Broken

251 12 1
                                    

A Take parlour ya wani dauki shiru saboda tsananin firgitan da ya nuna qarara a fuskar Neena, Armaan da Amaan. Dan ko kusa ba wanda yayi expecting jin anything like that. Neena tsanin tsoro ne da firgita ya nuna a fuskarta.
In Amaan yayi mutuwar zaune kwakwalwar sa na bashi ko dai Amaan akace shine baiji ba sosai, sai dai kallon shock din daya gani a fuskar Armaan yasa yasan cewa yaji daidai.
Duk yanda Armaan yakai da iya boye abu sai da fuskarshi ta nuna shock hade da confusion na what the hell is going on here!
Naziha kanta ji tayi kamar an watsa mata tuwan qanqara.

Dakyar Armaan ya tattara wani dacecen yawu abakinshi ya daure ya daga baki zai magana babanshi ya rigashi.
Inda baban shi ya fara da cewan "Wannan ba wani bane Abbu, daman tunda kayimin maganar na wakilta Bukar da Madu sunje sun mana tambaya kuma Alhaji Kabeer ya aminta ya bamu"
Ashe zuwa tambaya da akai ba na Amaan bane na Armaan ne, rashin maganar ne yasa Neena batasan details ba saboda Dr Mustapha yace amman kar awa yaran magana dan Grandpa yace shi da kansu yake son musu magana. (Toh fa!)

Alhaji kabeer na ya dora dacewan "ai baffa ba alfarma bane wannan yaran zasuyi maka umarni ce zasu bi da mukanmu gaba daya, dan wannan hadin da kayi yafi mana komai dadi"

Grandpa yayi murmushi ya amsa da "ahamdulillah tohm Allah ya raya muku iyalanku yayi muku albarka gaba daya" kowa ya amsa da ameen banda mutum 3 da sam hankalinsu bai kan maganar.

Grandpa ya fuskance akwai matsala amman ya share sanin cewar daman can da rashin jituwa tsakanin favorites din nashi tun zuwan Neena US.
Iyayen su maza kuma sun dauka kunya ce kawai ta hanasu magana. Inda mahaifiyar Neena kallo daya ta mata tasan yar ta na cikin tashin hankali amman batayi magana ba dan bama ta isa ta fara ja da maganar mahaifinta ba.

Haka dai aka gama tattaunawa aka tashi kowa jiki a mace saboda maganar ciwon Grandpa.
Kafin a tashi Grandpa ya sanar da ya bawa Neena da Armaan 2weeks su fahimci juna dan so ya ke ayi biki ya koma tare da matar shi bakin aikin sa.
Inda ya sanar da iyayen maza dasu fara shirin abinda suke ga its necessary ayi komai in 2weeks ba sai an tada wani gaggarimin biki ba.

Da wannan aka fufe taro aka tashi inda Amaan baima san sauran maganar da akai ba dan tunda akace za a sa biki nan da 2weeks yadaina jin me suke fada.
Neena ma haka ta tashi idonta na dusu dusu bata ganin gaban sosai saboda tsabar damuwa, Nazifa ce ta fuskanci halinda take ciki tayi saurin tashi ta kamo ta su ka wuce sama dakin da suke sauka a nan gidan Grandpa da Garki zone 2.

Shigansu dakin ke da wuya Neena ta fada gado ta fara wani irin kuka maicin rai, Naziha ta kamota ta rungume itama kukan kawai take takasa rarrashinta.

Saida Neena ta dauki almost 30 minutes a haka kafin tafara iya magana cikin shesheqa take cewa "Why? Why me?? Wat did i do to deserve this?" Naziha kallonta kawai take na hawaye ita ma
Neena ta qara da cewar "out of everyone a rasa wa za'a hadani dashi sai wancan mugun" Naziha na shaking head dinta amman bata kai ga magana ba Neena ta cigaba da "banason shi naziha bana kaunar shi, bakuma zan taba kaunarshi ba wallah, sai dai in a kasheni amman ko an hanani auren Amaan bazan taba yarda na auri Armaan ba" tana kaiwa nan daidai da bude kofar dakin da yaja hankalinsu duka suka juya.
Hajia fatima (mahaifiyar Neena) suka gani ranta abace tayi saurin qaraso cikin dakin tayi banging kofar ya rufe.
Ta fara magana "ashe daman baki da hankali? Wani maganar banza naji kinayi haka"
Neena tayi saurin miqe ta na matso kusa da mahaifiyarta idonta na zuba da hawaye tafar pleading tana cewa " Anne pls karkusa na aure shi, wallahi bana sonshi. Amaan nake"
Hajia fatima ta ware idanu tace "kinason kicemin maganar Baffa zaki tsallake kibi son ranki?"
Neena tace "Anne zan auri Amaan ai duk daya ne shida Armaan din wajen Baffa"
Hajiya fatima tace " in kinsan dayane sai ki rufe bakin ki auri zabinshi, dan ma baki da tacewa magana ta qare aure ne babu fashi ke da armaan kamar anyi angama ne"
Nan da nan Neena ta qara rudewa batasan sanda ta fara daga murya ba tana cewan "Allah bazan aure shi ba Anne bana son shi! Baku ma zan taba son shi ba ko... "
Neena bata kai ga qarasawa ba taji saukar mari a kumatunta da yasa ta rufe bakin ta ba shiri Hajia fatima tace " in mutuwa zakiyi saboda kiyayyarsa sai dai ki mutu amman aure anyi an gama, mara kunyar banza, har wani isa gareki da zaki ja maganar Baffa?" Taqara da cewa "shi Armaan din ai shi ya kamata yayi bori bake ba, sai ke da kikafi kowa baki da rashin kunya" tace "toh wallahi in har ni na haifeki neena karki sake kibar maganar rashin son auren nan ya bar dakin nan dan in har kika bata abin nan sai dai ki nemi wata uwar bani ba" Hajiya fatima na kaiwa nan tayi waje da buga kofa.
Take Neena ta zube qasa wani sabon ya fara zuba mata dan ana ta rayuwarta ta qare kawai.
Naziha dake gefe a tsorace da ganin hajia fatima da jin furucocin bakinta tayi saurin qarasawa wajen Neena ta rungumo ta tana hawaye ita ma.

A bangaren Amaan kuwa yana fita bai tsaya a gidan ba yayi waje yaja motar sa gudu yake sosai Allah ne kawai ya tsareshi dan baisan inda hankalinshi yake ba ma, ba tsaya ko inaba sai gidan su (shida Armaan) da yake maitama.
Gidan qaton gaske ne Abbansu ya gina musu shi da armaan, kowa da section dinshi. Qayatacen gida mai kyau da wadata, har da Garden da Gym da swimming pool. Very comfortable house dai.

Yana zuwa tun kan yaqarasa yadanna remote gate ya bude ya shiga a kuje kamar zaibi ta kan gardener dinsu dake watering carpet grass din gidan.
Da shiganshi yafita daga motar a parking kawai yasa giyar motar ya fita ko kashe ta baiba ya shige side dinshi. Sai driver dinshi ne da yaga shigowar shi yazo da gudu ya ja motar ya kaita yayi parking.

Amaan na shiga wayar shi ta fara ringing yana ciro ta daga pocket bai ko duba screen din yaga wake kira ba ya hada wayar da Tv din dake jikin wall, qarar glass kawai kakeji alamar fashewa, iya karfin shi yasa hannu yafara watsi da duk wani decors dake leaving room din nan na qasa.
Before you know leaving room din kacame da fassasun glasses. And shima ya yanke har waje 4 a hannunshi ba tare da ya damuba ya fadi anan ya fara kuka maicin rai zuciyar shi cike da quna kamar zata tarwatse.

QANGIN SODove le storie prendono vita. Scoprilo ora