🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
*NANA JAWAHEER*
🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
*STORY AND* *WRITING BY*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)**🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
_________________________________
*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*
'''Gaskiya yau my Fans kun sani farinciki sosai dan naga ruwan comments dinku sosai shiyasa Nima nace dai yakamata a maidama kura aniyarta😜, shiyasa nima yau zanyi maku posting sau biyu..'''
*Wannan page din nakune masoyan NANA JAWAHEER,gashi nan kuyi yanda kuke so dash, much love my fans🌹🤎*
Page 1⃣5⃣
Bayan Alhaji Sulaiman ya gama cin abinci, sun Kara tautauna wa da matar shi akan a dawowar Nana Jawaheer gidan shi da zama, nan ya shiga bedroom yayi wanka ya dan kwanta huta, bayan ya huta yake kiran Sadiq waya yana gaya mashi yanda suka yi da Yayan nashi...
"Sadiq kaji dai yanda mukayi da Abbanku, ammn ni naga kamar wannan karan zamuyi nasara a cikin lamarin..
"To Dady nima ina tunanin haka gaskiya, Allah yasa mudace dai, "Amin ya Allah, yauwa Yaushe kake fara exams ne?"next week insha Allah Dady, a cigaba da yi mamu addu'a dai Dady, "insha Allah, da'man kullun muna yi maku addu'a bakin dayan ku ma Son, "To Dady mun gode, yanzun dai ina karatu, "To shikenan, Allah ya baku sa'a, "Amin..
A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah, yanzun Nana ta shiga a biyar a secondary school, har sun gama first term ma, a cikin wannan kwanakin abubuwa sun faru masu dadi da mararsa dadi ma, saboda da Nana da Talatu zama ba dadi sai dai a ce abun sai addu'a, tunda ita Nana idan Talatu suka yi Mata sai ta rama take cewa..
Ya yin da Nana ta Amince da soyayyar DR KHALID,soyayya suke mai kyau da burgewa, da taimakon Zee wanann soyayya ta kunlu, yanzun abun ya kai da Nana bata iya bacci in ba ta ji muryar sahi'binta ba, Malan yayi ko'kari ya saya ma Nana wayar tecno da ita Nana ke wayarta da rabin rain'ta wanda yanzun take ji idan bashi ba sai dai rijiya... (Lol😜)
_________________________________*NEW DELHI INDIA*
Sadiq yanzun sauran shekara daya ya gama MSC din shi, yanzun sun gama yin lecture, sai dai project da yasa a gaba yanzun, bai da wani guri da ya wuce ya ganshi kasarshi Nigeria, Lukman kuma da Salma soyayya suke yi cikin natsuwa da fahimtar juna, sun fahimci junansu, sun san abunda wannan ke so da wanda ba ya so, suna yi ma juna son gaskiya da Amana, ba mai son ya ga bacin rain dan uwanshi, yanzun itama Salma tana final year tana karanta BSC NURSING, Alhmdulillah Salma itama tana da mai da hankali a kan abunda ya kawota, bata da wasa ba ko shirme a cikin karatun ta....
________________________________
*NIGERIA*
Wooow masha Allah, wata kyaukyawan budurwa na hango ita da wani saurayi, shima kyaukyawan karshe ne a wajen kyau da fari, ita dai yarinyar black beauter ce idan tana magana sai kayi tunani kamar ana tilasta ma yin maganar saboda da ajinta da natsuwarta, tana da idanuwa masha Allah dan idanuwanta sexy eyes ne, ga bakinta dai-dai masha Allah, hancinta dogo da shi idan tana magana har dimple queen dinta ke lotsawa duka size dinta biyun, bata da hayaniya ko kadan dan ita bata cika son yawan magana ba sosai, Allah yayi halinta a jikin Nana Jawaheer , ga booos dinta sun fito masha Allah, ga shape da hips nan sun fito suma, yanzun Nana an zama cikarkiyar budurwa tunda yanzun tana shirin zana exams din NECO da WEACE na aji shida, yanzun takai shekara 18 a duniya, Saurayin da Nana take tsaye dashi ba kowa bane face Khalid dinta, Wanda suke ma juna wani kallar so, wanda suke gani mai rabasu sai ya shirya dan sunma juna alkwarin aure..
