Shimfiɗa

1.1K 128 20
                                    

Assalamu Alaikum wa Rahamatullah ta'ala wa barkatuhu 'Yan uwa Maza da Mata.

Ƙyan tafiya aka ce dawowa.

Da fatan mun sake saduwa a cikin Alkhairi ? Saƙon gaisuwa a gare ku masoyan rubutuna.

Kamar yadda na Alƙawarta a ƙarshen littafina na baya cewa ina nan dawowa tare da sabon littafina to ga ni fa na dawo in sha Allahu littafin Aƙida linzami zai fara zo muku nan ba da daɗewa ba ku dai kawai ku yi zaman shiri irin na mai sauraro 😀

—————————————————–

Aƙida Linzami hakane??  Ko ba haka  ba ne ??

Aƙida kan iya zama linzami akan tafarki na Rayuwar Ɗan Adam

Aƙida kan iya zama linzami da zai ja kansa da kansa har yayi jagora a fagen tafiyar rayuwar Ɗan Adam .

Ba koyaushe Ɗan Adam yake da zaɓi ba akan aƙidarsa , a hankali aƙida take sanɗar Ɗan Adam har ta shiga ta saje da halayyarsa da kafin ya farga ta yi masa rumfar da ba shi da zaɓi wajen irin yanayin da zata iya zo masa da shi .

Amma me zai faru a lokacin da aƙidar ta zurfafa har ta kai mai ita ga makancewa daga ganin zuzzurfan ramin da ya mamaye kan tafarkin aƙidarsa ?? Ya kuma gaza wajen riƙo linzaminsa maimakon haka sai ya sakar ma ta linzami har ta kai maƙuryar ƙurewar da ta birkice ta jirkita ta rikiɗe ta koma mummunar akiɗar da ta zama guba sannan kuma annoba acikin al'umma sannan ta jefa mai ita a hallaka mafi munin ji da gani .

Anya Salman bai yi fargar daji ba ? Lokacin da ya farga ya fara yunƙurin riƙo linzamin aƙiɗarsa ya dawo da ita bisa kyakkyawan tafarkin da ainahi ya gina ta a kai , a kuma dai-dai lokacin ne zuciyarsa tayi masa tirjiya ta jaa ta toge sakamakon aƙidarsa da tayi arangama da wata aƙidar da take mabambanciya da ta shi .

So kuma yayi tasiri irin nasa ta hanyar sarƙe tsakanin aƙidun biyu da suke kishiyoyin juna ba tare da ya lura da tazarar da ke tsakanin su ba .

Sannan a ƙarshe zuciyoyinsu su ka zaɓi da suyi watsi da tasirin aƙidunsu su rungumi junan su a tsakiyar bigiren da ko cikin shuɗaɗɗun mafarkai irin na baccin tsakiyar hunturu , ɗayan su bai taɓa tsintar kansa a ciki ba sai ga rayuwa ta juya musu aƙida kuma ta musu jagora .

Shin wai gaske ne aƙidarka linzaminka ???

Sahihiyar amsar ta na ga Salman tare da Madina .

Umm'muaz

AKIDA LINZAMI Where stories live. Discover now