Fadar Sarki Aaron

396 38 6
                                    

               Rashin Comments din Fans na Daya daga cikin abunda ke kashe ma Marubuci Kwarin Gwiwa...Tabbas ya daga abunda ya maidani Lazy Writer sosai wanda ada bahaka nake ba...A Masarautar Boye inason Comments Sosai dan shike karfafa mana gwiwa hakan yasa nakasa fara sakinsa haryau duk da naci rabi a Rubutun dama sauran da nakeyi...Allah yasa Mudace wannan yajima dana sake page din a facebook.

🅿️01

Garin yayi duhu sosai sai karar tsawar da ke sauka kamar saukar aradu ga wani irin iska dake kadawa, tare da wani irin walkiya me haske sosai. Fadar tayi shiru banda kaiwa da komowa babu abunda Sarki yakeyi a wannan lokacin, Idannunsa sunkada sunyi jawur ba alamun Imani sam a tattare dashi, Wasu daga cikin Jaruman fadawansa ne suka bude Babbar kofar fadar suka shigo. Yana ganinsu ya karasa gabansu. ya kunganta?.

         shiru dukansu sukai tare da saukar da kansu kas saboda tsoro da kuma tunanin abunda zasu fada masa. Nace kun kawota?!. Yafada cikin wani irin murya mai karfi tare da daka musu wata irin kara wanda lokaci guda jikinsu ya shiga kadawa sosai.

       Aa ran Sarkin Larza ya dade mun kamata ta kub.. shirun da sauran suka ji yayine yasa suka dago inda abunda suka gani yasa jikinsu ya fara kadawa sosai, Kansa ne a jikin abun hannunta mai dogayen yatsu sai jininsa dake kwarara a kasa kamar anyanka saniya a gefe gangan jikinsa ne ke faman motsi suna kallo harya daina motsawa cikinsu ba wanda ya iya daga kansa ya kalla inda take tsaye.

Zakuje kukawo ta ko sai duk na rabaku da kawukan ku?. Tafada tana kallonsu. Cike da tsoro dukansu suka tashi suka fita da gudu harsuna tuntube. Sarki cike da damuwa ya juya mata baya.

        Murmushi tayi wacce zamu iya kira data gefe tare da sa hannunta a hakarkarinta ta karasa gabanshi tana wani irin taku kamar bata son taka kasa, Kan dake hannunta da jinin ta kalla lokaci guda komai ya bace agun kamar baayi komai ba.

        Murmushi ta kuma sakar mishi tare da saka hannayenta duka biyu kan kafadarsa, Tana mishi wani irin kallonsa, Murmushi ta kuma sakar masa tare da kara shigewa jikin nasa shima kallonta yake batare da yayi wani yunkuri ba na tabata ko matsawa daga inda yake ba.

Lumshe idanunta tayi lokacin da dumin jikinsa ya isa zuwa nata, Daga kafafunta dake kasa tashigayi dan samun damar cafko bakinsa dan ya mata tsawo da yawa cikin saa kuwa ta sama ikon cafkewa inda tashiga shashshafashi tana sumbartarsa, Lokaci guda batare da ya san me yake ba shima yashiga maida mata da martini yana shafata sosai, Lokaci guda Fadar ta kidime da gurnaninsu cak ya dagata inda suke kallon juna tana cigaba da mishi wani irin murmushi.

         Bai direta ko inaba sai daya zauna kan kujerar mulkin nasa ya daurata kan cinyarsa, suka kuma hade bakunansu gu guda, sosai suke romancing junansu kamar baa fada suke ba.

uhm uhm!. Sukaji anyi gyaran murya da sauri ta daga shi lokacin da take kokarin saita kanta shima sarkin haka, ko ajikinta babu abunda ya dameta da ganinsu da tsohon yayi. Lafiya meya kawo ka wajen Sarki a wannan lokacin da ake cikin tashin hankali da damuwa?. Dakyar ya iya daga idanunsa ya kalleta cikin sauri kuma tsohon ya maida kansa kasa.

        A ransa banda tirrr da halin yaran ba abunda yake yana matukar mamkin yadda yaro dan shekara sha tara da yar sha takwas ke juya musu kai a wannan masarautar gaba daya, Akulum suna jin mutuwar Sarki wato mahaifin  Sarki Aaron.

       Ba tambayar ka abu nayiba?. Tafada cikin daga murya tana huci.

A tsorace ya dago saboda jin muryarta inda wacce mutanen Kasar Larza ke tsoro a yanzu baiwuce Gimbiyar Bokayen Kasar ba Dalia wacce idan tayi Magana jiki yana rawa ake dauka, Da subi zancen masoyinta Sarki Aaron gwanda subi zancenta saboda irin zalinci da muguntar ta ba abune mai wahala ta kashe mutum nan da nan ba.

           Fadi abunda ke tafe dakai!. Aaron yafada sanin halin Dalia idan yakara lokaci harta mishi Magana ta iya mishi komai shiya sa yayi saurin karbeta ta hanyar mishi Magana.

Bakomai dama nazo duba lafiyar sarkine saboda mummunar labarin da muka samu kan guduwar Matar Waz.

      Shiru! rufemun baki! Me kake nufi da kazoo duba lafiyarsa?. Tafada cikin daka mishi wani irin mugun tsawa wanda saida jikinsa ya kada.

      Kayi gaggawar barin fada inba so kake yanzun nan na sauya maka duniya ba. Ta fada a fusace da gudu tsohon ya sunkuya ya tashi ya kalla Aaron dake kallonshi ya fita da gudu.

Wani irin ajiyar zuciya take saukewa me zafi tare fidda nishi wanda ke nuna ranta y abaci sosai. Ganin haka yasa Sarki Aaron saukowa daga kan kujerar mulkinsa ya nufota tare da girgiza kansa.

      Meyake faruwa? Meyasa kike irin wannan fushin bayan nasha fada miki kirage kidunga binsu a hankali. Yakarasa maganar lokacin daya rungumota ta baya tare da sauke lips dsinsa kan kafadarta yana lumshe ido.

      Ajiyar zuciya Dalia ta sauke tare da lumshe ido saboda abunda take matukar so yake mata, Dasauri ya dagata tuna yadda tsohon nan yazo ya samesu dazun yaja hannunta. Muje daga ciki. Yafada a kunnenta murmushi tayi tare da biye masa suka bar gun.

Gudu take cikin dajin ba takalmi a kafarta sai dai zaka iya ganin goyon dake bayanta da kukan jaririyar wanda baya fita sosai saboda ruwan, wacce ke rufe da leda, Shiga jejin take batare da ta tsayaba tana wani irin nishin wahala.

        Gata can!,. taji wata murya daga bayanta wanda hakan ya tabbatar mata sunkusa cinmata, zazzare manyan idannunta ta shiga yi a tsorace tare da kara k'arfin gudunta....









             Coming soon.






     

Boyayyar MasarautaDonde viven las historias. Descúbrelo ahora