Part 1

1.1K 40 3
                                    

[8/5, 8:19 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*



*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*

*Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat)

*Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat)

*Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare.

*Godiya*---- Ga Allah subhanahu wata'ala daya bani rai da lafiya na rubuta maku wannan littafin mai dinbin fad'akarwa da nishadantarwa, yanda nafara lafiya ina rok'on Allah yasa in k'are lafiya.

*Jinjina*--- ga 'yan Golden Pen writers association Allah ya k'ara hada kanmu ya qara mana zaqin hannu ya bamu ikon rubuta abunda zai amfani al'umma baki daya.

*Matashiya*--- wannan labarin qirqirarre ne banyi da niyyar cin zarafin kowa ba duk wanda ya ci karo da abunda yayi daidai dashi yayi haquri.

Page *_~1~_*

• ∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆•

Tsoro na Allah tsoro na muhadu dashi ahanya saboda ko ba komai dai ni nasan bana iya kallon cikin kwayar idanunshi,wani mugun kwarjini yakeman ta bangare guda kuma tsareni da idanunshi masu rikitar dani dayakeyi aduk lokacinda zamu hada hanya.

dukda an bashi shedar tinda ake dashi ba'a taba ganin miskili ta bangare guda kuma kamilin saurayi aduk fadin unguwar ba irin shi.

Unguwar da take cikeda 'ya'yan masu kudi 'yan gata, 'ya'yan masu fad'a aji a fad'in Nigeria, da yawa yawansu ma ba a qasar sukeyin karatu ba ta wani bangare kuma sha'aninsu sukeyi da 'yan matansu 'ya'yan k'usoshin gwamnati irinsu amman duk da haka acikinsu Ya Ameen daban yake.

mata dayawa suna sonshi amman shi Sam basa gabanshi Aikinshi da kasuwancinshi kadai yasanya gaba, acewarshi har yanzu ba'ayi yarinyar dazai tsaya b'ata ma kanshi lokaci akanta ba, kai shi soyayyar ma gabaki dayanta bai yarda da itaba.

Menene abunso a jikin mace? Kullum tambayar da ya keyi ma kanshi kenan.

(Nidai nace bakaje hannu baneba lol🤣)

""""""***************"""""

Ahankali nake takawa cikin natsuwata da tafiya ta mai ban sha'awa da burgewa, ni ahakan ma gani nakeyi sauri nakeyi saboda aiken da ummata tayiman kasuwa banaso na rasa adaidaita din da zai kaini duba da yanayin unguwar tamu, akwai drebobi har guda uku acikin tanqamemen gidan namu ko nace nasu amman dukda haka ummana ta haneni da shiga motocin domin kaini inda zani, a cewarta in tsaya matsayina na diyar mai aikin gidan mara galihu saboda gudun wulaqanci dukda cewa su drebobin ba zasu wulaqantani ba kasancewar mu dasu duk matsalar mu daya na wulaqanci da muke fuskanta daga matar gidan,

A wajen mai gidan da babban yaron gidan ne kawai muke samun sassauci amman ba daga su ba mudin da dabbobin dake gidan gonar bangare daya daga cikin gidan duk daya muke awajen iyalan gidan in kacire mutum uku rak cikin mutum bakwai daga cikin gidan watau Ya ameen Babban Dandan Gidan a maza, afnan watau autar gidan dashi kanshi kuma uban gayyar watau mai gidan Alhj Mustapha Dambulan

BAN FI KARFINTA BAWhere stories live. Discover now