Part 14

889 23 2
                                    

    ~Oum-Deedat ce~

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



  🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

              🌺🌺🌺🌺🌺



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*



Addu'ar Tsoron Shirka:

اَللَّهُمَّ  إِنِّي أَعُوذُبِكَ أَنْ أُشْرِكَ بِكَ وَأَنَا أَعْلَمْ، وَأَسْتَغْفِرُكَ لِمَا لاَ أَعْلَمُ.

Allahumma innee a'oozu bika an oshrika bika wa-ana a'lam, wa-astaghfiruka lima la a'lam.

Ya Allah! Ina neman tsari da Kai da na yi shirka da Kai alhali ina sani, kuma ina neman gafararka ga wanda ban sani ba.



>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

  *Rubutawa*--- _Amina Hassan  (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

  

                *Wannan Page ɗin naki ne @Salamatu kiyi yanda kike so dashi, kuma ki gaida mana da Ya Ameen kice muna mashi Allah ya huta gajiya*

            *Dama rayuwa ta gaji haka, sai Kaga wani cen daban wanda baka haɗa komai dashi ba, shine masoyn naka, mai bibiyar ka, Amman wanda kake ganin ɗan uwa ka ne, abokin ka ne, maƙwafcinka ne, ko kuma abokin wasan ka, shi kam baya bibiyar ka, balle ma idan kayi posting ɗan sharhin nan yayi maka, wanda ni kau a gani na ba haka zaman tare yace ba, idan kana son mutum kana son Abunda yake yi, ka faɗa mashi, ka ƙarfafa mashi guiwa, ta hakan ne kaɗai zaka gane cewa mutum ya san dakai kuma shi ɗin naka ne. Hmmm Allah dai ya kyauta wlh*



*Page ~66~*





                Walima tayi kyau sosai kam, ni dai ina cen zaune ɗakin da Mom ta sanya aka buɗe mana ni da ƙawaye na, afnan kau sai shige da fice take yi, komai ake buƙata ita ce mai kawo mana shi. Kyaututtuka dai na sha su daga hannun manya, idan Mom taga kyauta ce mai muhimmanci Afnan take ba ta kai mani sashe na ta kulle mani.

Kwata-kwata ban ko ga giccin Ya Ameen ba, ko da wasa, tin dai asuba daya fice.

Mai video coverage yana ta faman aikin yi, yayin da gidajen tv suma suna ta naɗar abubuwa masu amfani.

Hayaniya naji ta kaure sosai a cikin harabar gidan, wai ashe anguna ne suka shigo gaida iyayen su. Da kuma yi masu Allah ya sanya alkhairi.

Sashen Kaka zuwaira suka fara shiga, aiko sun sha zaulaya kaman me? Da zasu fice ne take cewa dasu wai suje su kawo mata amaryar a ɗauke su photon tarihi.

To koda suka shigo sashen Mom ɗinma sun gaggaisa sosai, inda suka buƙaci amarya ta fito za'ayi hotunan tarihi, na wannan babbar ranar.

   Haka aka sanya aka sake gyaggyara mani, kaina a lulluɓe aka fito dani, duk kowa ya fito kuwa ana ta son ɗaukar photo da amarya.

BAN FI KARFINTA BAWhere stories live. Discover now