35

1.2K 65 1
                                    


*ᎻᏌᎷᎪᏆᎠᎪᎻ*
(ᴛʜᴇ ᴄʜᴀʀᴍɪɴɢ ʟᴀᴅʏ)

           *ᎪYᏚᎻᎪᎡᎢᎾᏌ*
                ωαттρα∂ @neeshejay

_Dedιcaтed tσ_

*H͙  u͙ m͙ a͙ i͙ d͙ a͙ h͙*
(υммυ fυ'α∂)

*ⓟⓐⓡⓣ 176_180*

Pictures din ta da yawa Asiya ta turawa king sosae ya yaba da kwalliyar amaryarsa ji yake inama yaune za'a Kae masa ita gaba daya ya matsu yaji sa a kusa da gimbiyarsa.

Gaba daya ta gaji sosae hakan yasa ana gama event ta shige daki ta cire kayant tareda shiga toilet ta watsa ruwa ko zataji dadin jikinta koda ta fito ta tarar da gaba daya yan uwanta da sun shigo dan ita bata da frnds ko daya sae dae cousins dinta. Suma sae faman cire Kaya suke nan suka fara wanka wadan da Kuma ba dakin suke kwana ba suka wuce dakinsu, itama bata jima ba ta wuce warta dakin Ammi Dan yanzu a Chan take kwana, wani Dan karamin hard cover Mae masifar pink colour Kuma yanada Dan karamin padlock Shima Mae  kyau ta dauka, koda ta shiga ammi Bata dakin sanin Abba ya dawo ne yasa tayi kwanciyarta amma gaba daya ta kasa bacci hakan yasa ta mike take dakinsu ta Kira Asiya ta tayata kwana tunda Ammi Bata nan,bayan sun dawo dakin ne Kiran king a ya Mata ya gajiya nan suka shiga fira har dare ya raba Shima dakyar suka rabu,

Bata kwanta ba sbd ganin karfe 3:19am hakan yasa ta mike ta shiga toilet ta dauro alwala sallah tayi tareda addu'a sosae kafin ta kwanta ba jimawa aka Kira sallahr asuba.

Bayan sunyi sallah ta koma ta kwanta sae kusan 10 ta farka ko da ta tashi ba kowa a dakin wanka tayi ta fito ta shirya cikin doguwar rigar material, Aunty Suwaiba ce ta shigo hannunta dauke da wani cup nan da nan annurin fuskar Humaidah ya dauke Dan tasan abunda Bata so ne aka so Bata ganin haka yasa aunty Suwaiba tamke fuska ta Mika Mata ba Wasa ta karba ta shaye tana yatsinar fuska Kamar zatayi kuka. Bata kulata ba ta karbi cup din ta fita abunta itama fita tayi a parlour ta tararda dukansu dining ta wuce sae da ta dibo breakfast dinta kana ta koma parlour ta zauna.

Bayan ta gama suka fita gaba dayansu sae gdan mama Dan a chan ne zaayi lalle Basu jima da isa ba aka fara Dan already Mae lalle tazo har an ma wasu  amarya aka fara tsantsarwa lallae Mae kyau ja da baki yayi kyau sosae sae kusan 3 ta wanke tana cikin dakin ammi ta gama sallah ta mike kafarta tana lazimi ya shigo wani irin murmushi ya Mata Mae narkar da zuciya itama mayar masa tayi kana ya karasa shigo dakin bakin gado ya zauna Yana karema kafarta kallo sosae lallin ya masa kyau danshi mutum me Mae son shi. Ganin kallon da yake matane yasa tayi saurin boye kafarta tana smiling Shima dariya yayi yace"heartbeat rowa ko"

Dariya tayi tace"ni na isa mama mamallakin lallen rowa ne"

Yace"idan haka ne to meyesa kika boye kafar"

Cikin shagwaba tace"ba yanzu ya kamata ga gani ba" ta karasa da turo baki

Wani abu yaji tundaga kasan kafarsa har cikin kansa cikin ransa yace"ya ilahi da ace an daura Mana aure ba abunda zaesa nayi kissing dinta"

A fili  kuwa yace"baby you are killing me" da sauri ta mike zata fice yayi saurin kamo hannunta sae kawae tayi kasa da kanta kafin ya bude baki yayi mgn sae ga ammi da mama sun shigo ae da sauri mama ta koma ganin wannan ta'asar ammi kuwa rike baki tayi tana sallallami Humaidah da kunya ta rufeta tayi saurin ficewa waje da gudu.

Ammi ta kalli king tace"toh Mara kunya uban yan azarbabi zoka wuce ka bani guri shine zaka saka yarinya a gaba kana koya Mata rashin kunya Anya kuwa Taufeeq"

Sosa bayan kansa yayi yace"Kae ammi mutum da matarsa"

Ammi ta rike baki tace"yaushe aka daura auren ban sani ba"

HUMAIDAHWhere stories live. Discover now