https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺🌺
🌺*AUREN DOLE*
🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺🌺
🌺© *® Murjanatu Umar*
*Watpad : Maiyamma*
🌲🌲🌲9️⃣🌲🌲🌲
A yau ne aka tafi da Ammar kasar waje don duba zuciyar sa wacce ta buga a sakamakon labarin daurin auren Nuriyya da za'ayi amma Kuma bada shi ba.An daura auren Nuriyya Kuma har an kaita gidan miji, Nuriyya dai Bata da aiki sai kuka ,duk da lallashin da yan uwanta suka yi mata Iyayen ta kuwa sunce in ta ga dama ta hadiye zuciya ta mutu.
Yaya Tahir ya shigo dakin amarya kenan yaji tai ajiyar zuciya sai yace sorry baby kin ga na Dade ko wallahi friends ne suka Bata min lokaci Amma Bari in zo in baki wani warm kids don kiji sanyi a zuciya Yana Isa ya taba ta bai ji tayi motsi ba ga idonta Kuma kiftawa Bata yi ba,sannan ya kara kunnen shi a kirji ta yaji ba lumfashi ,bai San sadda ya shafe idonta,ba komai yake tunawa ba sai farin cikin ta da yazo rana daya ya sauya shi zuwa bakin ciki da Kuma cewar da tayi mai duk in ya aure ta mutuwa zata yi,wai shi kenan mai sonta,mai kaunar ta yasa ta acikin hali kunci ,har ya Kai ga mutumwar ta,to inna je lahira in ce ma Allah me? Yau nayi na dama da Bata da anfani ,wayyo Allah! Wayyo Allah!! Na ga ta kaina ,na cuce ko Nuriyya ki yafe mun.
Bayan jana'iza ne Yaya Tahir ya tashi Yana rokon su Yaya Abdullahi su yafe mai akan rashin jin shawarasu da yayi ,suka ce duk sun yafe mai ita Kuma Allah ya jikanta ,yace ya gode.
Sanan ya koma kan iyayen nasu ya musu nasiha akan auren dole baahi da alfanu saboda zamani ya canza Kuma Hausawa na cewa" in kida ya canja dole ruwa ta canja " saboda haka kiyi hakuri kuba ma 'ya'yanku Wanda suke so,don wanan ya ishe mu ishara saboda sako ya iske mu Shima Ammar Rai yayi halinsa.
To masu karatu
Anan zan tsaya
A guje ma 'ya'ya AUREN DOLEEND
©® MAIYAMMALIBRARY
![](https://img.wattpad.com/cover/233440583-288-kde10e4.jpg)
YOU ARE READING
AUREN DOLE (2010)
General Fictionlabarin ne akan wata yarinya Nuriyya da aka ma aure da Wanda Bata so karshe ya zama ajali!