AUREN DOLE (2010)

2 0 0
                                    

https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/

🐹🐹🐹🐹🐹🐹🐹🐹

AUREN DOLE🐹🐹🐹🐹

🐹🐹🐹🐹🐹🐹🐹🐹

©© Murjanatu Umar


🐔🐔🐔1️⃣🐔🐔🐔

Godiya da yabo ga Allah da ya bani ikon rubuta wanan labarin,Allah nagode maka da ka bani Rai da lafiya,Allah ka jikan Wanda suka Riga mu gidan gaskiya ya jikan mu in lokacin mu yayi,Wanda basu da lafiya Allah basu lafiya,matan da mazan dake cikin kuncin rayuwa ,Allah yaye musu,🙏amin

   Nuriyya yarinya ce son kowa kin Wanda ya rasa,ita kadai ce mace acikin 'ya'yan Alhaji Musa  da Hajiya Nabila,ita ce  Auta,maza biyar ne ; Abdullah,najib,bash,Saddam sai Anwar.

   Duk wata kula Nuriyya tana samu wurin iyayenta da yan uwanta,gata Yar gatan mamanta da babanta Kai har ma da yan uwanta da duk wani daginta ,kowa ya samo abinsa Nuriyya ana ji ita sosai.

  Nuriyya fara ce sol Kuma kyaukyauwace ce ga fara'a akwai ta Kuma da faran_faran.Duk in Nuriyya tai dariya sai kumatunta sun lotsa wato abinda bature kan Kira Dimple,Allah yai mata baiwar kwakwalwa akwai daukar karatu nan da nan ga shi tasa Aranta in Allah ya yarda sai ta zama cikakkiyar likita (wato likita bokan bturai)

  Nuriyya a yanzu tana Nursery three ne,sannan Anwar Yana aji daya ,Saddam Kuma aji uku,Bash Kuma aji Hudu ,sai Najib dake aji shidda sanan Abdallah Yana aji biyu a koramar secondary .

  Iyayen Nuriyya wato Alhaji Musa da Hajiya Nabila Auren zumunci akai musu ,don su a zuri'ar su ka'ida ne ka aure Dan gida ba'a auren bare ,in Kuma   ka bujire sai dai ka neme wasu iyayen basu ba ,duk wacce akai ma auren hadi haka nan take hakura ko tana so ko Bata so .To Amma baban Nuriyya shi Yana son matar shi ita ma haka .

©® Maiyammalibrary

AUREN DOLE (2010)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora