*A DUNIYARMU*
Written by (mrs bb)38.
Ban idasa zubewa k'asaba naji anyi sama dani cikin sauri mun shiga cikin gidan,AJ ne ya daukoni kaina ke juyawa ina ganinsu biyu biyu,kallona ya tsaya kan yah harun idona tuni ya fara anbaliyar ruwan hawaye......bansan sadda na fashe da kukaba kuka nake sosai mai tsuma zuciya,duk sunyi cirko cirko hajiya ce tafito tace"aaaha Hanan lafiya,Bilal me yafaru kukan me kike."
Zama tai kusadani tana bubbuga bayana"daku nake kunyi shiru."
Harun ne yaduka yana gaidata ta kallai"bawan Allah daga ina."
AJ ne yace yayanta ne d'an wajen Alhaji kabir kanen mahaifinta,tun sati biyu ya wuce yake zuwa nemana office bana zaune,yazo har sau uku bai sameni ba karshe nace abashi no dina ya nemeni,sai yau muka had'u.
Yayi man bayani sosai akan wad'anan azzaluman,yanzu dai munada kwararan shaidu wanda zama guda a kotu zaa warware komi."
Ajiyar zuciya hajiya tayi tace"to kukan datake namenen."
D'aga kafad'a yayi yace"ina zan sani kawai dai tana tuna rabonta dashi da kuma musabbabin abunda ya rabata dashi,that's why."
Lallashina hajiya keyi sosai inata shashsheka da ajiyar zuciya,
Sannan ta kira Amnah tace takaiwa bak'o abun tab'awa falon bak'i Bilal ne yayi mashi iso har can,don ban san sadda AJ yabar falonba.......hajiya tace inje can muyi magana haka natashi jikina babu kwari nanufi falo,yana zaune ya dafe kai nai sallama dasauri ya dago kanshi yana kallona,zama nai kujerar dake nesa dashi.
Tasowa yyi yazauna gabana k'asa idonshi akaina,jinai wani kukan zai kucceman yayi saurin girgiza man kanshi,
"Karkiyi inhar baso kike natai ba to kibar kukan haka,i wonder ma kike kuka Hanan,bacin nasan waccen Hanan din tawa jarumace mai dakakkar zuciya,bakomi ne yake sata kuka ba bata damuwa da abu inhar ba itace tasa kantaba plss stop this baimaki kyau."Hawaye suka zubo man nace"yah waccen hanan din tasha banban da wanan,ita wannan zuciyarta tariga tayi rauni,rauni ma kuwa ba na wasa ba tariga da ta zama marar dauriya bata iya jure damuwa koyatake,abu kalilan zai sata zubar da kwallah.
Yah rayuwata ta canza canzawa kuma ba yar karamaba,duk saboda dalilin iyayena iyayen da banda kamarsu duk duniya,sune sukai ruwa sukai tsaki cikin rayuwata,sukai nasarar wargaza komi.......hawaye keta sharara harna gaji da sharewa.
Sadda kanshi yayi yana jin duk duniya babu wanda yakejin kamar yakashe irin mahaifinsa da musa,meyasa ne abubuwan sukazo ahaka meyasa meyasa.Shiru mukai kowa da irin tunanin da yakeyi,kafin yace man ya bayan rabuwa.
Ganin zan mashi kuka yace to baiso tunda bazan dainaba,dole na aro jarumta nashiga bashi labarin abubuwan dasuka faru.
Duk ya firgice idonshi yayi jaa kamar jinja,jijiyar kanshi tafito saboda tsananin b'acin rai,jinjina kai kurun yake yana taune lebenshi na ka'sa.
Kafin daker yad'ago yana kallona cikin muryrasa kamar zai fashe da kuka yace,
"Hanan kinsan nayi aure."Tsananin yadda maganar ta shigeni saida na dafe kaina,jinake kamar ana buga man guduma sakaman kaina,idona yadaina zubar da hawaye saidai zuciyata ke zafi.
Muryata ta dishe sosai nace"wa ka aura."
Runtse idonshi yayi kana yace"kawarki *hibbah*"Silalowa nayi daga kan kujerar na duke kaina cikin guiyawuna,wani irin numfashi nake saukewa,duk yadda na keson nayi kukan abun ya faska ra,wani fitinennen zafi nakeji yana fitowa daga cikina..........nafi minty talatin haka karshe na rushe da kukana.....bai hananiba don inajin shima shi yake,kuka nake kamar yaune akace su mami sun rasu,jinake duk wata damuwata tatsawon shekara hudu tana dawoman.........saida naji numfashina yana niyyar barina sannan na hakura nai shiru.
Batare daya saurareni ba yafara bani labarin abubuwan dasuka faru bayan barowata gidan,tiryan tiryan har kan abunda dadynshi ya gaya mashi labarin rayuwarsu shida maihaifin hanan.
Anan yake cewa akwai plan din da sukai shida AJ insha Allah sanda za,ai shariar ma bazaki saniba insha Allah kinyi bankwana da duk wani kunci da bak'in ciki,donhaka ki kwantar da hankalinki komi ya k'are."
Kalamai masu kwantar da hankali yashiga gaya man tare da nuna man har gobe yana nan da soyayyata,bai tafi bah sai wajen karfe goma nadare kamar inbishi inga dady don labarin daya ban duk tausayin sa ya kamani,bakamar jin yadda yake kwance jikin yak'i dadi.
Mrs bb ce👌🏻

YOU ARE READING
A DUNIYAR MU
Fanfictionlabari mai d'auke da abubuwa da dama cin amana, son zuciya, zalinci,sannan da abubuwan da suke faruwa a wannan duniyar Tamu,cin hancin da Tashawa,danne Hakkin maraya, daidai sauransu sai Wata kalar Soyayya mai rikitar da zukata Duk acikin wannan li...