5

463 80 12
                                    

A harxuqe take kallon Dr safwan Karo na biyu.

Meyasa kake min haka, duk lokacin dana xo asibitin nan sai ka bata min rai, wannan shine Karo na biyu.

Oh zarah ko hajiya taxo da kanta dole sai ta jira bakori balle ke da magani kawai xaki karba mata, ni meyasa Ma take aiko ki ne.

Kutt ta had'iye wasu yawu kafin tayi magana kamar bata so tana yatsina fuska, na tsani wannan likitan gaskiya baxan iya jiran sa ba idan ka tashi aiki sai ka biya gida ka bata dan Allah, batare da ta saurari amsar sa ba ta juya da sauri xata fice kicibis suka yi Karo da juna Karo na biyu a had'uwar su, idanun su suka sarqe dana juna lokaci daya zukatan su na buga, yana tsinkayo tsanar sa fal a kwayar idanuwan ta, ta saki dogon tsaki tare da jifansa da harara kafin ta raba ta gefen sa ta fice da sauri cikin takaici, ya bi bayan ta da kallo har ta fice ya tabe bakin sa kawai yana maida kallon sa ga safwan, ledar magani ya miqa masa batare da  yayi magana ba ya juya ya fice daga office d'in.

Bayan wani lokaci aka d'aura auren saif bakori da zarah batare da son kowane daga cikin su ba, ba wani shagali akayi sosai ba kasancewar babu wanda ya bada hadin kai acikin su, tayi kukan rabuwa da iyaye tayi kukan rashin masoyin ta Aliyu har qawayen dake tare da ita suka gaji da xaman jiran ango suka fice ta rufe qofar d'akin da key.

Kusan d'aya na dare ya shiga gidan hannun sa riqe dana marwan, ya dube sa cikin murmushi.

Wannan ne Karo na farko dana taba ganin marwan yayi dare haka batare da yayi barci ba.

Kallon sa marwan yayi kamar baxai yi magana ba sai kuma yace daddy da gaske kayi min sabuwar umma kamar yanda hajiya ke fad'a?

Annurin dake fuskar bakori ya kau, batare da ya amsa masa ba suka nufi part d'in sa akan qayataccen gadon sa ya d'ora marwan yana kallon sa, kwanta kayi barci xan shiga wanka yanxu.

Marwan ya girgixa kansa, daddy ka kaini naga umma ina so na ganta.

Yace baxa muje ba, marwan ya shagwabe fuska tare da fad'in ni ina so naje, bakori ya bata fuska, kaima baxaka je ba bana son gardama kasani.

Daddy baka son ta ne? Marwan ya tambaya yana kallon mahaifin sa, bakori Ma kallon sa yake kafin ya gyad'a masa kai alamar eh,

Saboda me? Ya qara tambaya Karo na biyu.

Kai tsaye bakori yace saboda tana da sunan malamar ka.

Marwan ya soma tsalle tana da irin sunan anty zarah kenan, daddy ai tana da kirki sosai tana sona and I like her too, kaima ka so ta.

Kallon da bakori yayi masa ya saka sa had'iye murnar da yake tare da kwanciya ba dan xuciyarsa ta so hakan ba.

Tun da sassafe ta shirya ta fice cikin sabuwar motar da abbanta ya bata, wannan shine Karo na farko da ta soma fita da sauri tun fara service d'in ta, taja dogon tsaki bayan hawaye sun xubo mata tun da take a rayuwa bata taba tsintar kanta cikin irin wannan yanayin ba, tayi kuka kamar ranta xai fita hakan ya janyo mata matsinancin ciwon kai.

Ta d'ora kanta kan teburin dake gabanta tana cigaba da kuka, jin an dafata yasa ta d'ago kanta carab suka had'a ido.

Yace anty zarah meyasa kike kuka ko ummanki ta dake ki, ta goge hawayen tana kallon sa batare da tayi magana ba.

Yace daddy na yayi amarya na sami sabuwar umma, kinga yau nayi saurin xuwa baxa ki qara dukana akan latti ba, ta tsura masa ido tana son tuna wani abu  tabbas baban marwan ne yaxo neman ta dan ta dake shi, oh Allah da gaske wannan tsohon take aure ta qara rushewa da kukan baqin ciki.

Marwan yaji ba dad'i halin daya sami malamar tashi a yau, ya riqa hannun ta yana kallon ta sosai cikin tausayawa kiyi haquri anty xarah kinji, xaki xo kiga amarya daddy yau, ta girgixa kanta tare da janye hannun ta daga riqon da yayi mata tace jeka xauna dalibai sun fara shigowa kaji, ba musu ya juya ya bar gurin.

Da kyar ta tashi saboda jirgin da take ji, asibiti ta nufa office d'in Dr safwan ta nufa kamar ko yaushe ta shiga batare da neman ixini ba, su uku ta sama a office d'in har Dr bakori.....

Please search for my channel, comment and subscribe 🙏 🙏 🙏

Pherty zarah tv

Subscribe dan Allah.

ZARAH... Where stories live. Discover now