EPISODE 3

277 6 0
                                    

*🤫💔🤫SENA AURI MIJIN ƳATA, (TA CIKINA)🤫💔🤫*

          By

*Ummu dilshad*

*Wattpad_@ummudilshad*

*Facebook_Shamsiya Abdullahi*

*Email_@ ummudilshadauthour30@gmail.com*

*Instagram_@Officialummudilshad*

*Watsapp_07013872581*

*INTELLIGENT WRITERS ASSOCIATION®️✍️*
     (Onward together)

👆Wannan book din daga farko har karshe sadaukarwa ne ga ilahirin Yan kungiyarmu, Ina alfahari daku gabadaya, musamman *My*(Janafty).....sannan *boss* (mom afra) tamu gabadaya muna kaunarki Kuma muna alfahari da ruling dinki agaremu kedin shugabace ta kwarai, bazan manta dakeba *magatakarda*(ZM chubado), tareda sauran members din gabadaya harzuwa kaina, bazan iya lissafoku dukaba saboda innace zan lissafoku kuma infadi irin kyawawan halayyarku, to kuwa bazan taba samun damar rubuta wannan novel dinba gabadaya sedai tundaga page 1 harzuwa karshe zan Kai Ina fado irin Alkairanku Kuma Basu kareba, sakamakon dunbin yawan da suke dashi. Ina godiya mara adadi, Allah yabarmu tare *Son So fisabilillahi*😍😘🥰.

Dedicated to,  *My Zeenat* (ummu Abdul & Islam) uwa ta gari kedin ta dabance a Raina.
zainab Muhammad *(Zee Musty)*. Jinjinar ban girma zuwa ga Ummu Suhaanar. Uwani Koko kema fa banmanta dakeba, dama sauran Yan group din UMMU DILSHAD NOVELS na watsapp, duk inajin dadin addu'oin da kukema Islam, Alhamdulillah tanata samun sauki. Ina GODIYA Sosai.

*BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

                   🤫_3

Hajiya Rahmatu tana shiga Fallon ta taras Babu kowa, se tashin kamshin Abinci dake Kara karade gidan, sannan Dan madaidaicin TV dake makale a jikin bangon fallon yanata magana.

Ganin haka yasa takara tabbatar wa da cewa akwai mutum a cikin gidan Dan Haka kawai seta samu guri ta zauna, kanta Yana matukar sarawa jitake kamar kanta ze cire, wani irin tukukin takaici na jin haushin mahaifinta Malam Haruna Yana Kara mamaye Mata zuciya, hawayen masu zafi suka Fara zuba daga idanuwan ta, a inda ta Fara yima kanta tanbayoyin da Basu da amsa acikin ranta tana fadin, _menayima *Abba* ne dayasa kwata kwata tun Ina karama baya kaunata? Gashi yanzu yajawo  itama *Umma* ta biyemai, meyasa arayuwa mutane inkayi me kyau ba'a tankawa sekayi akasin Haka sekaji ancika gari da zancenkane? Meyasa mutane basa iyayin temako alokacin da kake bukatar hakan? Meyasa bil'adama ke saurin yanke hukunci akan abunda Basu tanbayi dalilin faruwarsa ba? Meyasa mutane basa yin uzuri akan abubuwa ko halayyar mutane ne? Tanbaya ta karshe meyasa bazaku tsaya ku saurareni, ko ku tanbayeni dalilin son Auren mijin yata Hajara ba????????

Momy.......!!!!!!!!!!!

Na'am! Cikin yanayin razana ta dago kanta da sauri tana kallon Wata kyakkyawar matashiyar yarinya da bazata wuce shekaru 16, wacce ta Dade a tsaye tana fadin Momy... Yafi a kirga harseda ta gaji da Kiran ta tabata sannan ta dago. Momy Lafiya naketa kiranki kin sunkuyar dakai Baki amsaba, Kuma Lafiya naga kina hawaye meke damunki momy? Se alokacin Hajiya Rahmatu ta lura da Sanyin hawayen dake gudu akan kumatun ta, da sauri ta goge tareda fadin Babu komai *Habiba*, Ina *Habib* da *Amira*. A takaice Habiba ta amsa Mata da *suntafi Hadda*, Nima dama inata saurine insamu ingama girkin Nan inkaima *Anty Hajara* asibiti kinsan jiya tace tanaso in dafa Mata fryied rice da kunun Aya da soyayyan Naman rago, to gurinneman namanne na Dade Dan kusan duk masu danyan Naman shanu suka yanka, Amma yanzu na gama zan wuce in Mika Mata,  in 4:00 tayi se inwuce Islamiyya Dan yau zamu fara jarabawa, momy su *Kaka* Kika Bari acan tareda ita Hala?.

Ganin Momyn tasu Bata kulatabane se aikin zubda sabon hawaye da taketa famaryi ne yasa Habiba tsagaitawa da dogon surutun dataketayi tareda tsugunawa agaban momyn tasu tana fadin Momy Wai Dan Allah meke damunkine? Tunda Kika shigo kiketa zubda hawaye? Meke faruwa ne kodai jikin na Anty Hajara ne yayi Kara zafi?

🤫SAINA AURI MIJIN 'YATA (TA CIKINA)🤫Kde žijí příběhy. Začni objevovat