_*AURENTA ZANYI.......*_🌷
_Wattpad@Aufana8184_
_13/14....._
Haka takwana itakadai acikin d'akin ba cin abinci bare shan ruwa, har izowa yanzu baccin wahala take,jikinta dikyai tabo tabo na duka, ita sallah bama'a maganarta.Hajiya maccha ce tasaka bakinta a zancen sbd sanin halin abban ramadan idan yai fushi ransa yab'aci to yanada wahalan sakkowa, danhaka tashiga bashi hkr amma daga k'arshe saima yace ta tafi tanashi wuri dole yakoyawa bunayya hankali yagyara mata zamanta, bata daina bashi hkr ba har saida tasamu nasara akansa.
Dasauri taje tabud'e kofar dakinda bunayya take a ciki, ak'asa tahangota a kwance yanda tazo kayan jikinta har yanxu haka suke bawani abun da aka canja,hakan ya tabbatar mata dacewa yanda take a jiya haka take har yau.
Dasauri taje ta tallafo fuskarta data kumbura sosai sbd kuka,nantake wani irin taisayinta ya mamayeta,ahankali takama ta mik'arda ita tadora hanunta kan shoulder d'inta tana taimaka mata har suka fita.
Dakyar hajiya maccha tasamu tagasawa bunayya jikinta sbd kukanda take dan azaba sai kiran dady da momy take,sabon kuka yazomata yanzu sbd ganin irin dukanda abban ramadan yamata, gani take dik duniya anmata abunda bawani wanda yatab'a mata kamarshi sai kuka take sosai tana kiran iyayenta.
Dakyar ajiya tasamu tasha tea sannan tacanja mata kayan jikinta tasakamata na sa'arta nabila riga da wando masu kyau, har yanzu kuka take tana kiran iyayenta .
Dakyar hajiya maccha tasamu tadaina kukan,nan tashiga mata nasihohi masu ratsa jiki akan takare kanta namatsayinta na y'amace kodan tazama uwa tagari agun y'ayanta,
Da'alama kam nasihar tashiga jikinta dan tai shuu tana sauraren abunda hajiyar kefada,daga bisani hajiya tafita tabarta acikin d'akin.A ranar hajiyar dady tasaka aka kirawo mata dadyn bunayya,yana zowa yaga yanayin fuskarta yasan akwai damuwa, kamar yanda yasaba haka yadurkusa har k'asa yagaidata, ko kallon kirki bata masaba barema ta amsa gaisuwarsa,zama yai akasa itakuma tanakan kujera.
Ahankali tafara magana cikin kakkausar murya "nakirakane domin yasanya maka albarka akan irin tarbiyyarda kabama y'arka fatima,lallai kayi k'okari sosai sannunka,amma kasani kadel ni Sam bazan d'auki wannan iskancin da lalacin ba,wai yanzu acikin zuri'ata za'asamu wacca take zowa night club kuma ma wai mace ba namiji ba, eh...toh wlh kasani idan har kai bazaka iya kula daitaba ni zan iya shys ma na tura aka d'akkomin ita, daga yanzu kuma tadawo nan da zama sbd naga alamar ku bazaku iya tarbiyyantarda ita yanda yadaceba,wato ku gaku sarakunan san yaya".
Tinda tafara magana dady baice uffanba harta gama,bayan tagama yarisinarda kansa kasa yace "Allah yahuci zuciyarki, ayi kr insha Allah baza'a sakeba,za'a gyara" tab'e baki tai tareda fadin "tashi kabani wuri" haka yamike kowa yafita yana kara bata hkr.
Yana fita yadoshi parlon abban ramadan,kan hanya gaba daya kansa yad'auki zafi lissafinsa dikya jagule, hankalinsa yamatukar tashi sbd yafi kowa sanin halin hajiyarsa haka kuma yafi kowa sanin halin bunayya, yasani bunayya batada tsoro danhaka zata iya mayarwa da hajiya magana idan tamata magana ko fad'a,itakuma hajiya yasan bazata bartaba, danhaka hankalinsa amatukar tashe yake sbd baya kaunar abunda zai taba yar gold dinsa.
Dazuwansa hankali a tashi yashiga tambayar abban ramadan ina bunayya yana buk'atar yaganta, nan abban ramadan yacemasa yaje yatambayi Hajiyarsu idan ta amince sai kaishi gunta yaganta amma idan bata aminceba saidai yai hkr.
Abun yabashi matuk'ar mamaki sbd irin yanda abban ramadan ke girmamasa amma yau shine yakefadawa haka, saidai sam bazai iya zowa yatinkari hajirasu da wannan maganarba sbd sanin halinta baram ma yanzu datake hassale dashi,danhaka bayanda yaiya haka yafice batareda yaganta ba.
