AURENTA ZANYI....5/6

375 36 3
                                        

_*AURENTA ZANYI....._*🌷

_Wattpad@Aufana8183_

    _5/6....._
Sannu ahankali bunayya tafara karatu cikin nasara da ikon ubangiji,soyayyarta acikin zuciyar iyayenta kowa sai dad'a k'aruwa take,hakama ahalinta na dika b'angaren biyun sai dad'a sonta da k'aunarta sukeyi.

Nanny's biyu takeda masu kula daita sbd momynta tana yawan tafiye tafiye k'asashe k'asashe kasuwanci haka shima abbanta,yanzukam suda Nigeria sai idan bunayya sunyi hutun school saisuzo anan suyi hutun.

Wata iriyar soyayya take samun agun iyayenta musamman mahaifiyarta wacca kokad'an batasan ganin b'acin ranta, hakama mahaifinta idan kaga yanda yake mata zaka rantse da Allah itakad'ai ce yarsa bashida wasu yayan sbd tsabar kaunarda yake nunamata,
     Dahaka rayuwarta tacigaba da gudana cikin tsintsar so da k'auna dakuma cikekkiyar kulawa.
     ..................

_After 15 year's....._
Cikin sauri sauri take shirinta na zowa school bayanda tagama sanya uniform's d'inta wanda yake riga iya guiwa girmanta dark blue da t-shirt fara aciki mai girman hanu iya guiwar hanu, sai white socks da takalma.

Kanta ba hula ko d'ankwali tatufke sumarta gu d'aya tasako da jelar izowa gadon bayanta.

A duk'e take kusa da bed d'inta tana gyara takalmanta, ahankali tad'ago tamike tsaye tareda juyowa domin d'aukan school bag d'inta, woww masha Allah nafurta azahiri batareda ma nasan nafurta ba sbd ganin kyakkyawor halittarda nai.

Dikda ba make-up a fuskarta amma hakan baihana bayyanar tsintsar kyanta a fili ba.

Faffad'ar fuska kyakkyawa kuma fara tas wacca take d'aukeda golding eyes nd' siririn hanci mai d'an girma da tsayi daidai fuskar, bakinta d'an k'arami mara girma sosai,sumarta mai cika da bak'i wulik kuma mai tsayi ssi.

Dikda sanye take da uniforms amma hakan baihana bayyanar kyakkyawor surarta a fili ba, k'itjinta a cike yake taf da dukiyar fulani daka kalla kasan acike yake,hakama bayanda masha Allah hips dinta barakallah dan har rigarta tad'an d'aga daga baya sbd girman hips dinta, gaban rigar yafi bayan dan tsayi, kai atak'aice dai kyakkyawa ce san kowa k'in wanda yarasa.

Dasauri tashuri jakarta tafice harda d'an gudunta sbd dagani tai letti.

Kai tsaye a dining room tafice inda ta tadda iyayenta acan suna breakfast, dasauri taje ta zauna tana fadin "gud morning momy...gud dady" cikin farinciki suka amsa mata cikin faraa abban yashafa kanta yana fadin "baby kinyi letti yau,ya'akayi hakan tafaru ne" d'an b'ata fuska tai tareda tab'e d'an k'aramin bakinta tace "su jasmine ne suka d'auken hankali jiya mukaita chart har 12, shys nai letti".

Cooker dinsu ne yazo yafara zubamata abincinda yasan tafiso take kuma yin break dashi,bayan yagama nan tafara ci sukuma su dady suna firarsu.

Kad'an taci tamik'e tana fadin "am satisfying dad" yace "ok darling, Samuel yana jiranki tin d'azu" shagwabe fuska tai cikin sigar shagwaba tace.

     "Oh...nooo dady, nifa kai nakesan ka kaini yau" yar dariya yai tareda rik'a hanunta yace "angama sweetheart yau hukuncin yamotsa kenan" itadai momy kallonsu kawai take.

Mikewa yai yana saka takalmansa tareda fadin "oya...lets go" cikin faraa taje tarungume momynta tareda sumbatarta a kunce tana fadin "bye momy" itama ta sumbaceta a goshi tana murmushi tace "Ok...bye sweetheart" nan tafice tana dan tsalle.

Koda suka isa tini har an shiga class bakowa a waje, danhaka dagudu tafice izowa class tanama dadyn nata bye bye, shima bye din yamata yana kallonta harta haye step izowa class dinsu sannan yafice.

Sai 10am sannan suka fito break,damacan ita baruwanta dacin break tin a gida takeyin abunta datazo school saidai taci chocolate da sweet dinta,tin fil azal haka take har teachers dinsu sunsanta dashan chocolate da sweet any time zaka samesu acikin school bag dinta shys koda yaushe taketa fama da ciwon mara sbd zak'i.

Mimi da jasmine sune k'awayenta waenda suka hadu a secondary school dinnan tasu tin jss 1 har izowa yanzu dasuke ss 3 wato ajin k'arshe, suma dikansu yan Nigeria ne zamane yakawo iyayensu anan Australia.

Bayan su jasmine sungama break sai suka koma class,
     1:30pm suka tashi daga school suka koma gida.

Daisarta tai wanka tacanja kaya izowa gajeren wando iya guiwa da riga t-shirt fara sannan tafito parlor, ganin momynta bata parlor yasa tahaura sama, a bedroom din dadyn ta tacimmata tana linke masa kaya shikuma yafito daga toilet yana saka kaya, cikin sallama tashiga tareda fadin "hy momy....hy dady" cikin faraa dady yace "welcome sweetheart" ta amsa da "hy dady" tareda kwanciya kan gado.

Kallonta momyn ta tai sannan tace "tashi kije kici abinci mana" toh tafada sannan tamike tsaye tafice.

Kai tsaye dining room tafice taci abinci, bayan tagama takoma bedroom dinta takwanta, wayarta taciro tabude music tafara sha, daga haka har bacci yad'auketa.

Sai kusan 5pm sannan tafarka,wanka tasakeyi kasancewar tana fashin sallah yasa batai batun yin sallah ba,bayan tashirya cikin wata gown girmanta iya guiwa da wata yar hula baka sannan tafice parlor.

#/Vote nd Comment.
#/Aufana for life.

AURENTA ZANYIWhere stories live. Discover now