*A DUNIYARMU*
Writing by mrs bb.42.
Bin bayansa nai da kallo,ina sake da bakina kallon kaina nayi sai naji murmushi mai sauti ya kucce man,tashi nai nanufi dakina don Amnah tabar mun shi yanzu,after dress na dauko baka nasaka nasake gyara rolling dina da pink din gyalena turare na sake fesawa,sannan nafito wajen hajiya nanufa nace mata zanje gidansu zulaiha.
Tayi man adawo lafiya tare da cewa ingaida iyar,
Watau yana kishin infita haka yake,to meya kawo hakan inma sona kake malam ni ban sonka,wata zuciyar tace shima ai bai furta ba hajiya hanan.
Duk yadda naso shan mur fuskata taki bani hadin kai,don ban san ma murmushin yana fita ba,duk da haushin da yake ban akan abunda yayi man kan wannan yarinyar, da kuma text din danai mashi jiya yaki ban ansa.......tuna wa nai da mutanem da suka biyoni dannan nan gaba na yafadi.
Ya na wajen zaman banza yana nufin nizan tukashi kenan.
Tsaye nai bakin kofar dayake, ya sauke glass din yana kallona.
"Kishigo mana."
Kallonsa nai na bata fuska,"wai meka maidani ne driver ka kome."
Hannuwansa ya hada waje guda alamun begin,
"Tuba nake rankiyadade kishigo."
Kallon da yake man yana neman tsayuwata gagara,dole na zagaya na anshi key din na tada.
Saida muka hau titi yace"ban tab'a ganin wadda tuk'i yakewa kyauba irinki."
Maganar ta shigan, amman sai nayi kamar kamar banjiba cigaba yayi da cewa,
"Waye ya koya maki mota."
Murmushi nai don tuno ansar dazan bashi,inga yadda zai dauki maganar."Yayana da banda kamarshi aduniya yah harun."
Lumshe idonsa yayi yanajin kamar ana doka mashi guduma a tsakar kai,maganar ta dokeshi metake nufi har yanzu tana kan son wannan rub'eb'b'en guy din,wan da Saboda tsufa har furfura ta yawai ta ga fuskarsa.
Jiyai wani matsanan cin kishi ya tasho mashi,har bakinshi daci yake shiru yayi yama rasa mezai ce mata.
Sai da yadau lokaci sannan yace idonsa rufe"Au wannan yayan naki daya riga ya tsufa,gaskiya yayi kokari don gashinan kin kware."Haushi ya kamani don me zaice mashi yatsufa,cikin masifa nace"Koma dai me yazama ai dan uwana ne kuma ina sonshi ahaka ehe."
"Nikuma bare bah,ai ko shi banga alamar zai aureki ba."
Wani wawan burki na taka daidai shiga unguwar su zulaiha,don tamun kwatance ta waya.
Kallonsa nai idona cike da masifa,
Shima ni yake kallo idonsa tar kaina,fuskarsa babu walwala kokadan.
Nace"ina ruwanka kuma ai bayyi dakai cewa bazai auran ba,kuma saboda wane dalili kace baka alamar zai auran ba,kana da wanda zakaban ne kome."Lumshe ido yayi baison tun zurata amman duk ta kare hakan shine mafita,
Ya na kallon cikin indonta yace"munyi maganar dashi yace matarsa ta isheshi,kuma ke ai abun kunyarki ne ma ki auri mijin kawarki."Runtse idona nayi inajin wani zafi akirjina,kuka nake son yi amman yaki zuwa,saidai wani tukukin bakin ciki dake taso man cikin balbalin masifa nace"ina ruwanka ai tunkafin ya auretan nason kayana,itama tasani kuma idan ban aureshi ba kai zan aure,nace kai zan aura Allah ma yatsareni da auren irinka."
Ransa yafara b'aci shima ya sake kallonta da idonsa dasuka canza launi,saboda tsabar kishi da baki ciki.
"Ai kuwa nine daidai dake,nine zan yi maleji dake nine zan rufa maki asiri,kinga kuwa Aurena shine rufin asirinki mama Hanan,inajin da yaronki ya rayu yanzu zaiyyi shekara nawa mah?"Innalillahi!in ka kalli idon ta sai ya baka tsoro,tsabar yadda yayi fitinennen jaaa,batace komi ba ta bude motar ta fito.........
Cikin wani irin yanayi,wani irin numfashi take ja saboda yadda kirjinta yake masifar zafi da duka........tafiya tafara yi tana runtse idonta,daker ta tari taxi tashiga.Sadda zai iso wajen sunbar gun,ta wata hanya suka bi tana mashi kwatancen gidansu zulaiha.
Duk inda hankalinsa yake ya tashi,ya kasa motsin kirki mayakai shi meyasa baiyyi shawara da zuciyarsa ba waje. Furta mata wadannan kalaman,ban kyauta ba wlh ban kyautaba.......dukan kanshi kurun yake tana jin haushin kanshi,
"Kece kika tunzurani akan me zakice kina sonsa,eh donme zaki furta wannan kalma gabana wallahi bakison kowa saini,nikikeso hanan nine mijinki.
Hon d'in da ake mashi ne ya dawo dashi daga duniyar dayake...........kallon motar yayi yaga ta Asim ce,zai shigo babu hanya.
Shiga yai yajata gefe shikuma yashigo da tashi.
Fitowa yai da mamaki ganin yadda ya hango tashin hankali karara kan fuskarsa,duk ya yamutse gashin kanshi.Isowa yai ya samai tsaye jingine da motar yana sauke numfashi,ya dafashi.
"Aboki,lafiya meke damunka yanzu naga sakonka nabaro inda nake na taho,wani abun yafaru ne."Girgiza kai yake yana luma hannunsa cikin gashinsa,yana kuma dukan kanshi,saurin rikw hannun sa yayi yana cewa"subhanallahi aboki kanka kalau,lafiya kagaya man mana."
Ganin mutane suna kallonsu yasa yace shiga mota mukarasa gida janshi yayi har motar Asim din,sukabar tashi wajen."Don girman Allah Hanan kiyi shiru ki gaya man abunda yafaru,kedawa meya sameki,tunda kika shigo kike kuka duk kin tayar mana da hankali."
Iyace ta ajiye abincin da aa tanadar ma Hanan din ta zauna,tana jawoni jikinta cikin lallashi take ban baki akan inyi shiru indaina kukan haka nan,kar kaina yayi ciwo araina nace saidai kar akara,don yajima da fara wa.
Ahankali nake ajiyar zuciya ina share hawayen da majinar dake fitowa,hankicif na ansa hannun zulaiha ina cigaba da tsane fuskata.
Mariya nacewa"kiyi hkr Anty komi yayi zafi maganinsa Allah."
Jinjina kaina nayi daker nace"nagode mariya."Ganin nayi shiru yasa iya da mariyar fita suka barmu,iya ta koma wajen baba da take karasa jinyarsa,don yanzu kafar alhamdulilah komi yayi yadda akeso,mariyar kuma tafita dama islamiya xata.
Kallona kurun takeyi ganin har yanzu bance komi ba,saida naje na wanko fuskata nazo na dasha zobon da akaha hadaman da julluf din shinkafa d wken.
Kadan naci na ajiye sai ajiyar zuciya nake,ganin har lokacin bance da ita komi tace,
"Hanan badai ki sanar dani abunda ya faru ko."
Kallonta nai na kawar dakaina nace,"Zan sanar dake kinsani ai ko."
Gyara zamanta tayi tana cewa,
"Ina saurarenki to."Labarin abunda yafaru tsakanina da shi na bata,tun ranar da mukazo har kawo yau,da abunda yafaru nida wannan marar kunyar fitsararrar diyar hajjo.
Ajiyar zuciya tayi tana kallona kafin tace,
"Idan na fahimceku kuduka kuna kishin juna,shine duk yayi musabbabin wannan fadan,shi yana da kuskure kema kina dashi."Kallonta nake idona yasake cikowa da kwallah nace,
"Kina goyon bayan rashin mutuncin dayayi man,ya goranta man kinaji fa har cewa yake wai yarona da yarayu yanzu shekararsa nawa,wane irin. Tozarci ne wannan har yake cewa shine daidaini shine yadace na aura saboda ya rufa man asiri,to ban nemi ya rufeba yatona kowa yaji,banajin komi ai bakaina farauba kuma ba yawon tazubar nayiba,kaddaratace kuma kowa bai isa ya tsallake tash...............ba" kuka mai karfi ya kunceman har kirjina yana dagawa."Wallahi zaisha mamakina ni zaiwa wulakanci,ni Hanan zaisan yayi da diya da sheiyaba,kuma muddin yah harun yanuna son Aurena shizan Aura saidai ya mutu da bakin ciki."
Shiru zulaiha tayi tama kasa cewa komi,don gaskiya ne AJ bai kyauta ba duk da ita ta tunzurashi,hakan bai kamace shiba matsayinsa na namiji babba,ba haka zai nuna kishin saba.
"Ba bayansa nake goya ba Hanan,kiyi hakuri nasan yayi laifi kuma dole zai fuskanci hukunci bama daga wajenki ba harnii saina hukuntashi,ai bazai yuwu ya wulakantaki ina kuma sake mai fuskaba."
Tafadi hakane don ta tsagaita kukan,babu dadin ji don itama zata iya sata."Kibarni dashi zaizo yasaman wallahi."
Lallashina takeyi har na hakura nai shiru,text nayiwa Hajiya cewa bazan dawo ba sai nadan kwana biyu,sannan idan Amnah tadawo ta tahoman kaya kala biyu Bilal ya kawota gidansu Zulaiha.
Kuyi hkr pls nasan kuna hkr dani to kukara wlh yauda gobece sai Allah,ayyuka yawa sukeman gashi typing biyu nake shiyasa nake shan wuya.
Mrs bb ce

YOU ARE READING
A DUNIYAR MU
Fanfictionlabari mai d'auke da abubuwa da dama cin amana, son zuciya, zalinci,sannan da abubuwan da suke faruwa a wannan duniyar Tamu,cin hancin da Tashawa,danne Hakkin maraya, daidai sauransu sai Wata kalar Soyayya mai rikitar da zukata Duk acikin wannan li...