🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
*NANA JAWAHEER*
🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕*STORY And WRITING* *By*
*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)**🌎MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️
*M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻
'''__________________________________
*BISSIILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*
Page_5️⃣1️⃣➖5️⃣5️⃣
"Myluv!
"Naam ina jinki"..
"Da man wai ina san muje wani biki nida Salma".
"Biki myluv?"..
"Eh wata course mate dinmu ce za'ayi ma biki, shiyasa"..
"Myluv magana fa nike kayi shiru", ta yi maganar tana dirdira kafafu tana ta zuba mashi shagwabarta wanda ta zamai mata jinin jiki..
"Uhmm, ki bari zan maki magana yanzun ai kinga ina wani aiki ne"..
"Myluv munfa shirya kawai yanzun tafiya zamuyi yau ake dinner".
"What?"..
"Dinner myluv?"..
"Eh dinner ai bani daya zani ba nida Salma ce, kuma na san Zee ma zataje"..
"To in Zee zata ke baki zuwa, gaskiya ba zan laminci wanann yawon ba, yanzun karfe hudu fa myluv"..
"Amman sai yanzun zaki biki, Aah bama gidan yinin biki ba, dinner zaki tafi haba myluv"..
"Tom nidai dan Allah please myluv".
"Gaskiya ba zan boye maki ba Amman sorry to said myluv ba wata dinner da zaki je"..
"Kana nufin bani zuwa bikin baki daya?"..
"Aa zakije yinin biki insha Allah, amman banda zuwa dinner Myluv"..
"Tom Shikenan hakan ma mungode Myluv".
"Sorry Myluv komai kika nayi maki akan Sonki ne, luv uh"...
"I know Myluv"..
"Salma wallahi ya hana, yace bamu zuwa wata dinner".
"Dan Allah? karki fadi man haka Nana".
"Wallahi dagaske ya hana amman yace gobe munje yinin biki".
"Uhmm Sadiq! wallahi Sadiq halin shi sai shi, yanzun duk wannan kwaliyar da muka yi zata tafi a banza kenan?''..
"Hmmm! Haka yake nufi Salma"..
"No impossible! Ba zai Yuyuba, Nana tashi mu tafi garden ko pictures ne munyi na turama Baby"..
"Good idea! Kin kawo mafita wallahi taso mu tafi ma kafin dare yayi"..
Nan suka je garden suka fara dauka pictures kala-kala, shi dai Sadiq yana gefe yana aikin shi amman ya kan kallesu sai dai yayi dariya yana mamakin wai su a dole basu kwaliyar banza..
"Myluv nazo a dauka dani ko?"Yana dage mata gira daya..
"Ni bani hoto da maza, sai mata" ta fadi tana murguɗa baki😚..
