshi cikin kyarmar murya t...